Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
3 Mun soma yabon kanmu kuma ne? Ko kuma kamar wasu mutane, muna bukatar wasiƙun yabo zuwa gare ku, ko daga wurin ku ne? 2 Ku da kanku ne wasiƙarmu, wadda aka rubuta a kan zukatanmu, wadda dukan mutane suka sani kuma suke karantawa. 3 Kun nuna cewa ku wasiƙar Kristi ne da muka rubuta a matsayinmu na masu hidima, ba a rubuta shi da abin rubutu* ba, amma an rubuta ne da ruhun Allah mai rai, ba a kan allunan dutse ba, amma a kan allunan jiki, a kan zukata.
4 Muna da irin wannan tabbacin a gaban Allah ta wurin Kristi. 5 Ba wai muna ɗaukan kanmu a matsayin waɗanda suka cancanci su yi wani abu ba ne, amma Allah ne yake sa mu cancanta. 6 A gaskiya, Allah ne ya sa muka cancanci mu zama masu hidimar sabuwar yarjejeniya, ba na Doka* da aka rubuta ba, amma na ruhu. Gama Dokar tana sa a yanke wa mutum hukuncin kisa, amma ruhun yana sa mutum ya rayu.
7 Idan Dokar da ke kai ga mutuwa, wadda aka rubuta da harufa a kan duwatsu, an ba da ita da irin wannan ɗaukakar, har ꞌyaꞌyan Israꞌila suka kasa kallon fuskar Musa domin ɗaukakar da ke fuskarsa, ko da yake za a kawar da ɗaukakar, 8 me ya sa aikin da ruhun zai yi ba zai kasance da ɗaukaka fiye da hakan ba? 9 Idan Dokar da ke kai ga mutuwa tana da ɗaukaka, to aikin da ke sa mutane su zama masu adalci zai fi ɗaukaka! 10 Gaskiyar ita ce, abin da yake da ɗaukaka a dā, bai da ɗaukaka yanzu saboda ɗaukakar da ta fi shi. 11 Idan abin da ke shuɗewa ya zo da ɗaukaka, babu shakka abin da zai dawwama zai fi shi ɗaukaka!
12 Tun da yake muna da irin wannan bege, muna da ꞌyanci sosai na yin magana,* 13 mu ba kamar Musa ba ne wanda yake rufe fuskarsa da mayafi domin kada Israꞌilawa su ga ƙarshen ɗaukakar nan mai shuɗewa. 14 Amma sun kasa fahimta. Gama har wa yau, mayafin yana rufe fuskarsu yayin da ake karanta tsohuwar yarjejeniyar, domin ta wurin Kristi ne kawai za a iya cire mayafin. 15 Gaskiyar ita ce, har zuwa yau, a duk lokacin da ake karanta abubuwan da Musa ya rubuta, akwai mayafi da ke rufe zukatansu. 16 Amma idan mutum ya juyo ga Jehobah* za a cire mayafin. 17 Jehobah* ne Ruhun, a inda ruhun Jehobah* yake kuwa, akwai ꞌyanci. 18 Kuma dukanmu da ba a rufe fuskokinmu ba, muna nuna hasken ɗaukakar Jehobah* kamar madubi, ana canja mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai ƙaruwa,* daidai yadda Jehobah* wanda shi Ruhu ne yake so mu kasance.