Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
15 Yanzu ꞌyanꞌuwa, ina so in tuna muku game da labari mai daɗin da na yi muku shelar sa, wanda kuka karɓa kuma kuka riƙe da ƙarfi. 2 Ta wurinsa ne kuke samun ceto idan kuka riƙe labari mai daɗi da na yi muku shelar sa sosai, in ba haka ba, kun zama masu bi a banza.
3 Ɗaya daga cikin abubuwa na farko da na koya muku, shi ne abin da ni ma aka koya mini, cewa Kristi ya mutu saboda zunubanmu kamar yadda yake a rubuce a Nassosi; 4 kuma an binne shi, hakika an ta da shi a rana ta uku kamar yadda Nassosi suka faɗa; 5 kuma ya bayyana ga Kefas,* saꞌan nan ya bayyana ga almajiransa goma sha biyun. 6 Bayan haka, ya sake bayyana ga ꞌyanꞌuwa fiye da ɗari biyar a lokaci ɗaya. Yawancinsu suna tare da mu har wa yau, ko da yake wasu cikinsu sun mutu.* 7 Bayan haka ya bayyana ga Yaƙub, saꞌan nan ya bayyana ga dukan manzannin. 8 Amma a ƙarshe ya bayyana gare ni kamar jaririn da aka haifa tun lokaci bai yi ba.
9 Gama ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, kuma ban cancanci a kira ni manzo ba, domin na tsananta wa ikilisiyar Allah. 10 Amma saboda alherin Allah ne na zama yadda nake, kuma alherinsa a gare ni ba a banza ba ne, domin na yi aiki fiye da kowannensu; duk da haka, ba ni ba ne, amma alherin Allah da ke tare da ni ne. 11 Don haka, ko da ni ne, ko kuma su ne suka koyar da ku, haka ne muke waꞌazi, kuma haka ne kuka ba da gaskiya.
12 Yanzu tun da ana waꞌazi cewa an ta da Kristi daga mutuwa, me ya sa wasu a cikinku suka ce ba za a yi tashin matattu ba? 13 Idan gaskiya ne cewa ba za a yi tashin matattu ba, ba a ta da Kristi daga mutuwa ke nan ba. 14 Amma idan ba a ta da Kristi daga mutuwa ba, babu shakka, waꞌazinmu a banza ne, kuma kun ba da gaskiya a banza. 15 Ƙari ga haka, da a ce ba za a ta da matattu daga mutuwa ba, da zai zama cewa mun yi shaidar ƙarya a kan Allah, domin mun ce ya ta da Kristi daga mutuwa, amma bai ta da shi ba. 16 Don idan ba za a ta da matattu ba, to, ba a ta da Kristi ba ke nan. 17 Ban da haka, idan ba a ta da Kristi daga mutuwa ba, bangaskiyarku ba ta da amfani; har yanzu kuna cikin zunubanku. 18 Kuma waɗanda suke da haɗin kai da Kristi da suka mutu sun shuɗe. 19 Idan saboda rayuwa na yanzu ne kawai muke da bege cikin Kristi, to ya kamata a tausaya mana fiye da kowa.
20 Amma yanzu an ta da Kristi daga mutuwa, shi ne kuwa nunan fari cikin waɗanda suka mutu. 21 Tun da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum ɗaya, za a yi tashin matattu ma ta wurin mutum ɗaya. 22 Kamar yadda ta wurin Adamu kowa na mutuwa, haka ma ta wurin Kristi kowa zai samu rai. 23 Amma za a ta da kowa bi da bi: Da farko, Kristi,* bayan haka sai waɗanda suke na Kristi a lokacin dawowarsa. 24 Bayan haka, sai ƙarshen ya zo, saꞌad da zai miƙa Mulkin ga Allahnsa da Ubansa, bayan ya kawo ƙarshen dukan gwamnatoci, da dukan hukumomi, da kuma iko. 25 Domin zai yi sarauta har sai lokacin da Allah ya sa dukan abokan gāba a ƙarƙashin ƙafafunsa. 26 Kuma abokiyar gāba ta ƙarshe, wato mutuwa, za a kawo ƙarshen ta. 27 Allah ya “sa kome a ƙarƙashin Mulkinsa.”* Amma da ya ce an ‘sa kome a ƙarƙashin Mulkinsa,’ a bayyane yake cewa hakan bai haɗa da Wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa ba. 28 Saꞌad da aka sa dukan abubuwa a ƙarƙashin Mulkinsa, Ɗan ma da kansa zai miƙa kansa ƙarƙashin ikon Wanda ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin Mulkinsa, domin Allah ya zama kome ga kowa.
29 Idan ba haka ba, mene ne waɗanda aka yi musu baftisma don su mutu za su yi? Idan ba za a ta da matattu gabaki-ɗaya ba, to me ya sa ake musu baftisma don su mutu? 30 Me ya sa muke shiga haɗari a kowane lokaci? 31 A kullum ina shiga yanayin da zai iya sa a kashe ni. Hakan tabbatacce ne ꞌyanꞌuwana, kamar yadda nake taƙama da ku cikin Kristi Yesu Ubangijinmu. 32 Idan kamar wasu mutane,* na yi faɗa da dabbobin daji a Afisa, wane amfani ne hakan yake a gare ni? Idan ba za a ta da matattu ba, “bari mu ci mu sha don gobe za mu mutu.” 33 Kada a ruɗe ku. Yin tarayya da abokan banza yakan ɓata halayen kirki. 34 Ku dawo cikin hankalinku a hanyar adalci kuma kada ku yi zunubi, don wasu ba su san Allah ba. Ina faɗin hakan ne don in kunyatar da ku.
35 Amma wani zai ce: “Ta yaya za a ta da matattu? E, da wane irin jiki ne za su dawo?” 36 Kai marar tunani! Abin da ka shuka ba zai yi girma ba sai ya mutu tukuna. 37 Kuma abin da ka shuka, ba jiki ba ne da zai tsira,* amma hatsi ne kawai, na alkama ko wani iri dabam; 38 amma Allah yana ba shi jiki yadda ya ga dama, yana ba kowane iri nasa jikin. 39 Ba duka jiki ba ne iri ɗaya, akwai jiki na ꞌyanꞌadam, akwai na shanu, akwai na tsuntsaye, akwai kuma na kifaye. 40 Waɗanda suke sama suna da nasu jikin; kuma waɗanda suke duniya suna da nasu jikin; amma ɗaukakar jikin waɗanda suke sama dabam take, kuma ɗaukakar jikin waɗanda suke duniya dabam take. 41 Ɗaukakar rana dabam take, ɗaukakar wata dabam take, kuma ɗaukakar taurari dabam take; gaskiyar ita ce, ɗaukakar wani tauraro ma ta yi dabam da na wani tauraro.
42 Haka yake da tashin matattu. Jikin da aka binne* yana ruɓewa, amma jikin da aka ta da ba ya ruɓewa. 43 Ana binne jiki da rashin daraja; ana ta da shi kuma da ɗaukaka. Ana binne shi da rashin ƙarfi; ana ta da shi da iko. 44 Ana binne jiki na zahiri; ana ta da jiki na ruhu. Idan akwai jiki na zahiri, akwai jiki na ruhu ma. 45 Haka yake a rubuce cewa: “Mutum na farko wato Adamu ya zama mai rai.” Adamu na ƙarshe ya zama ruhu mai ba da rai. 46 Amma ba na ruhun ne farko ba. Na zahirin ne farko, kuma bayan hakan sai na ruhun. 47 Mutum na farko ya fito daga duniya kuma an yi shi da ƙurar ƙasa; mutum na biyu ya fito daga sama. 48 Kamar mutumin da aka yi da ƙurar ƙasa, haka ma yake da waɗanda aka yi da ƙurar ƙasa; kuma kamar yadda yake da wanda yake na sama, haka yake da waɗanda suke na sama. 49 Kamar yadda muka ɗauki kamannin wanda aka yi da ƙurar ƙasa, za mu kuma ɗauki kamannin wanda yake na sama.
50 Amma ina gaya muku ꞌyanꞌuwana cewa, nama da jini ba za su gāji Mulkin Allah ba, kuma ruɓewa ba zai gāji rashin ruɓewa ba. 51 Ku saurara in gaya muku wani asiri mai tsarki: Ba dukanmu ne za mu mutu ba, amma za a canja dukanmu, 52 cikin ƙanƙanin lokaci, da ƙyiftawar ido, saꞌad da aka busa kakaki na ƙarshe. Gama za a busa kakakin, kuma matattu za su tashi da jikin da ba ya ruɓewa, kuma za a canja mu. 53 Don dole ne jiki mai ruɓewa ya canja zuwa marar ruɓewa, kuma dole ne jikin da yake mutuwa ya canja ya zama jikin da ba ya mutuwa. 54 Amma saꞌad da jiki mai ruɓewa ya canja zuwa marar ruɓewa, kuma saꞌad da jiki mai mutuwa ya canja zuwa marar mutuwa, a lokacin ne maganar nan za ta cika, wato: “An haɗiye mutuwa har abada.” 55 “Ke mutuwa, ina nasararki? Ke mutuwa, ina dafinki?” 56 Dafin da ke jawo mutuwa shi ne zunubi, kuma ikon zunubi shi ne Doka.* 57 Amma godiya ga Allah, domin yana ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kristi!
58 Saboda haka, ꞌyanꞌuwana waɗanda nake ƙauna, ku tsaya daram, kada ku jijjigu, a kullum ya zama cewa kuna yin ayyuka da yawa a hidimar Ubangiji, domin kun san cewa aikin Ubangiji da kuke yi ba a banza ba ne.