Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
6 Yayin da kuke aiki tare da Allah, muna roƙon ku kada ku karɓi alherinsa a banza.* 2 Gama ya ce: “A lokacin alheri, na saurare ka, kuma a lokacin ceto, na taimaka maka.” Ga shi! Yanzu ne Allah ya fi nuna mana alheri. Ga shi! Yanzu ne ranar ceto.
3 Ba ma yin wani abu da zai sa wani tuntuɓe, don kada a sami wani laifi a hidimar da muke yi; 4 amma a kowace hanya, muna nuna mu masu hidimar Allah ne, ta wurin jimre abubuwa da yawa, ta wurin ƙunci, ta wurin rashin abin biyan bukata, ta wurin matsaloli, 5 ta wurin dūka, ta wurin kurkuku, ta wurin tashin hankali, ta wurin aiki da ƙwazo, ta wurin rashin barci da rashin abinci; 6 ta wurin rayuwa mai tsabta, ta wurin ilimi, ta wurin haƙuri, ta wurin alheri, ta wurin ruhu mai tsarki, ta wurin ƙauna marar munafunci, 7 ta wurin maganar gaskiya, ta wurin ikon Allah, ta wurin riƙe makaman adalci a hannun dama* da hannun hagu,* 8 ta wurin ɗaukaka da rashin ɗaukaka, ta wurin labari marar kyau da labari mai kyau. Ko da yake mu masu gaskiya ne, ana ɗaukan mu kamar masu yaudara, 9 duk da cewa an san mu, an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, an ɗauke mu kamar waɗanda suke mutuwa, duk da haka, muna a raye, an ɗauke mu kamar mutanen da aka yi musu horo, duk da haka, ba a miƙa mu don a kashe mu ba, 10 an ɗauke mu kamar masu baƙin ciki, amma muna farin ciki kullum, an ɗauke mu kamar talakawa, amma muna mai da mutane da yawa masu arziki, an ɗauke mu kamar ba mu da wani abu, duk da haka, kome namu ne.
11 Ya ku Korintiyawa, ba mu ɓoye muku kome ba,* kuma mun nuna muna ƙaunar ku sosai. 12 Mun nuna muku ƙauna da dukan zuciyarmu, amma ku ba ku ƙaunace mu da dukan zuciyarku ba. 13 Don haka ina ce muku a matsayin yarana, ku buɗe zukatanku sosai a gare mu.
14 Kada ku haɗa kai da marasa bi.* Don wace dangantaka ce ke tsakanin adalci da rashin adalci? Ko kuma, wace alaƙa ce ke tsakanin duhu da haske? 15 Ƙari ga haka, wane haɗin kai ne yake tsakanin Kristi da Beliyal?* Ko kuma me ya haɗa mai bi da marar bi? 16 Kuma wace yarjejeniya ce ke tsakanin haikalin Allah da gumaka? Gama, mu haikalin Allah mai rai ne; kamar yadda Allah ya ce: “Zan zauna tare da su, in yi tafiya a cikinsu, zan zama Allahnsu, kuma za su zama mutanena.” 17 “‘Don haka, ku fita daga cikinsu, ku rabu da su,’ in ji Jehobah,* ‘kuma ku daina taɓa abu marar tsarki’”; “‘ni kuwa zan karɓe ku.’” 18 “‘Kuma zan zama uba a gare ku, ku kuma za ku zama ꞌyaꞌya maza da mata a gare ni,’ in ji Jehobah,* Maɗaukaki.”