Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
4 Ya kamata mutum ya ɗauke mu a matsayin masu hidima na Kristi da kuma waɗanda aka ba su riƙon amanar asirai masu tsarki na Allah. 2 Saboda haka, abin da ake bukata daga waɗanda aka ba su amanar shi ne su kasance da aminci. 3 A gare ni, ba shi da muhimmanci sosai ku, ko wani kotu ya bincika ni. Gaskiyar ita ce, ba na ma bincika kaina. 4 Ban san da wani laifin da na yi ba. Amma hakan ba ya nuna cewa ni mai adalci ne; wanda yake bincika ni shi ne Jehobah.* 5 Saboda haka, kada ku shariꞌanta kome tun lokaci bai yi ba, har sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake ɓoye a cikin duhu, zai nuna abin da ke cikin zukatan mutane, kuma kowa zai samu nasa yabo daga wurin Allah.
6 ꞌYanꞌuwana, abubuwan nan da na gaya muku game da ni da Afollos don ku amfana ne kuma ku koyi wannan darasin cewa: “Kada ku yi fiye da abubuwan da aka rubuta,” don kada ku cika da girman kai, kuna ɗaukan wani da muhimmanci fiye da wani. 7 Wa ya mai da kai da muhimmanci fiye da wani? Hakika, mene ne kake da shi wanda ba wani ne ya ba ka ba? Idan da gaske ne cewa wani ne ya ba ka, to, me ya sa kake taƙama kamar dai ba wani ne ya ba ka ba?
8 Kun riga kun sami abin da kuke so ne? Kun riga kun zama masu arziki ne? Kun soma sarauta ne ba tare da mu ba? Na so da a ce kun riga kun soma sarauta, domin mu ma mu yi sarauta tare da ku. 9 A ganina, Allah ya sa mu manzanni a rukuni na ƙarshe a fagen wasa, kamar mutanen da aka yanke musu hukuncin kisa, don mun zama kamar ꞌyan wasa a fage ga duniya, da malaꞌiku, da kuma mutane. 10 Mu wawaye ne saboda Kristi, amma ku masu hikima ne a cikin Kristi; ba mu da ƙarfi, amma kuna da ƙarfi; ana mutunta ku, mu kuma ana rena mu. 11 Har zuwa wannan lokacin, mun ci-gaba da fama da yunwa, da ƙishin ruwa, da ƙarancin kayan sakawa, da dūka, da kuma rashin gida, 12 da wahala, kuma muna aiki da hannayenmu. Saꞌad da aka zage mu, mukan albarkace su; saꞌad da aka tsananta mana, mukan yi haƙuri mu jimre; 13 saꞌad da aka ɓata sunanmu, mukan yi musu magana cikin salama; mun zama kamar bola a duniya, abin da kowa ke ƙyama har wa yau.
14 Ina rubuta waɗannan abubuwan, ba don in kunyatar da ku ba, amma don in gargaɗe ku a matsayin yarana waɗanda nake ƙauna. 15 Ko da yake kuna da mutane dubu goma masu yi muku ja-goranci game da yadda za ku bi Kristi, a gaskiya ba ku da ubanni da yawa, amma na zama ubanku cikin Kristi Yesu, da yake na kawo muku labari mai daɗi. 16 Don haka, ina roƙon ku ku yi koyi da ni. 17 Shi ya sa nake aika muku Timoti, domin shi ɗana ne da nake ƙauna, kuma yana da aminci cikin Ubangiji. Zai tuna muku yadda nake yin abubuwa a cikin hidimar Kristi Yesu, kamar yadda nake koyarwa a koꞌina a kowace ikilisiya.
18 Wasu suna ganin ba zan zo kuma ba, har sun soma fahariya. 19 Amma zan zo wurinku ba da daɗewa ba, idan nufin Jehobah* ne, zan kuma duba in ga ikon da masu fahariyar nan suke da shi, ba maganganunsu ba. 20 Gama Mulkin Allah ba batun maganar baki ba ne, amma batun iko ne. 21 Wanne ne kuka fi so? In zo muku da sanda ne, ko kuwa da ƙauna da kuma rashin zafin rai?