Ta Hannun Markus
15 Nan da nan da gari ya waye, sai manyan firistoci, da dattawa, da marubuta, har ma da dukan Sanhedrin* suka yi shawara tare, sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi kuma suka ba da shi ga Bilatus. 2 Sai Bilatus ya tambaye shi cewa: “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Sai Yesu ya amsa ya ce: “Kai ma da kanka ka faɗi hakan.” 3 Amma manyan firistoci sun zarge shi da aikata laifuffuka da yawa. 4 Sai Bilatus ya soma yi masa tambaya kuma ya ce: “Ba za ka ce kome ba? Ga shi ana zarginka a kan abubuwa da yawa.” 5 Amma Yesu bai ƙara amsawa ba, hakan ya ba wa Bilatus mamaki sosai.
6 A kowane lokacin biki, Bilatus ya saba sake wa jamaꞌar duk fursuna da suke so. 7 A lokacin akwai wani mutum mai suna Barabbas da ake tsare da shi, tare da ꞌyan tawaye a kurkuku, kuma a tawayen da suka yi, sun yi kisa. 8 Sai jamaꞌar suka zo suka soma miƙa roƙonsu ga Bilatus bisa ga abin da ya saba yi musu. 9 Sai ya amsa ya ce musu: “Kuna so in sake muku Sarkin Yahudawa?” 10 Don Bilatus ya san cewa kishi ne ya sa manyan firistocin suka ba da shi. 11 Amma manyan firistocin sun zuga jamaꞌa su ce a sako musu Barabbas a maimakon Yesu. 12 Bilatus ya sake cewa: “Mene ne kuke so in yi da wanda kuka kira Sarkin Yahudawa?” 13 Sai suka sake ta da murya suka ce: “A rataye shi a kan gungume!”* 14 Amma Bilatus ya ci-gaba da cewa: “Me ya sa? Wane laifi ne ya yi?” Har ila suka ci-gaba da ihu, suna cewa: “A rataye shi a kan gungume!”* 15 Da yake Bilatus yana so ya faranta wa jamaꞌar rai, sai ya sake musu Barabbas. Bayan ya sa aka yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a kashe shi a kan gungume.
16 Sai sojojin suka tafi da Yesu zuwa cikin farfajiya, wato a cikin gidan gwamnan, sai suka tara dukan sojoji. 17 Sai suka saka masa jan mayafi, suka yi wani rawanin ƙaya suka saka masa a kai. 18 Sai suka soma ce masa: “Ranka ya daɗe,* Sarkin Yahudawa!” 19 Ƙari ga haka, sun ɗauki sanda suna buga masa a kai, suna tofa masa miyau, kuma suka sa gwiwoyinsu a ƙasa suka durƙusa a gabansa. 20 A ƙarshe, bayan sun gama yi masa baꞌa, sai suka tuɓe masa jan mayafin, kuma suka saka masa kayansa. Sai suka tafi da shi don su rataye shi a kan gungume. 21 Ƙari ga haka, sun tilasta ma wani mutumin Sayirin da yake wucewa, mai suna Siman, ya ɗauki gungumen azabar* Yesu. Mutumin baban Alekzanda da Rufus ne, kuma yana dawowa ne daga ƙauye.
22 Sai suka kawo shi wani wurin da ake kira Golgota, wanda idan aka fassara yana nufin, “Wurin Ƙoƙon Kai.” 23 A wurin, sun yi ƙoƙari su ba shi ruwan inabi da aka garwaye da mur,* amma ya ƙi ya sha. 24 Sai suka rataye shi a kan gungume kuma suka raba mayafinsa ta wajen jefa ƙuriꞌa a kansu domin su san abin da kowa zai samu. 25 Wajen ƙarfe tara na safe* ne suka rataye shi a kan gungumen. 26 An kuma rubuta laifin da aka ce ya yi, cewa: “Sarkin Yahudawa.” 27 Ƙari ga haka, an rataye ɓarayi biyu tare da shi, ɗaya a hannun hagunsa, ɗaya kuma a hannun damansa. 28* —— 29 Mutanen da suke wucewa suna ta zagin sa, suna kaɗa kansu kuma suna cewa: “Kai da ka ce za ka rushe haikali kuma ka gina shi cikin kwana uku, 30 ka ceci kanka mana, ta wajen saukowa daga kan gungumen azabar.”* 31 Haka nan ma, manyan firistoci da marubuta suna ta yi masa baꞌa a tsakaninsu, suna cewa: “Ya ceci wasu, amma ya kasa ceton kansa! 32 Bari Kristi, Sarkin Israꞌila ya sauko daga kan gungumen azabar* yanzu don mu yarda da shi.” Har ɓarayin da aka rataye su tare da shi ma, suna yi masa baƙar magana.
33 Da wajen ƙarfe sha biyu na rana* ya yi, sai duhu ya rufe koꞌina a ƙasar har zuwa wajen ƙarfe uku na yamma.* 34 A wajen ƙarfe uku na yamma, Yesu ya yi magana da babbar murya, yana cewa: “Eli, Eli, lama sabaktani?” wanda idan aka fassara yana nufin: “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” 35 Saꞌad da wasu daga cikin mutanen da suke tsaye kusa da wajen suka ji hakan, sai suka ce: “Duba! Yana kiran Iliya.” 36 Sai wani ya yi gudu ya je ya ɗauki soso ya jiƙa shi a cikin ruwan inabi da ya yi tsami, ya soka shi a sanda, ya miƙa masa ya sha, yana cewa: “Ku bar shi! Bari mu ga ko Iliya zai zo ya saukar da shi.” 37 Yesu ya yi ihu da babbar murya, sai ya mutu.* 38 Sai labulen da ke haikali ya rabu kashi biyu, daga sama zuwa ƙasa. 39 Saꞌad da jamiꞌin sojan da ke tsaye a gaban Yesu ya ga abubuwan da suka faru a lokacin da Yesu ya mutu, sai ya ce: “Ba shakka, mutumin nan Ɗan Allah ne.”
40 Akwai kuma mata da suke tsaye suna kallo daga nesa, a cikinsu akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu mamar Yaƙub Ƙarami da Joses, da kuma Salomi, 41 su ne waɗanda suke bin Yesu, suke yi masa hidima saꞌad da yake Galili. Akwai kuma wasu mata da yawa da suka zo Urushalima da shi.
42 Da yamma ta yi kusa, kuma da yake Ranar Shiri* ne, wato rana ta ƙarshe kafin Ranar Assabaci, 43 sai wani mutum mai suna Yusufu daga Arimatiya ya zo, shi ɗan Majalisa* ne da ake mutuntawa. Shi ma da kansa yana jiran Mulkin Allah. Da ƙarfin zuciya ya je wurin Bilatus kuma ya roƙa a ba shi gawar Yesu. 44 Amma Bilatus ya so ya sani ko Yesu ya riga ya mutu, sai ya kira jamiꞌin sojan, ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu. 45 Bayan ya ji daga jamiꞌin sojan cewa Yesu ya riga ya mutu, Sai ya ba wa Yusufu gawar Yesu. 46 Bayan ya saya yadin lilin mai kyau, sai ya saukar da gawar Yesu, ya naɗe shi da yadin, sai ya kwantar da gawar Yesu a kabarin da aka tona a cikin dutse; kuma ya tura dutse ya rufe bakin kabarin. 47 Amma Maryamu Magdalin, da Maryamu mamar Joses sun ci-gaba da kallon wurin da aka kwantar da Yesu.