Ta Hannun Markus
4 Yesu ya kuma soma koyarwa a bakin teku, jamaꞌa da yawa suka taru kusa da shi. Sai ya shiga cikin jirgin ruwa ya zauna, kuma aka ɗan matsar da jirgin cikin teku, amma dukan jamaꞌar kuwa suna bakin tekun. 2 Sai ya soma koya musu abubuwa da yawa ta wurin misalai. Yayin da yake koyarwar ya ce musu: 3 “Ku saurara. Ga shi! Wani mutum ya fita don ya je ya yi shuki. 4 Yayin da yake shukin, wasu iri sun faɗi a kan hanya, kuma tsuntsaye sun zo sun cinye su. 5 Waɗansu kuma suka faɗi a wuri mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, kuma suka tsira da sauri saboda ƙasar ba zurfi. 6 Amma da rana ta fito, sai ta ƙone su, kuma suka bushe domin ba su da jijiya. 7 Wasu irin sun faɗi a cikin ƙayoyi, ƙayoyin suka yi girma suka kashe su, kuma ba su ba da amfani ba. 8 Wasu kuma suka faɗi a ƙasa mai kyau, da suka tsiro kuma suka yi girma, sai suka soma ba da amfani, kuma suna ba da amfani sau talatin, da sau sittin, da kuma sau ɗari.” 9 Sai Yesu ya ƙara cewa: “Bari mai kunne ya kasa kunne ya ji.”
10 Saꞌad da yake shi kaɗai, almajiransa goma sha biyun da kuma waɗanda suke bin sa suka soma yi masa tambaya game da misalan. 11 Ya ce musu: “An yarda muku ku gane asiri mai tsarki na Mulkin Allah, amma sauran mutanen nakan koya musu abubuwa ta wurin misalai. 12 Domin ko da suna dubawa, ba za su iya gani ba. Ko da suna ji, ba za su iya fahimtar abin da ake nufi ba; kuma ba za su taɓa juyo* don a gafarta musu ba.” 13 Ƙari ga haka, ya ce musu: “Ba ku gane maꞌanar wannan misalin ba. To, ta yaya za ku gane sauran misalan?
14 “Kalmar Allah ce mai shukin ya shuka. 15 Irin da suka faɗi a kan hanya su ne misalin mutanen da suka ji kalmar, amma nan da nan, Shaiɗan ya zo ya ɗauke kalmar da aka shuka a cikin zuciyarsu. 16 Haka ma, irin da suka faɗi a wurin da akwai duwatsu, su ne misalin waɗanda suka ji kalmar kuma nan da nan suka karɓe ta da farin ciki. 17 Amma da yake kalmar ba ta yi jijiya a cikin zuciyarsu ba, ba su daɗe ba. Da zarar suka fuskanci tsanantawa ko azaba saboda kalmar, sai suka yi tuntuɓe. 18 Akwai kuma irin da suka faɗi a cikin ƙayoyi. Su ne misalin waɗanda suka ji kalmar, 19 amma yawan damuwa na wannan zamanin,* da yadda son arziki yake ruɗin mutane, da kuma son samun kome da kome, sun shiga zuciyarsu suka kashe kalmar, kuma ba ta ba da amfani ba. 20 A ƙarshe, irin da suka faɗi a ƙasa mai kyau, su ne misalin waɗanda suka ji kalmar, suka karɓe ta hannu bibbiyu, kuma suka ba da amfani, sau talatin, da sau sittin, da kuma sau ɗari.”
21 Ya kuma ce musu: “Ba a kunna fitila don a rufe ta* ko kuma a saka ta a ƙarƙashin gado, ko ba haka ba? Amma ba ana saka fitila a kan sandar riƙe fitila ba? 22 Domin babu abin da aka ɓoye da ba za a fallasa ba; kuma babu asirin da aka ɓoye da kyau da ba za a sani ba. 23 Duk mai kunne bari ya kasa kunne ya ji.”
24 Ƙari ga haka, ya ce musu: “Ku mai da hankali ga abin da kuke ji. Da mudun da kuke auna wa mutane, da shi za a auna muku. Hakika, har ma za a ƙara muku. 25 Domin duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma duk wanda bai da abu, za a ɗauke har ɗan abin da yake da shi.”
26 Sai ya ce musu: “Mulkin Allah yana kama da mutumin da ya shuka iri a ƙasa. 27 A-kwana-a-tashi, irin ya tsira ya yi girma, mutumin bai ma san yadda hakan ya faru ba. 28 Ƙasa tana ba da amfani da kanta. Da farko takan fitar da kara, saꞌan nan kai, sai kuma kan ya fitar da ƙwaya. 29 Amma da zarar amfanin ya nuna, sai ya sa lauje ya yanka, domin lokacin girbi ya yi.”
30 Yesu ya ci-gaba da cewa: “Da mene ne za mu iya kwatanta Mulkin Allah? Ko kuma da wane misali ne za mu iya bayyana shi? 31 Yana kama da ƙwayar mastad,* wadda a lokacin da aka shuka ta, ta fi ƙanƙanta a duniya. 32 Amma bayan an shuka ta, takan yi girma, ta fi sauran abubuwan da aka shuka kuma ta yi manyan rassa, har ma tsuntsayen sama sukan samu wurin zama a inuwarta.”
33 Da irin waɗannan misalai da yawa, Yesu ya koya musu kalmar Allah daidai yadda za su iya ganewa. 34 Hakika, ba ya gaya musu kome sai tare da misali, amma saꞌad da yake tare da almajiransa su kaɗai, yakan bayyana musu kome.
35 A ranar, saꞌad da yamma ta riga ta yi, sai ya ce musu: “Mu ƙetare zuwa ɗayan gefen tekun.” 36 Bayan da sun sallami jamaꞌar, sai suka tafi da shi a cikin jirgin,* kuma akwai wasu jirage da suka bi shi. 37 Sai aka soma iska mai ƙarfi, kuma hadari ya haɗu, har iskar tana ta da ruwan tekun sama, yana buga jirgin. Hakan ya sa jirgin ya kusan nitsewa. 38 Amma Yesu yana bayan jirgin, yana barci a kan filo.* Sai suka tashe shi kuma suka ce masa: “Malam, ba ka damu cewa za mu hallaka ba?” 39 Sai ya tashi ya tsawata wa iskar kuma ya ce wa tekun: “Natsu! Ka yi shuru!” Sai iskar ta tsaya kuma koꞌina ya yi shuru tsit. 40 Sai ya ce musu: “Me ya sa kuke jin tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya?” 41 Amma sai suka ji tsoro sosai, kuma suka ce wa juna: “Wane ne wannan? Har iska da teku ma suna yi masa biyayya.”