Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
3 Saboda haka ꞌyanꞌuwana, ban iya na yi muku magana kamar waɗanda suke rayuwa bisa ga ruhu ba, sai dai kamar waɗanda suke rayuwa bisa ga shaꞌawoyin jiki, kamar jarirai cikin Kristi. 2 Na ba ku madara, ba abinci mai kauri ba, domin ba ku yi ƙarfi ba tukuna. Gaskiyar ita ce, har yanzu ma ba ku yi ƙarfi yadda ya kamata ba, 3 gama har ila kuna rayuwa bisa shaꞌawoyin jiki. Da yake akwai kishi da faɗa a tsakaninku, ba kuna rayuwa bisa ga shaꞌawoyin jiki ba, kuma ba kuna rayuwa kamar yadda mutane suke yi ba? 4 Idan wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” amma wani ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba halin mutanen duniya kuke nunawa ba?
5 To, wane ne Afollos? Kuma wane ne Bulus? Dukansu masu hidima ne da kuka ba da gaskiya ta wurinsu, daidai yadda Ubangiji ya ba wa kowannensu aiki. 6 Ni na shuka, Afollos ne ya yi ban ruwa, amma Allah ne ya ci-gaba da sa irin ya yi girma, 7 don haka, ba wanda ya shuka ko wanda ya yi ban ruwa ne ya kamata a yaba wa ba, amma Allah wanda ya sa shukar ta yi girma ne. 8 Wanda ya yi shukin da wanda ya yi ban ruwa nufinsu ɗaya ne, amma kowannensu zai samu nasa lada daidai da aikinsa. 9 Gama mu abokan aiki ne na Allah. Ku kuwa gonar Allah ce da ake aiki a ciki, ginin Allah kuma.
10 Ta wurin alherin Allah da aka ba ni, na kafa tushen ginin kamar ƙwararren magini, amma wani yana gini a kai. Bari kowa ya ci-gaba da lura da yadda yake yin gini a kai. 11 Gama babu wani da zai iya kafa wani tushe dabam da wanda aka riga aka kafa, wato Yesu Kristi. 12 Idan wani ya yi gini a kan tushen nan da zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ciyawa, ko kuma kara, 13 Za a ga aikin kowa, gama za a bayyana aikin da wuta a ranar, domin wutar za ta nuna irin ginin da kowa ya yi. 14 Idan ginin da mutumin ya yi ya ci-gaba da tsayawa, zai sami lada; 15 idan aikin mutumin ya ƙone, zai yi hasara, amma za a cece shi; idan hakan ya faru, kamar dai mutumin ya bi ta cikin wuta ne.
16 Ba ku sani cewa ku haikalin Allah ne, kuma ruhun Allah yana zama a cikinku ba? 17 Idan wani ya hallaka haikalin Allah, Allah zai hallaka shi; domin haikalin Allah yana da tsarki, kuma ku ne haikalin.
18 Kada ku ruɗi kanku: Idan wani cikinku yana tunanin cewa yana da hikima a wannan zamanin,* bari ya zama wawa don ya iya zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyar nan wawanci ne a wurin Allah, domin a rubuce yake cewa: “Yakan kama masu hikima a cikin wayonsu.” 20 An sake rubuta cewa: “Jehobah* ya san cewa tunanin masu hikima banza ne.” 21 Kada wani ya yi taƙama da mutum; gama kome naku ne, 22 ko da Bulus ne, ko Afollos, ko Kefas* ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwan da suke nan yanzu, ko abubuwa masu zuwa, duk naku ne; 23 ku kuwa na Kristi ne; Kristi kuma na Allah ne.