Ta Hannun Matiyu
8 Bayan da Yesu ya sauko daga kan tudun, taron jamaꞌa sun bi shi. 2 Sai wani kuturu ya zo, kuma ya rusuna a gabansa yana cewa: “Ubangiji idan kana so, za ka iya warkar da ni.” 3 Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa mutumin, ya ce: “E, ina so! Na warkar da kai.” Nan da nan mutumin ya warke daga cutar kuturtar. 4 Sai Yesu ya ce masa: “Kada ka gaya wa kowa, amma ka je ka nuna kanka a wurin firist, kuma ka miƙa hadaya da Musa ya ce a bayar, don su ga cewa an warkar da kai.”
5 Saꞌad da ya shiga Kafarnahum, sai wani jamiꞌin soja* ya zo yana roƙon sa 6 yana cewa: “Ubangiji, bawana yana kwance a gida, yana fama da ciwo da ke hana shi motsawa kuma yana shan wahala sosai.” 7 Sai Yesu ya ce masa: “Idan na kai wurin, zan warkar da shi.” 8 Sai jamiꞌin sojan ya ce: “Ubangiji, ban cancanci ka shiga gidana ba, amma ka yi maganar a nan kawai, kuma bawana zai warke. 9 Domin ni ma mutum ne mai iko, ina da sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce ma wannan, ‘Je ka!’ sai ya je, wani kuma in ce masa ‘Zo!’ sai ya zo, bawana kuma nakan ce masa, ‘Yi abu kaza!’ sai ya yi.” 10 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki kuma ya ce wa masu bin sa: “Ina gaya muku gaskiya, ban taɓa ganin mutum a Israꞌila da yake da bangaskiya sosai kamar wannan ba. 11 Amma ina gaya muku, mutane da yawa daga gabas da yamma, za su zo su ci abinci a teburi tare da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, a Mulkin sama; 12 amma waɗanda ya kamata su gāji Mulkin, za a jefar da su waje cikin duhu. A wurin ne za su yi ta kuka da cizon haƙora.” 13 Sai Yesu ya ce wa jamiꞌin sojan: “Ka koma gida. Kamar yadda ka ba da gaskiya, bari hakan ya faru maka.” Nan da nan bawansa ya warke.
14 Da Yesu ya shiga gidan Bitrus, sai ya ga mamar matar Bitrus a kwance, tana fama da zazzaɓi. 15 Ya taɓa hannunta, sai zazzaɓin ya bar ta, kuma ta tashi ta soma yi masa hidima. 16 Amma da yamma ta yi, sai mutane suka kawo masa masu aljanu da yawa. Ya fitar da aljanun ta wurin yin magana kawai, kuma ya warkar da dukan waɗanda suke fama da cututtuka, 17 ya yi wannan don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa: “Shi da kansa ya ɗauke cututtukanmu kuma ya kawar da rashin lafiyarmu.”
18 Saꞌad da Yesu ya ga taron jamaꞌa kewaye da shi, sai ya gaya wa almajiransa su ƙetare zuwa ɗayan gefen teku. 19 Sai wani marubuci ya zo ya same shi ya ce masa: “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.” 20 Amma Yesu ya ce masa: “Karnukan daji suna da ramukansu, tsuntsaye kuma suna da wurin kwana, amma Ɗan mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.” 21 Sai wani daga cikin almajiransa ya ce masa: “Ubangiji, bari in je in binne babana tukuna.” 22 Sai Yesu ya ce masa: “Ka ci-gaba da bi na, ka bar matattu su binne matattunsu.”
23 Da Yesu ya shiga jirgin ruwa, sai almajiransa suka bi shi. 24 Sai babban hadari mai iska ya taso a tekun, har ruwan yana tashi yana shiga cikin jirgin; amma Yesu yana nan yana barci. 25 Sai suka zo suka tashe shi suka ce masa: “Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!” 26 Amma ya ce musu: “Me ya sa kuke jin tsoro haka, ku masu ƙaramar bangaskiya?” Sai ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma tekun, sai koꞌina ya yi shuru tsit. 27 Sai mutanen suka yi mamaki, suka ce: “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da teku ma suna yi masa biyayya.”
28 Da Yesu ya ƙetare zuwa ɗayan gefen tekun a yankin mutanen Gadara, sai wasu mutane biyu masu aljanu suka fito daga wurin da ake binne mutane* kuma suka same shi. Su mugaye ne kuma suna da ban tsoro sosai, har ma kowa yana jin tsoron bin hanyar. 29 Sai suka yi ihu suna cewa: “Ina ruwanka da mu Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka hukunta mu kafin lokacin da aka tsara?” 30 Can gaba kaɗan, akwai garken aladu da suke cin abinci. 31 Sai aljanun suka soma roƙon sa suna cewa: “Idan ka kore mu, ka tura mu cikin garken aladun nan.” 32 Sai Yesu ya ce musu: “Ku tafi!” Da jin hakan, sai suka fito suka shiga jikin aladun. Sai garken aladun gabaki-ɗaya suka gangara suka faɗi cikin teku kuma suka mutu a cikin ruwan. 33 Amma masu kiwon aladun suka gudu. Da suka shiga cikin birni, sun ba da labarin duk abin da ya faru, har da labarin masu aljanun. 34 Sai dukan mutanen birnin suka fito su sami Yesu. Da suka gan shi, sai suka roƙe shi ya bar yankinsu.