Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
14 Ku nace wajen nuna ƙauna, kuma ku ci-gaba da yin iya ƙoƙarinku don ku sami baiwa iri-iri da ruhu mai tsarki yake bayarwa, musamman ma na yin annabci. 2 Domin wanda yake magana a harsuna, ba da mutane yake magana ba, amma da Allah yake yi, gama babu mai saurara, domin abin da yake faɗa asirai masu tsarki ne ta wurin ruhu. 3 Amma wanda yake annabci yana gina mutane, da ƙarfafa su, da kuma taꞌazantar da su ta wajen maganarsa. 4 Wanda yake magana a harsuna yana gina kansa ne, amma wanda yake annabci yana gina ikilisiya ne. 5 Zan so dukanku ku yi magana a harsuna, amma na fi so ku yi annabci. Wanda yake yin annabci ya fi wanda yake yin magana a harsuna, sai dai ko ya fassara don ya iya gina ikilisiyar. 6 Amma yanzu ꞌyanꞌuwa, idan na zo wurinku ina yi muku magana a harsuna, ta yaya hakan zai amfane ku, idan ban yi magana da wahayi ko ilimi ko annabci ko kuma koyarwa ba?
7 Haka ma yake da abubuwa marasa rai da suke ba da sauti, kamar sarewa, ko molo. Idan sautinsu bai fita sosai ba, ta yaya wani zai san abin da ake busawa ko kuma kaɗawa? 8 Idan ba a busa kakaki daidai yadda za a gane ba, wa zai yi shirin yaƙi? 9 Haka nan ma, in ba dai kun yi wa mutane magana da kalmomi da ke da sauƙin fahimta ba, ta yaya mutum zai gane abin da kuke faɗa? A gaskiya, maganarku tana bin iska ne kawai. 10 Mai yiwuwa akwai furuci dabam-dabam a duniya, kuma kowannensu yana da maꞌana. 11 Idan ban fahimci abin da furucin yake nufi ba, na zama baƙo ga mai magana, kuma mai maganan ma zai zama baƙo a gare ni. 12 Haka yake a gare ku, da yake kuna da niyyar samun baiwa iri-iri na ruhu, ku yi ƙoƙarin samun baiwa da za su gina ikilisiya.
13 Don haka, bari wanda yake magana a harsuna ya yi adduꞌa don ya iya fassara maganarsa. 14 Gama idan ina adduꞌa a harsuna, baiwar da ruhu ya ba ni ne yake yin adduꞌa, amma tunanina ba ya fahimtar abin da nake faɗa. 15 To, me zan yi ke nan? Zan yi adduꞌa da baiwar da ruhu ya ba ni, amma kuma zan yi adduꞌa da tunanina. Zan rera yabo da baiwar da ruhu ya ba ni, amma kuma zan rera yabo da tunanina. 16 In ba haka ba, idan ka ba da godiya da kyautar da ruhu ya ba ka, ta yaya marar sani da ke tsakaninku zai ce “Amin” ga godiyar da ka bayar, da yake bai san abin da kake faɗa ba? 17 A gaskiya, kana miƙa godiya a hanyar da ta dace, amma hakan ba ya gina ɗayan mutumin. 18 Ina gode wa Allah domin ina yin magana a harsuna dabam-dabam fiye da dukanku. 19 Amma a cikin ikilisiya gwamma in yi magana da kalmomi biyar da tunanina* don in koyar da wasu ma, maimakon in yi magana da kalmomi dubu goma a harsuna.
20 ꞌYanꞌuwa, kada ku zama kamar yara a yadda kuke tunani, amma ku zama kamar yara wajen yin mugunta; kuma ku zama manya a yadda kuke tunani. 21 An rubuta a cikin Doka* cewa: “‘Da harsunan mutanen wata ƙasa da kuma leɓunan baƙi zan yi magana da mutanen nan, duk da haka, za su ƙi su saurare ni,’ in ji Jehobah.”* 22 Don haka, harsuna ba alama ba ce don masu bi, amma don marasa bi ne. Annabci kuwa ba don marasa bi ba ne amma don masu bi ne. 23 Don haka, idan dukan ikilisiyar suka taru wuri ɗaya, suka soma magana a harsuna, kuma marasa sani ko marasa bi suka shigo, ba za su ɗauka cewa kun haukace ba? 24 Amma in dukanku kuna annabci kuma marar bi ko marar sani ya shigo, abin da muke faɗa zai zama gargaɗi a gare shi kuma zai sa ya bincika kansa sosai. 25 Asiran zuciyarsa kuma za su bayyana a fili, don haka zai faɗi da fuskarsa a ƙasa kuma ya yi wa Allah sujada, yana cewa: “A gaskiya Allah yana cikinku.”
26 To ꞌyanꞌuwa, mene ne ya kamata ku yi? Saꞌad da kuka taru, wani yana da zabura da zai rera, wani yana da koyarwa, wani yana da wahayi, wani yana magana da harsuna, wani kuma yana fassara. Ku yi kome don ku gina juna. 27 Kuma idan wasu suna magana a harsuna, kada ya wuce mutum biyu, in ya yi yawa, mutum uku, kuma su yi shi bi da bi. Ƙari ga haka, dole ne wani ya fassara abin da suke faɗa. 28 Amma idan babu mai fassara, sai ya yi shuru a cikin ikilisiya, kuma ya yi magana ga kansa da Allah. 29 Bari annabawa biyu ko uku su yi magana, kuma sauran mutane su gane maꞌanar abin da suka faɗa. 30 Amma idan wani ya sami wahayi saꞌad da yake zaune a wurin, sai wanda yake magana ya yi shuru. 31 Gama dukanku za ku iya yin annabci ɗaya bayan ɗaya, domin kowa ya koyi darasi kuma ya samu ƙarfafa. 32 Kuma ya kamata annabawan su kame kansu yayin da suke amfani da baiwar da ruhun ya ba su. 33 Gama Allah ba Allah na rikicewa* ba ne, amma Allah ne na salama.
Kamar yadda yake a dukan ikilisiyoyin tsarkaka, 34 bari mata su yi shuru a cikin ikilisiyoyi, domin ba a yarda musu su yi magana ba. A maimako, sai dai su miƙa kansu kamar yadda Doka ma ta faɗa. 35 Idan suna so su koya wani abu, sai su tambayi mazajensu a gida, don abin kunya ne mace ta yi magana a cikin ikilisiya.
36 Daga wurinku ne kalmar Allah ta fito, ko kuma ta isa wurinku ne kawai?
37 Idan wani yana ganin shi annabi ne, ko kuma yana da baiwar da ruhu yake bayarwa, dole ya yarda cewa abin da nake rubuta muku umurni ne daga wurin Ubangiji. 38 Amma idan wani ya yi watsi da wannan, shi ma za a yi watsi da shi.* 39 Saboda haka, ꞌyanꞌuwana, ku ci-gaba da yin iya ƙoƙarinku don ku yi annabci, kuma kada ku haramta yin magana a harsuna. 40 Amma a yi kome daidai yadda ya kamata kuma a yi hakan cikin tsari.*