Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
6 Idan wani a cikinku ya samu saɓani da ɗanꞌuwansa, me ya sa zai kai shi kotu a gaban marasa adalci, maimakon ya kai shi gaban tsarkaka? 2 Ko ba ku sani ba cewa tsarkaka ne za su shariꞌanta duniya ba? Kuma idan ku ne za ku yi wa duniya shariꞌa, ai kun cancanci ku yi shariꞌa a kan ƙananan batutuwa, ko ba haka ba? 3 Ba ku san cewa za mu yi wa malaꞌiku shariꞌa ba? To me ya sa ba za mu iya yin shariꞌa a kan batutuwa da suka shafi rayuwar duniya ba? 4 Idan kuna bukatar ku yi shariꞌa a kan irin batutuwan nan, shin mutanen da ba su isa kome ba a idon ikilisiya ne kuke naɗawa a matsayin alƙalai? 5 Ina magana ne don in kunyatar da ku. Shin babu wani mai hikima a cikinku da zai iya yin shariꞌa tsakanin ꞌyanꞌuwansa ne? 6 A maimakon haka, ɗanꞌuwa yakan kai ƙarar ɗanꞌuwa kotu, a gaban marasa bangaskiya!
7 Ai kasawa ce a gare ku tun da kuna kai juna kotu. Me ya sa ba za ku ƙyale a yi muku laifi ba? Kuma me ya sa ba za ku bari a cuce ku ba? 8 A maimakon haka, ꞌyanꞌuwanku ne kuka yi wa laifi, kuma kuna cucin su!
9 Ko dai ba ku sani ba cewa marasa adalci ba za su gāji Mulkin Allah ba? Kada a ruɗe ku. Masu yin lalata,* da masu bautar gumaka, da masu yin zina, da maza da ke barin wasu maza su kwana da su, da maza masu kwana* da maza, 10 da ɓarayi, da masu haɗama, da masu buguwa, da masu zage-zage, da kuma masu damfara, ba za su gāji Mulkin Allah ba. 11 Haka wasu cikinku suke a dā. Amma an wanke ku; an tsarkake ku; kuma an mai da ku masu adalci cikin sunan Ubangiji Yesu Kristi da kuma ruhun Allahnmu.
12 Ina da damar yin dukan abubuwan da nake so, amma ba dukan abubuwa ba ne suke da amfani. Ina da damar yin dukan abubuwan da nake so, amma ba zan bar wani abu ya yi iko a kaina ba. 13 An yi abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci, amma Allah zai sa dukansu su shuɗe. An yi jiki ba don lalata* ba, amma don Ubangiji, Ubangiji kuma don jiki ne. 14 Allah ya ta da Ubangiji kuma mu ma zai ta da mu daga mutuwa da ikonsa.
15 Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kristi ne ba? Shin zai dace in ɗauki gaɓoɓin Kristi in haɗa su da na karuwa? Ba zan yi haka ba ko kaɗan! 16 Ba ku sani ba cewa duk wanda ya haɗa kansa da karuwa, ya zama jiki ɗaya da ita ba? Gama Allah ya ce, “su biyun za su zama jiki ɗaya.” 17 Amma duk wanda ya haɗa kansa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi a cikin ruhu. 18 Ku guji yin lalata!* Duk wani zunubi da mutum ya yi ba zai shafi jikinsa ba, amma duk mutumin da ya yi lalata, ya yi wa jikinsa zunubi ne. 19 Ba ku sani ba cewa jikinku shi ne haikalin ruhu mai tsarki da ke cikinku, da kuka samo daga wurin Allah ba? Kuma, ba ku ne kuke da iko a kanku ba, 20 gama an saye ku da tsada. Saboda haka, ko ta yaya, ku girmama Allah da jikinku.