Ayyukan Manzanni
25 Don haka, kwana uku bayan isowar Festus yankin kuma ya karɓi mulki, sai ya haura zuwa Urushalima daga Kaisariya. 2 Sai manyan firistoci da kuma mutanen da ake darajawa a tsakanin Yahudawa suka kai ƙarar Bulus wurinsa. Sai suka soma roƙan Festus 3 ya yi musu alfarma ta wajen aika Bulus ya zo Urushalima. Amma suna shirin su tare Bulus a hanya kuma su kashe shi. 4 Festus ya amsa musu cewa za a ci-gaba da tsare Bulus a Kaisariya kuma shi ma ya yi kusan koma wurin. 5 Sai ya ce: “Bari shugabanninku su bi ni, kuma su gabatar da ƙara a kan mutumin idan da gaske ne ya yi wani laifi.”
6 Bayan ya yi kwanaki takwas ko goma tare da su, sai ya koma Kaisariya. Washegari, ya zauna a kujerar shariꞌa kuma ya ba da umurni cewa a kawo Bulus. 7 Da Bulus ya shigo, sai Yahudawa da suka gangaro daga Urushalima suka tsaya kewaye da shi, suna zargin sa da aikata laifuffuka da yawa masu tsanani waɗanda su da kansu ma sun kasa ba da tabbacin hakan.
8 Amma Bulus ya kāre kansa ta wurin cewa: “Ban yi wani abin da ya saɓa wa Dokar Yahudawa* ko haikali ko kuma Kaisar ba.” 9 Amma da yake Festus yana so ya samu farin jini a wurin Yahudawan, sai ya amsa ma Bulus ya ce: “Za ka so ka haura zuwa Urushalima kuma a yi maka shariꞌa a gabana game da abubuwan nan a wurin?” 10 Amma Bulus ya amsa ya ce: “Ina tsaye a gaban kujerar shariꞌa na Kaisar, inda ya kamata a yi mini shariꞌa. Ban yi ma Yahudawa wani laifi ba, kai da kanka ma ka soma gane hakan. 11 In kuwa na yi wani laifi da gaske da ya isa a kashe ni, ban ƙi in mutu ba; amma idan zargi da mutanen nan suka kawo a kaina ba gaskiya ba ne, ba wanda ya isa ya ba da ni a gare su a matsayin alfarma. Na ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar!” 12 Bayan Festus ya yi magana da taron masu ba shi shawara, sai ya amsa ma Bulus ya ce: “Ka ɗaukaka ƙara zuwa wurin Kaisar; to wurin Kaisar za ka je.”
13 Bayan ꞌyan kwanaki, sai Sarki Agirifa da kuma Banis suka isa Kaisariya domin su yi wa Festus ziyarar bangirma. 14 Da yake za su yi kwanaki a wurin, sai Festus ya gaya wa sarkin game da ƙarar da aka kawo a kan Bulus, yana cewa:
“Akwai wani mutum da Felis ya bari a kurkuku, 15 kuma saꞌad da nake Urushalima, manyan firistoci da dattawan Yahudawa sun kawo ƙarar sa wurina kuma suka roƙe ni in yanke masa hukuncin kisa. 16 Amma na gaya musu cewa a alꞌadarmu ta Romawa, ba ma ba da mutum a matsayin alfarma sai ya fuskanci masu zargin sa kuma ya sami damar kāre kansa daga zargin da suke yi masa. 17 Saboda haka da suka iso nan, ban ɓata lokaci ba, amma washegari na zauna a kujerar shariꞌa kuma na ba da umurni a kawo mutumin. 18 Saꞌad da masu zargin sa suka tashi don su yi magana, ba su zarge shi da wasu laifuffuka masu tsanani kamar yadda nake tsammani ba. 19 Suna dai gardama ne game da addininsu da kuma wani mutum mai suna Yesu wanda ya mutu, amma Bulus ya ci-gaba da cewa yana raye. 20 Da yake na rasa yadda zan sasanta irin wannan gardamar, sai na tambaye shi ko zai so ya je Urushalima domin a yi masa shariꞌa a wurin. 21 Amma saꞌad da Bulus ya ce a ci-gaba da tsare shi zuwa lokacin da Babban Sarki* zai yanke shawara, sai na ba da umurni a ci-gaba da tsare shi har sai lokacin da zan aika shi zuwa wurin Kaisar.”
22 Sai Sarki Agirifa ya ce wa Festus: “Zan so in saurari mutumin nan da kaina.” Sai Festus ya ce masa: “Za ka saurare shi gobe.” 23 Washegari, Agirifa da Banis sun shigo wurin da ake shariꞌar da alfarma mai girma tare da manyan sojoji da manyan mutanen birnin. Saꞌad da Festus ya ba da umurni, sai aka shigo da Bulus. 24 Sai Festus ya ce: “Ya Sarki Agirifa da kuma dukanku da ke tare da mu, ga mutumin da dukan Yahudawa suka kawo ƙarar sa a wurina a Urushalima da kuma a nan, suna kuma ta da murya suna cewa bai cancanci ya ci-gaba da rayuwa ba. 25 Ina ganin bai yi wani laifin da ya isa a kashe shi ba. Don haka, saꞌad da mutumin nan ya ɗaukaka ƙara zuwa wurin Babban Sarki, sai na tsai da shawarar aika shi wurinsa. 26 Amma ba ni da wani abin da zan rubuta game da mutumin nan zuwa ga Ubangijina. Saboda haka, na kawo shi a gaban dukanku, musamman ma a gabanka, Sarki Agirifa. Domin bayan mun bincika ƙararsa, zan iya samun abin da zan rubuta. 27 A ganina, bai kamata a aika fursuna ba tare da an rubuta laifuffukan da ake zargin sa da yi ba.”