Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
1 Daga Bulus, wanda aka kira ya zama manzo na Kristi Yesu bisa ga nufin Allah, da kuma ɗanꞌuwanmu Sostanus, 2 zuwa ga ikilisiyar Allah da ke Korinti, wato ku da aka tsarkake ku cikin haɗin kai da Kristi Yesu, ku da aka kira ku ku zama tsarkaka, tare da dukan waɗanda suke kira ga sunan Ubangijinmu Yesu Kristi a koꞌina, Ubangijinsu da kuma namu:
3 Bari alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kristi su kasance tare da ku.
4 Ina gode wa Allahna domin ku a koyaushe, saboda alherinsa da ya ba ku cikin Kristi Yesu; 5 domin ya albarkace ku a kowace hanya a cikin Yesu, ya sa kun iya yin magana da kyau kuma ya ba ku cikakken ilimi, 6 tun da yake shaida game da Kristi ta yi ƙarfi a tsakaninku, 7 domin kada ku rasa wata kyauta, yayin da kuke jira da dukan zuciyarku lokacin da Ubangijinmu Yesu Kristi zai bayyana. 8 Zai sa ku tsaya da ƙarfi har zuwa ƙarshe don kada wani ya zarge ku a ranar da Ubangijinmu Yesu Kristi zai dawo. 9 Allah wanda ya kira ku ku yi zumunci tare da Ɗansa, Yesu Kristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.
10 Yanzu ina roƙon ku ꞌyanꞌuwa, ta wurin sunan Ubangijinmu Yesu Kristi, cewa bakinku ya zama ɗaya kuma kada a samu rabuwa a tsakaninku, a maimakon haka, ku kasance da haɗin kai a cikin dukan abubuwa da kuma yadda kuke tunani. 11 Gama wasu daga cikin gidan Kulowi sun gaya mini game da ku cewa akwai rashin jituwa a tsakaninku ꞌyanꞌuwana. 12 Abin da nake nufi shi ne, wasu a cikinku suna cewa: “Ni na Bulus ne,” wasu suna cewa: “Ni na Afollos ne,” wasu kuma, “Ni na Kefas ne,”* wasu kuma sun ce: “Ni na Kristi ne.” 13 Shin Kristi ya rabu kashi-kashi ne? Ai ba Bulus aka kashe a kan gungume saboda ku ba, ko ba haka ba? Ko kuma an yi muku baftisma cikin sunan Bulus ne? 14 Ina gode wa Allah cewa ban yi ma wani cikinku baftisma ba, sai dai Kirisbus da Gayus, 15 don kada wani cikinku ya ce an yi masa baftisma a cikin sunana. 16 Hakika, na kuma yi wa mutanen gidan Stifanas baftisma. Sauran kam, ban san ko na yi ma wani cikinsu baftisma ba. 17 Domin Kristi ya aiko ni, ba don in yi baftisma ba, amma in yi shelar labari mai daɗi; kuma ba don in yi magana kamar wanda ya je makaranta sosai ba, don kada a mai da gungumen azaba* na Kristi ya zama marar amfani.
18 Domin saƙo game da gungumen azaba* saƙon banza ne ga waɗanda suke hanyar hallaka, amma ga mu da muke samun ceto, ikon Allah ne. 19 Gama a rubuce yake cewa: “Zan sa hikimar masu hikima ta hallaka, kuma zan ƙi ilimin masu ilimi.” 20 Ina mutum mai hikima yake? Ina marubuci* yake? Ina mutumin da ya iya mahawara game da abubuwan zamanin nan* yake? Allah ya sa hikimar duniyar nan ta zama wawanci, ko ba haka ba? 21 Gama ta wurin hikimar Allah, duniya ta kasa sanin Allah ta wurin nata hikimar, amma Allah ya yi farin ciki ya ceto mutanen da suka ba da gaskiya ga saƙon da ake waꞌazin sa, ko da yake wasu mutane suna ganin saƙon wawanci ne.
22 Yahudawa suna neman a nuna musu alamu, mutanen Girka kuma suna neman hikima; 23 amma mu muna waꞌazi cewa an kashe Kristi a kan gungume, a wurin Yahudawa hakan abin tuntuɓe ne, a wurin alꞌummai kuma wawanci ne. 24 Amma ga waɗanda aka kira, ko da su Yahudawa ne, ko mutanen Girka, Kristi ne ikon Allah da kuma hikimar Allah. 25 Domin abin da ake ganin kamar wawanci ne na Allah, ya fi mutane hikima, kuma abin da ake ganin kasawa ce ta Allah, ya fi mutane ƙarfi.
26 Gama ꞌyanꞌuwana, saꞌad da Allah ya kira ku, kaɗan ne daga cikinku suke da hikima a idon ꞌyanꞌadam, kaɗan ne suke da iko, kaɗan ne kuma suka fito daga iyalan da ake darajawa, 27 amma Allah ya zaɓi abubuwan wawanci na duniya don ya kunyatar da masu hikima; kuma Allah ya zaɓi abubuwa masu kasawa na duniya don ya kunyatar da abubuwa masu ƙarfi; 28 kuma Allah ya zaɓi abubuwa marasa muhimmanci na duniya, da abubuwan da aka rena, da abubuwan da ba kome ba, don ya kawo ƙarshen abubuwan da ake ganin suna da muhimmanci, 29 hakan zai sa kada wani ya yi taƙama a gaban Allah. 30 Amma saboda shi ne kuke da haɗin kai da Kristi Yesu, wanda ya zama mana hikima daga wurin Allah, da adalci, da tsarkakewa, da kuma ceto ta wurin fansa, 31 don ya kasance daidai yadda aka rubuta cewa: “Wanda yake taƙama, bari ya yi taƙama da Jehobah.”*