Ayyukan Manzanni
6 A kwanakin, saꞌad da almajiran suke ƙaruwa, Yahudawa da ke yaren Girka suka soma gunaguni a kan Yahudawa da ke Ibrananci, don matan Yahudawa da ke yaren Girka waɗanda mazajensu suka mutu ba sa samun rabonsu na abincin da ake rabawa kullum. 2 Sai manzanni goma sha biyun suka kira dukan almajiran kuma suka ce musu: “Ba zai dace mu bar kalmar Allah mu soma raba abinci ba. 3 Saboda haka ꞌyanꞌuwa, ku zaɓa daga tsakaninku maza bakwai da aka san su da halin kirki, da suke cike da ruhu da kuma hikima, don mu naɗa su su yi wannan aiki mai muhimmanci; 4 amma mu za mu mai da hankali ga yin adduꞌa da kuma koyar da mutane kalmar Allah.” 5 Dukan almajiran sun ji daɗin abin da suka faɗa kuma suka zaɓi Istifanus, mutumin da ke cike da bangaskiya da kuma ruhu mai tsarki, da Filibus, da Burokorus, da Nikano, da Timon, da Barminas, da Nikolas mutumin Antakiya, wanda a dā yake bin addinin Yahudawa.* 6 Suka kawo su wurin manzannin, kuma bayan da manzannin sun yi musu adduꞌa, sai manzannin suka sa hannayensu a kan mutanen nan da suka zaɓa.
7 Saboda haka, kalmar Allah ta ci-gaba da yaɗuwa kuma adadin almajiran ya ci-gaba da ƙaruwa a Urushalima. Ƙari ga haka, firistoci masu yawan gaske suka fara ba da gaskiya.
8 Istifanus wanda ya samu alheri sosai da iko daga wurin Allah, yana yin manya-manyan abubuwa masu ban mamaki da kuma alamu a tsakanin mutanen. 9 Wasu mutane daga rukunin da ake kira Majamiꞌar ꞌYantattu sun zo tare da wasu mutane daga Sayirin da Alekzandiriya da wasu daga Kilikiya da kuma Asiya don su yi gardama da Istifanus. 10 Amma sun kasa yin nasara a kansa domin ya yi magana da hikima da kuma ruhun da Allah ya ba shi. 11 Sai suka zuga wasu mutane a ɓoye su ce: “Mun ji shi yana maganganun saɓo a kan Musa da kuma Allah.” 12 Ta haka, sun zuga jamaꞌa da dattawa da kuma marubuta su yi fushi da Istifanus, nan da nan, jamaꞌar suka zo da gudu suka kama shi kuma suka kai shi gaban Sanhedrin.* 13 Kuma suka kawo shaidun ƙarya waɗanda suka ce: “Mutumin nan ya ƙi ya daina faɗan abubuwa marasa kyau game da wannan wuri mai tsarki da kuma Doka.* 14 Alal misali, mun ji shi yana cewa wannan Yesu mutumin Nazaret zai rushe wannan wurin, ya kuma canja alꞌadun da Musa ya bar mana.”
15 Kuma dukan waɗanda suke zama a wurin taron Sanhedrin* suka zuba masa ido, sai suka ga cewa fuskarsa ta zama kamar fuskar malaꞌika.