Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
7 Yanzu, game da batutuwan da kuka rubuto, ai gwamma kada namiji ya taɓa* ta mace; 2 amma saboda mutane da yawa suna yin lalata,* bari kowane namiji ya samu nasa mata kuma kowace mace ta samu nata mijin. 3 Bari maigida ya ba wa matarsa hakkinta, kuma matar ma ta ba wa mijinta hakkinsa. 4 Matar ba ta da iko a kan jikinta, amma mijinta ne yake da iko a kan jikinta; haka ma, maigidan ba shi da iko a kan jikinsa, amma matar ce take da iko a kan jikinsa. 5 Kada ku hana juna, sai dai ko ku biyun kun yarda ku yi hakan na ɗan lokaci, don ku iya keɓe lokaci saboda adduꞌa kuma ku sake haɗuwa don kada Shaiɗan ya ci-gaba da jarrabtar ku saboda rashin kamun kanku. 6 Amma wannan shawara ce ba umurni ba. 7 Da ma a ce kowa yana kamar yadda nake. Amma kowa yana da baiwa da Allah ya ba shi, wani yana da irin wannan, wani kuma yana da irin wancan.
8 Yanzu ga marasa aure da matan da mazajensu sun mutu, ina cewa zai fi kyau su kasance yadda nake. 9 Amma idan ba za su iya kame kansu ba, sai su yi aure, domin gwamma mutum ya yi aure da ya yi ta fama da shaꞌawar yin jimaꞌi.
10 Ga maꞌaurata ina ba da umurni, ba ni nake magana ba, amma Ubangiji ne, cewa, kada mata ta rabu da mijinta. 11 Amma idan ta rabu da mijinta, kada ta sake yin wani aure, maimakon haka, ta koma ta yi sulhu da maigidanta; kuma kada maigida ya bar matarsa.
12 Ga sauran, ni nake wannan magana ba Ubangiji ba cewa: Idan wani ɗanꞌuwa yana da mata marar bi kuma ta yarda ta ci-gaba da zama da shi, kada ya bar ta; 13 kuma idan mace tana da maigida marar bi kuma ya yarda ya ci-gaba da zama da ita, kada ta bar mijinta. 14 Gama an tsarkake maigida marar bi saboda matarsa, kuma an tsarkake mata marar bi saboda ɗanꞌuwan; in ba haka ba, ꞌyaꞌyanku za su zama marasa tsarki, amma yanzu suna da tsarki. 15 Idan kuma marar bin ya zaɓi ya tafi,* bari ya tafi; idan hakan ya faru, ba dole ne ɗanꞌuwan ko ꞌyarꞌuwar ta ci-gaba da zama da marar bin ba, amma Allah ya kira ku don ya ba ku salama. 16 Ke mace, ta yaya kika san cewa ba za ki iya ceci maigidanki ba? Ko kuma, kai maigida, ta yaya ka san cewa ba za ka iya ceci matarka ba?
17 Kamar yadda Jehobah* ya ba wa kowa rabonsa, bari kowa ya yi tafiya daidai da yadda Allah ya kira shi. Saboda haka, ina ba da wannan umurnin a dukan ikilisiyoyi. 18 Shin akwai wanda ya riga ya yi kaciya saꞌad da aka kira shi? To kada ya zama marar kaciya. Akwai wani da aka kira shi saꞌad da bai yi kaciya ba? To kada ya yi kaciya. 19 Kaciya ba kome ba ne, kuma rashin kaciya ma ba kome ba ne; abin da yake da muhimmanci shi ne kiyaye dokokin Allah. 20 A duk yanayin da aka kira kowane mutum, bari ya ci-gaba da kasancewa a yanayin. 21 Kai bawa ne saꞌad da aka kira ka? Kada hakan ya dame ka; amma idan za ka iya samun ꞌyanci to sai ka yi amfani da damar. 22 Gama duk wanda aka kira shi saꞌad da yake bawa shi mai ꞌyanci ne na Ubangiji, haka ma duk wanda yake da ꞌyanci saꞌad da aka kira shi, shi bawan Kristi ne. 23 Allah ya saye ku da tsada; ku daina zama bayin mutane. 24 ꞌYanꞌuwana, a duk wani yanayin da aka kira kowane mutum, bari ya ci-gaba da kasancewa a yanayin a gaban Allah.
25 Game da waɗanda ba su taɓa yin aure ba, ba ni da wani umurni daga wurin Ubangiji, amma ina faɗan raꞌayina a matsayin wanda Ubangiji ya nuna masa jinƙai don ya zama mai aminci.* 26 Ina ganin zai fi wa mutum ya ci-gaba da zama yadda yake saboda wahalolin da ake fama da su yanzu. 27 Ka yi aure ne? Ka daina ƙoƙarin rabuwa da matarka. Ba ka yi aure ba? Ka daina neman aure. 28 Amma ko da ka yi aure, ba ka yi zunubi ba. Kuma idan wanda bai taɓa yin aure ba ya yi aure, bai yi zunubi ba. Amma waɗanda suka yi aure, za su sha wahala a jikinsu. Kuma ina so in kāre ku daga hakan.
29 Ƙari ga haka, ꞌyanꞌuwana, abin da nake faɗa shi ne, lokacin da ya rage kaɗan ne. Daga yanzu, bari waɗanda suke da mata su yi kamar ba su da mata, 30 waɗanda suke kuka, kamar waɗanda ba sa kuka, waɗanda suke farin ciki, kamar waɗanda ba sa farin ciki, kuma waɗanda suke sayan abubuwa, kamar waɗanda ba su da kome, 31 waɗanda suke amfani da duniya, kamar ba sa amfani da ita sosai; domin yanayin duniyar nan yana canjawa. 32 Hakika, ina so ku sami ꞌyanci daga yawan damuwa. Mutumin da bai yi aure ba, yana yawan damuwa a kan ayyukan Ubangiji, game da yadda zai samu amincewar Ubangiji. 33 Amma mutumin da ya yi aure yana yawan damuwa a kan abubuwan duniya, game da yadda zai sami amincewar matarsa, 34 kuma hankalinsa ya rabu biyu. Ƙari ga haka, macen da ba ta yi aure ba tana yawan damuwa a kan ayyukan Ubangiji don ta kasance da tsarki a jikinta da kuma ruhunta, haka ma budurwa. Amma macen da ta yi aure tana yawan damuwa game da abubuwan duniya, yadda za ta iya samun amincewar maigidanta. 35 Ina faɗan abubuwan nan ne domin amfanin ku, ba don in hana ku yin wani abu ba, amma don in sa ku yi abin da ya dace, kuma ku ci-gaba da bauta wa Ubangiji ba tare da wani abu ya raba hankalinku ba.
36 Idan wani yana ganin yana yin abin da bai dace ba saboda bai yi aure ba, kuma lokacin ƙuruciyarsa* ta wuce, ga abin da ya kamata ya faru: Bari ya yi abin da yake so; bai yi zunubi ba. Sai su yi aure. 37 Amma mutumin da ya yanke shawara a zuciyarsa kuma ba ya bukatar yin aure, amma yana iya kame kansa kuma ya riga ya yanke shawara a zuciyarsa cewa ba zai yi aure ba, hakan zai zama shawara mai kyau. 38 Wanda ya yi aure ma ya yanke shawara mai kyau, amma wanda bai yi aure ba, ya yanke shawara mafi kyau.
39 Mace ba za ta rabu da maigidanta ba, muddin yana nan da rai. Amma idan mijinta ya mutu,* tana da ꞌyancin auran duk wanda take so, amma dai mai bin Ubangiji kaɗai. 40 Amma a raꞌayina za ta fi yin farin ciki idan ta kasance yadda take; kuma ina da tabbacin cewa ruhun Allah yana tare da ni ma.