Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
16 Yanzu game da gudummawa domin tsarkaka, za ku iya bin umurnan da na ba wa ikilisiyoyin Galatiya. 2 A ranar farko ta kowane mako, ya kamata kowannenku ya keɓe wani abu gwargwadon ƙarfinsa, ba sai na iso kafin ku tara gudummawar ba. 3 Saꞌad da na isa, zan aika mazan da kuka zaɓa a cikin wasiƙunku su kai gudummawarku zuwa Urushalima. 4 Amma idan na ga cewa ya dace ni ma in je wurin, zan tafi tare da su.
5 Zan zo wurinku bayan na zagaya Makidoniya, domin zan bi ta Makidoniya; 6 wataƙila zan zauna da ku, ko ma in kasance da ku a lokacin sanyi domin ku ɗan raka ni zuwa inda zan je. 7 Gama ba na so in gan ku yayin da nake wucewa kawai, tun da ina sa ran kasancewa tare da ku na ɗan lokaci idan Jehobah* ya yarda. 8 Amma zan ci-gaba da zama a Afisa har Bikin Fentikos, 9 domin an buɗe mini wata ƙofa mai faɗi da za ta kai ga yin ayyuka, amma akwai masu hamayya da yawa.
10 Idan Timoti ya isa, ku tabbata cewa babu abin da zai tsorata shi yayin da yake tsakaninku, domin yana yin aikin Jehobah* kamar yadda nake yi. 11 Don haka, kada wani ya rena shi. Ku sallame shi cikin salama domin ya iya zuwa wurina, gama ina jiran shi tare da ꞌyanꞌuwa.
12 Yanzu game da ɗanꞌuwanmu Afollos, na roƙe shi sosai ya zo wurinku tare da ꞌyanꞌuwa. Bai so ya zo yanzu ba, amma zai zo idan ya samu zarafi.
13 Ku zauna da shiri,* ku tsaya daram cikin bangaskiya, ku ci-gaba da kasancewa da ƙarfin zuciya, ku yi ƙarfi. 14 Bari duk abin da za ku yi, ku yi shi cikin ƙauna.
15 Yanzu, ina roƙon ku ꞌyanꞌuwa: Kun sani cewa iyalin Stifanas ne na farko da suka ba da gaskiya a Akaya kuma sun ba da kansu don su yi wa tsarkaka hidima. 16 Ku ci-gaba da miƙa kanku ga mutane kamar haka, da kuma dukan waɗanda suke aiki da haɗin kai da kuma ƙwazo. 17 Na ji daɗin cewa Stifanas da Fortunatus da Akaikus suna tare da ni, domin suna taimaka mini yadda za ku yi da a ce kuna nan. 18 Gama sun ƙarfafa ni da ku. Saboda haka, ku girmama irin waɗannan mutanen.
19 Ikilisiyoyin da ke Asiya suna aika muku gaisuwarsu. Akila da Biriskila tare da ikilisiyar da ke gidansu suna gaishe ku da dukan zuciyarsu cikin Ubangiji. 20 Dukan ꞌyanꞌuwa suna gaishe ku. Ku gaishe da juna da sumba mai tsarki.
21 Ni Bulus nake rubuta muku wannan gaisuwar da hannuna, kuma ina gaishe ku.
22 Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, bari ya zama laꞌananne. Ya Ubangijinmu, ka zo! 23 Bari alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da ku. 24 Bari ƙaunata ta kasance da dukanku cikin haɗin kai da Kristi Yesu.