Ayyukan Manzanni
22 “ꞌYanꞌuwana da ubannina, ku saurara in bayyana muku abin da ya faru.” 2 Saꞌad da suka ji yana musu magana da Ibrananci, sai suka ƙara yin shuru, kuma ya ce: 3 “Ni Bayahude ne, kuma an haife ni a Tarsus na Kilikiya, amma na yi makaranta a birnin nan, a ƙarƙashin Gamaliyel. An koyar da ni in bi dukan abubuwan da ke cikin Dokokin* da kakanninmu suka bi, kuma na yi ƙwazo a yin aikin Allah kamar yadda dukanku kuke yi a yau. 4 Na tsananta wa masu bin Hanyar Ubangiji, har ma na kashe su, na ɗaure maza da mata, kuma na aika su kurkuku, 5 shugaban firistoci da dukan taron dattawa za su iya shaida hakan. Don daga wurinsu ne na karɓi wasiƙu game da ꞌyanꞌuwa da ke Damaskus, kuma ina kan hanya in kama waɗanda suke wurin, in kuma kawo su Urushalima a ɗaure don a hukunta su.
6 “Amma, da nake tafiya kuma na yi kusa da Damaskus da tsakar rana, sai nan take, haske daga sama ya haskaka kewaye da ni, 7 sai na faɗi a ƙasa kuma na ji wata murya da ta ce mini: ‘Shawulu, Shawulu, me ya sa kake tsananta mini?’ 8 Sai na amsa na ce: ‘Wane ne kai, Ubangiji?’ Kuma ya ce mini: ‘Ni ne Yesu mutumin Nazaret, wanda kake tsananta masa.’ 9 Mutanen da suke tare da ni sun ga hasken, amma ba su ji muryar wanda yake yi mini magana ba. 10 Da jin haka, sai na ce: ‘Me ya kamata in yi, Ubangiji?’ Sai Ubangijin ya ce mini: ‘Ka tashi ka je cikin Damaskus, a wurin akwai wanda zai gaya maka duk abubuwan da ya kamata ka yi.’ 11 Tun da yake na kasa ganin kome saboda tsananin hasken, mutanen da suke tare da ni sun riƙe hannuna kuma sun ja-gorance ni zuwa Damaskus.
12 “Sai wani mutum mai suna Hananiya, mai bauta wa Allah sosai bisa Doka, wanda dukan Yahudawa masu zama a wurin sun faɗi abubuwa masu kyau game da shi, 13 ya zo wurina. Ya tsaya kusa da ni ya ce mini: ‘Ɗanꞌuwa Shawulu, ka soma gani!’ Nan take sai na ɗaga idanuna kuma na gan shi. 14 Sai ya ce: ‘Allahn kakanninmu ya zaɓe ka don ka san nufinsa, ka ga mai adalcin nan, kuma ka ji magana daga bakinsa, 15 domin za ka zama shaidarsa ga dukan mutane game da abubuwan da ka gani, kuma ka ji. 16 Don me kake ɓata lokaci? Ka tashi a yi maka baftisma, kuma idan ka kira ga sunan Yesu, za a wanke zunubanka.’
17 “Amma bayan da na dawo Urushalima kuma ina adduꞌa a cikin haikali, sai na ga wahayi, 18 kuma na ga Ubangiji yana ce mini: ‘Ka yi sauri ka fita daga Urushalima, domin ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’ 19 Sai na ce: ‘Ubangiji, sun san cewa a dā nakan je majamiꞌu ɗaya bayan ɗaya, don in saka waɗanda suka ba da gaskiya a gare ka cikin kurkuku kuma in yi musu bulala. 20 Ban da haka, a lokacin da aka kashe Istifanus mashaidinka, ina tsaye a wurin, na amince da abin da suke yi, kuma ina gadin mayafin waɗanda suka kashe shi.’ 21 Duk da haka ya ce mini: ‘Ka tafi, domin zan aike ka zuwa wurin alꞌummai masu nisa.’”
22 Sun ci-gaba da saurarar sa har lokacin da ya furta wannan kalmar. Saꞌan nan suka ta da muryoyinsu suna cewa: “A kashe irin wannan mutumin, bai cancanci ya rayu ba!” 23 Da yake suna ta ihu, suna jefa mayafansu, kuma suna ta da ƙura, 24 sai shugaban sojojin ya ce a kai Bulus cikin barikin sojojin kuma a yi masa bulala saꞌad da ake yi masa tambayoyi, don yana so ya san ainihin dalilin da ya sa jamaꞌar suka ce a kashe Bulus. 25 Saꞌad da aka ɗaure Bulus domin a yi masa bulala, sai ya ce wa jamiꞌin soja da ke tsaye a wurin: “Ya dace bisa doka ka yi wa ɗan ƙasar Roma bulala ba tare da an yi masa shariꞌa ba?” 26 Saꞌad da jamiꞌin sojan ya ji hakan, sai ya je wurin shugaban sojojin ya gaya masa hakan, kuma ya ce: “Mene ne kake so ka yi haka? Shi ɗan ƙasar Roma ne fa.” 27 Sai shugaban sojojin ya zo wurin Bulus kuma ya tambaye shi: “Ka gaya mini, kai ɗan ƙasar Roma ne?” Sai ya ce: “E.” 28 Sai shugaban sojojin ya amsa ya ce: “Na kashe kuɗi mai yawa kafin na sami izinin zama ɗan ƙasar Roma.” Bulus ya ce: “Ni ɗan ƙasar Roma ne tun da aka haife ni.”
29 Nan da nan, mutanen da suke shirin yi masa bulala saꞌad da suke masa tambayoyi suka ja da baya; sai tsoro ya kama shugaban sojojin saꞌad da ya ji cewa Bulus mutumin Roma ne, kuma ga shi ya ɗaure shi da sarƙoƙi.
30 Washegari, da yake shugaban sojojin yana so ya san ainihin dalilin da ya sa Yahudawan suke zargin Bulus, sai ya sake shi, kuma ya umurci manyan firistoci da dukan Sanhedrin* su taru. Sai ya kawo Bulus kuma ya sa shi ya tsaya a tsakaninsu.