Ta Hannun Luka
7 Saꞌad da ya gama gaya wa mutanen abin da yake so ya gaya musu, sai ya shiga Kafarnahum. 2 Bawan wani jamiꞌin soja da yake ƙauna sosai yana rashin lafiya mai tsanani kuma yana bakin mutuwa. 3 Da ya ji game da Yesu, sai ya tura wasu dattawan Yahudawa su je wajen Yesu su roƙe shi ya zo ya warkar da bawansa da yake rashin lafiya. 4 Sun je wajen Yesu, suka soma roƙon sa sosai suna cewa: “Mutumin ya cancanci ka taimaka masa, 5 yana ƙaunar alꞌummarmu, kuma shi da kansa ne ya gina majamiꞌarmu.” 6 Sai Yesu ya tafi tare da su. Amma saꞌad da ya yi kusa da gidan, jamiꞌin sojan ya tura abokansa su gaya masa cewa: “Mai Girma, kada ka damu, don ban cancanci ka shiga gidana ba. 7 Shi ya sa ban ga na cancanci in zo wurinka da kaina ba. Amma ka yi magana, kuma bawana zai warke. 8 Domin ni ma mutum ne mai iko, ina da sojoji a ƙarƙashina, nakan ce ma wannan, ‘Je ka!’ sai ya je, wani kuma in ce masa, ‘Zo!’ sai ya zo, bawana kuma nakan ce masa, ‘Yi abu kaza!’ sai ya yi.” 9 Da Yesu ya ji abubuwan da mutumin nan ya faɗa, ya yi mamaki, sai ya juya ya ce wa jamaꞌar da suke bin sa: “Ina gaya muku, ban taɓa ganin mutum ko a Israꞌila da yake da bangaskiya sosai kamar wannan ba.” 10 Saꞌad da waɗanda jamiꞌin sojan ya aika suka koma gida, sai suka ga cewa bawan ya warke.
11 Jim kaɗan bayan hakan, sai Yesu ya yi tafiya zuwa garin Nayin, almajiransa da jamaꞌa da yawa suna tafiya tare da shi. 12 Saꞌad da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wasu mutane suna ɗauke da gawar wani mutum, shi kaɗai ne mamarsa ta haifa. Ban da haka ma, mijinta ya rasu. Kuma mutane da yawa daga garin suna tafiya tare da ita. 13 Saꞌad da Ubangiji ya ga matar, sai ya tausaya mata, kuma ya ce mata: “Ki daina kuka.” 14 Sai Yesu ya zo kusa, ya taɓa abin da* aka ɗauki gawar mutumin da shi, kuma waɗanda suka ɗauki gawar suka tsaya. Sai ya ce: “Saurayi, ina ce maka, ka tashi!” 15 Sai mutumin da ya mutu ya tashi, ya soma magana kuma Yesu ya miƙa shi ga mamarsa. 16 Sai tsoro ya kama dukansu, kuma suka soma ɗaukaka Allah, suna cewa: “An ta da wani babban annabi a tsakaninmu,” kuma “Allah ya tuna da mutanensa.” 17 Kuma wannan labari game da shi ya yaɗu a dukan Yahudiya, da kuma dukan yankunan da ke kewaye da ita.
18 Almajiran Yohanna kuwa sun gaya wa Yohanna dukan abubuwan nan. 19 Sai Yohanna ya kira biyu cikin almajiransa kuma ya aike su zuwa wurin Ubangiji, su tambaye shi cewa: “Kai ne Wanda Zai Zo, ko kuma mu jira wani dabam?” 20 Saꞌad da suka zo wurin Yesu, mutanen sun ce: “Yohanna Mai Baftisma ya aiko mu wajenka mu tambaye ka, ‘Kai ne Wanda Zai Zo, ko kuma mu jira wani dabam?’” 21 A daidai lokacin, Yesu ya warkar da masu rashin lafiya da yawa, da masu fama da cututtuka masu tsanani, da masu aljanu, kuma ya sa makafi da yawa su soma gani. 22 Sai ya amsa wa almajiran Yohanna ya ce musu: “Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka gani da kuma abin da kuka ji: Yanzu makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da kutare, kurame suna ji, ana ta da waɗanda suka mutu, ana kuma gaya wa talakawa labari mai daɗi. 23 Mai farin ciki ne wanda bai ga wani dalilin yin tuntuɓe* saboda ni ba.”
24 Bayan waɗanda Yohanna ya aiko suka tafi, sai Yesu ya soma yi wa jamaꞌar magana game da Yohanna cewa: “Mene ne kuka fito ku gani a daji? Kun fito ganin dogayen ciyayi da iska take kaɗawa ne? 25 To, mene ne kuka fito ku gani? Mutumin da ke sanye da riguna masu kyau ne? Ai, ꞌyan gidan sarakuna ne suke saka riguna masu kyau da kuma zaman jin daɗi. 26 To, wai mene ne ainihi kuka fito ku gani? Don ku ga annabi ne? E, ina gaya muku, shi annabi ne, har ma ya fi annabi sosai. 27 Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa: ‘Ga shi! Ina aika manzona ya riga ka, wanda zai shirya maka hanya kafin ka zo.’ 28 A gaskiya, a cikin dukan ꞌyanꞌadam, babu wanda ya fi Yohanna daraja, amma mai matsayi mafi ƙanƙanta a Mulkin Allah ya fi shi daraja.” 29 (Saꞌad da dukan mutanen da masu karɓan haraji suka ji wannan, sai suka ce Allah mai adalci ne, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma. 30 Amma Farisiyawa da waɗanda suka san Doka,* sun yi watsi da umurnin da Allah ya ba su, tun da ba su yarda Yohanna ya yi musu baftisma ba.)
31 “Saboda haka, da wane ne zan kwatanta mutanen wannan zamanin, kuma da wa suka yi kama? 32 Suna kama da yara da suke kasuwa suna magana da juna, suna cewa: ‘Mun busa muku sarewa amma kun ƙi ku yi rawa; mun yi kuka sosai, amma ba ku yi kuka ba.’ 33 Haka nan ma, Yohanna Mai Baftisma ya zo, bai ci burodi ba, bai sha ruwan inabi ba, amma kuka ce: ‘Yana da aljani.’ 34 Ɗan mutum ya zo yana ci yana sha, amma kun ce: ‘Ga mai yawan ci da sha, abokin masu karɓan haraji da masu zunubi!’ 35 Duk da haka dai, ana gane mai hikima ta wurin dukan ayyuka masu kyau da yake yi.”*
36 Wani Bafarisi ya yi ta roƙon sa ya zo su ci abinci tare. Sai Yesu ya shiga gidan Bafarisin kuma ya zauna yana cin abinci a kan teburi. 37 Sai wata mata da aka sani a matsayin mai zunubi a garin, ta ji cewa Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisin, kuma ta zo da kwalba* da ke ɗauke da mān ƙamshi. 38 Ta zo ta tsaya a bayansa wajen ƙafafunsa, tana kuka. Da hawayenta ya fara zuba a ƙafafunsa, sai ta goge ƙafafunsa da gashin kanta. Ƙari ga haka, ta yi wa ƙafafunsa sumba kuma ta shafa musu mān ƙamshin. 39 Da Bafarisin da ya gayyace shi ya ga hakan, sai ya ce wa kansa: “Da a ce mutumin nan annabi ne da gaske, da ya san irin matar da take ta taɓa shi, cewa ita mai zunubi ce.” 40 Amma Yesu ya amsa ya ce: “Siman, akwai abin da nake so in gaya maka.” Sai ya ce: “Malam, ina jin ka!”
41 “Akwai wani mutum da ke bin mutane biyu bashi; yana bin ɗaya bashin dinari* ɗari biyar, ɗaya kuma bashin dinari hamsin. 42 Da suka kasa biyan mutumin kuɗinsa, sai ya yafe wa dukansu. To, a ganinka, wane ne a cikinsu zai fi ƙaunar mutumin?” 43 Sai Siman ya amsa ya ce: “A ganina, wanda aka yafe masa kuɗi mai yawa ne.” Yesu ya ce masa: “Ka amsa daidai.” 44 Sai Yesu ya juya ya kalli matar, kuma ya ce wa Siman: “Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa in wanke ƙafafuna ba. Ka ga matar nan, ta jiƙe ƙafafuna da hawayenta, kuma ta goge su da gashin kanta. 45 Ba ka yi mini sumba ba, amma ka ga matar nan, tun daga lokacin da na shigo, ba ta daina yi wa ƙafafuna sumba ba. 46 Ba ka zuba māi a kaina ba, amma wannan matar ta zuba mān ƙamshi a ƙafafuna. 47 Saboda haka, ina gaya maka, ko da yake zunubanta masu yawa ne, an gafarta mata, don ta nuna ƙauna sosai. Amma wanda aka gafarta masa abu kaɗan, ƙauna kaɗan yake nunawa.” 48 Sai ya ce mata: “An gafarta zunubanki.” 49 Sai waɗanda suke cin abinci tare da shi a teburi, suka soma gaya wa juna: “Wane ne wannan da har yana gafarta zunubai?” 50 Sai Yesu ya ce wa matar: “Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya.”