Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
7 Saboda haka ƙaunatattuna, da yake an yi mana waɗannan alkawura, bari mu tsabtace kanmu daga kowace irin ƙazanta na jiki da na ruhu, mu kuma zama da cikakken tsarki a cikin tsoron Allah.
2 Ku karɓe mu a zuciyarku. Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, kuma ba mu cuci kowa ba. 3 Ban faɗi hakan don in ɗaura muku laifi ba, don dā na faɗa cewa kuna cikin zukatanmu don mu mutu tare kuma mu rayu tare. 4 Ina da ꞌyancin yin magana a gare ku. Ina taƙama sosai da ku. Zuciyata tana cike da ƙarfafa;* ina cike da farin ciki, duk da wahalolin da muke sha.
5 A gaskiya, saꞌad da muka isa Makidoniya, ba mu samu hutu ba ko kaɗan,* amma mun ci-gaba da shan wahala a kowace hanya—akwai rikici a waje, a ciki kuma akwai tsoro. 6 Amma Allah, wanda yake ƙarfafa* waɗanda suke baƙin ciki, ya ƙarfafa mu ta wurin zuwan Titus; 7 kuma ba ta wurin zuwansa kaɗai ba, amma har ta wurin ƙarfafar da ya samu saboda ku, yayin da yake gaya mana yadda kuke marmarin gani na, da yadda kuke baƙin ciki sosai, da kuma yadda kuka damu da ni da dukan zuciyarku; kuma hakan ya ƙara sa ni farin ciki.
8 Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙar da na rubuta muku, ba na da-na-sani don hakan. Ko da yake da farko na yi da-na-sani (ganin cewa wasiƙar ta sa ku baƙin ciki, duk da cewa na ɗan lokaci ne kawai), 9 yanzu ina farin ciki, ba kawai domin kun yi baƙin ciki ba, amma domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki irin wanda Allah yake so, don babu wani mummunan abu da ya faru da ku saboda mu. 10 Baƙin ciki irin wanda Allah yake so yana kai ga samun ceto; ba ya sa mutum ya yi da-na-sani, amma baƙin ciki irin na duniya, yana kai ga mutuwa. 11 Ku duba ku gani irin amfanin da kuka samu domin kun yi baƙin ciki irin wanda Allah yake so, hakika, kun wanke kanku daga zargi, kun yi baƙin ciki don laifin, kun ji tsoron Allah, kun yi niyyar tuba, kun bauta wa Allah da ƙwazo, kun ɗauki mataki don laifin. A kowace hanya kun yi abubuwa daidai don ku magance wannan matsalar. 12 Ko da yake na rubuta muku wasiƙa, ban yi hakan don wanda ya yi laifin, ko wanda aka yi wa laifin ba, a maimakon haka, na rubuta muku ne don in ga ko za ku nuna a gaban Allah cewa kuna marmarin bin abin da muka gaya muku. 13 Shi ya sa muka sami ƙarfafa.
Amma ban da ƙarfafar da muka samu, mun yi farin ciki sosai, don Titus yana farin ciki, saboda dukanku kun ƙarfafa shi. 14 Gama idan na yi taƙama da ku a gabansa, ban sha kunya ba; amma kamar yadda duk abubuwan da muka gaya muku gaskiya ne, haka ma taƙamar da muka yi a gaban Titus ta zama gaskiya. 15 Haka ma, ƙaunarsa a gareku tana ta ƙaruwa yayin da yake tunawa da biyayyar dukanku, da yadda kuka karɓe shi da girmamawa* sosai. 16 Na yi farin ciki domin a kome zan iya yarda da ku.*