Ta Hannun Luka
8 Jim kaɗan bayan haka, Yesu ya bi gari zuwa gari da ƙauyuka, yana waꞌazi da shelar labari mai daɗi na Mulkin Allah kuma almajiransa goma sha biyu suna tare da shi, 2 da kuma wasu mata da aka fitar da mugayen ruhohi daga jikinsu kuma aka warkar da su daga rashin lafiya. A cikinsu akwai: Maryamu wadda ake kira Magdalin, wadda aljanu bakwai suka fita daga jikinta. 3 Da Jowanna matar Kuza, shugaban gidan Hirudus,* da Suzana, da waɗansu mata da yawa da suke yi musu hidima daga cikin kayansu.
4 Saꞌad da jamaꞌa suka taru tare da waɗanda suka zo wurinsa daga wasu garuruwa, sai ya yi musu magana ta wurin misali cewa: 5 “Wani mutum ya fita don ya je ya yi shuki. Yayin da yake shukin, wasu irin sun faɗi a kan hanya, aka tattaka su, kuma tsuntsayen sama sun cinye su. 6 Wasu kuma sun faɗi a kan dutse, bayan da sun tsiro, sai suka bushe domin babu ruwa a wurin. 7 Wasu kuma sun faɗi a cikin ƙayoyi, da ƙayoyin suka yi girma, sai suka kashe su. 8 Amma wasu sun faɗi a ƙasa mai kyau, da suka tsira, sai suka ba da amfani sau ɗari.” Bayan ya faɗa abubuwan nan, sai ya ce: “Bari mai kunne ya kasa kunne ya ji.”
9 Amma almajiransa suka tambaye shi abin da misalin yake nufi. 10 Sai ya ce musu: “Ku dai an yarda muku ku gane asirai masu tsarki na Mulkin Allah, amma ga sauran mutanen, nakan koya musu abubuwa ta wurin misalai. Domin ko da suna dubawa, ba za su ga wani abu ba. Kuma ko da suna ji, ba za su iya fahimtar abin da ake nufi ba. 11 Yanzu ga maꞌanar misalin: Irin shi ne kalmar Allah. 12 Waɗanda suka faɗi a kan hanya, su ne misalin mutanen da suka ji kalmar, kuma Ibilis ya zo ya ɗauke kalmar daga zuciyarsu domin kada su ba da gaskiya kuma su sami ceto. 13 Waɗanda suka faɗi a kan dutse, su ne misalin mutanen da suka ji kalmar, kuma suka karɓe ta da farin ciki, amma ba su yi jijiya ba, kuma da suka fuskanci jarraba, sai suka faɗi. 14 Waɗanda suka faɗi a cikin ƙayoyi kuma, su ne misalin mutanen da suka ji kalmar, amma yawan damuwa, da arziki, da jin daɗi na wannan rayuwa sun ɗauke hankalinsu, kuma suka kashe su gabaki-ɗaya har sun kasa ba da amfani. 15 Waɗanda suka faɗi a ƙasa mai kyau, su ne misalin mutanen da suka ji kalmar Allah, kuma suka karɓe ta da dukan zuciyarsu, suka riƙe ta, kuma suka jimre suka ba da ꞌyaꞌya.
16 “Babu wanda zai kunna fitila sai ya rufe ta da kwano ko kuma ya saka ta a ƙarƙashin gado, amma yakan ajiye ta ne a kan sandar riƙe fitila, domin waɗanda suka shigo su ga hasken. 17 Babu abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana ba, ko kuma asiri da aka ɓoye da kyau da ba zai taɓa fitowa fili kuma a sani ba. 18 Saboda haka, ku mai da hankali ga yadda kuke ji, domin duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma wanda ba shi da abu, za a ƙwace har abin da yake tsammanin yana da shi.”
19 Sai mamar Yesu da ꞌyanꞌuwansa suka zo wurinsa, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda yawan jamaꞌa. 20 Sai aka gaya masa cewa: “Mamarka da ꞌyanꞌuwanka suna tsaye a waje kuma suna so su gan ka.” 21 Sai ya ce musu: “Waɗanda suka ji kalmar Allah, kuma suka aikata ta, su ne mamata da kuma ꞌyanꞌuwana.”
22 Wata rana Yesu da almajiransa sun shiga cikin jirgin ruwa, sai ya ce musu: “Mu ƙetare zuwa ɗayan gefen tafkin.” Sai suka soma tafiya a cikin jirgin ruwan. 23 Amma yayin da suke tafiya, sai ya soma barci. Sai aka soma iska mai ƙarfi a tafkin, kuma jirgin ruwan ya soma cika da ruwa, hakan ya sa su cikin haɗari. 24 Sai suka je suka tashe shi suka ce masa: “Malam, Malam, za mu hallaka!” Sai Yesu ya tashi ya tsawata wa iskar da ruwan, sai iskar da ruwan suka tsaya cik, kuma koꞌina ya yi shuru tsit. 25 Sai ya ce musu: “Ina bangaskiyarku take?” Amma sun ji tsoro sosai, kuma sun yi mamaki, suna ce wa juna: “Wane ne wannan? Da har ya ba wa iska da ruwa umurni, kuma suka yi masa biyayya.”
26 Sai suka kai bakin tafkin a yankin mutanen Garasa, wanda yake a ƙetaren tafkin Galili. 27 Da Yesu ya fita daga jirgin ruwan, sai wani mutum da ke da aljani daga garin ya zo ya same shi. Mutumin ya daɗe yana yawo ba riga, kuma ba ya zama a gida, amma yana zama a wurin da ake binne mutane.* 28 Da ya ga Yesu, sai ya yi ihu, ya faɗi a gabansa, kuma ya ta da murya ya ce: “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙon ka, kada ka azabtar da ni.” 29 (Domin Yesu ya yi ta gaya wa ƙazamin ruhun ya fita daga jikin mutumin. Sau da yawa, aljanin ya sha shiga jikin mutumin,* kuma mutane sun sha ɗaure mutumin da sarƙa a hannu da ƙafa, kuma su tsare shi, amma mutumin yakan tsinka sarƙoƙin, kuma aljanin yakan kai shi wurin da babu kowa.) 30 Sai Yesu ya tambaye shi cewa: “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa ya ce: “Runduna,” domin aljanu da yawa ne sun shiga jikinsa. 31 Sai aljanun suka yi ta roƙon Yesu kada ya tura su rami mai zurfi.* 32 Akwai garken aladu da suke cin abinci a kan tudu, sai aljanun suka roƙe shi ya bar su su shiga jikin aladun, kuma ya ba su izinin. 33 Sai aljanun suka fita daga jikin mutumin, suka shiga jikin aladun, kuma garken aladun suka gangara suka faɗi cikin tafkin, kuma suka nitse. 34 Amma saꞌad da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu, kuma suka ba da labarin abin da ya faru a cikin gari da kuma ƙauyuka.
35 Sai mutane suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka zo wurin Yesu kuma suka ga mutumin da aka fitar da aljanu daga jikinsa sanye da riga, kuma yana cikin hankalinsa, yana zaune kusa da Yesu, sai tsoro ya kama su. 36 Waɗanda abin ya faru a idanunsu sun ba su labarin yadda aka warkar da mutumin da ke da aljanun. 37 Amma mutane da yawa daga kewayen yankin Garasinawa suka gaya wa Yesu cewa ya bar yankinsu domin sun ji tsoro sosai. Sai ya shiga jirgin ruwan don ya tafi. 38 Amma mutumin da aka fitar da aljanu daga jikinsa ya yi ta roƙon Yesu ya bar shi ya bi shi. Amma Yesu ya sallami mutumin kuma ya ce masa: 39 “Ka koma gida, kuma ka ci-gaba da gaya wa mutane abin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi kuma ya yi ta shelar abin da Yesu ya yi masa a dukan garin.
40 Saꞌad da Yesu ya dawo, jamaꞌar sun karɓe shi hannu bibbiyu, domin dukansu sun yi ta jiran sa. 41 Sai ga wani mutum mai suna Yayirus ya zo; mutumin shugaban majamiꞌa ne. Sai ya faɗi a gaban Yesu, kuma ya soma roƙan Yesu ya zo gidansa, 42 domin ꞌyarsa tilo,* wadda shekarunta wajen goma sha biyu ne, tana bakin mutuwa.
Da Yesu yake tafiya, sai jamaꞌar suna ta matsa shi. 43 Akwai wata mata da ta yi shekaru goma sha biyu tana fama da yoyon jini kuma babu wanda ya iya warkar da ita. 44 Ta zo ta bayansa kuma ta taɓa bakin mayafinsa, sai nan da nan, yoyon jinin ya tsaya. 45 Sai Yesu ya ce: “Wa ya taɓa ni?” Saꞌad da dukansu suka ce ba su ba ne, sai Bitrus ya ce: “Malam, ka ga jamaꞌa sun kewaye ka kuma suna ta matsa ka.” 46 Amma Yesu ya ce: “Wani ya taɓa ni, don na san iko ya fita daga jikina.” 47 Da ta ga an gane cewa ita ce, sai matar ta zo, tana rawar jiki kuma ta faɗi a gabansa. Sai ta gaya masa a gaban dukan mutanen dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan da nan. 48 Sai Yesu ya ce mata: “ꞌYata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”
49 Yayin da Yesu yake kan magana, sai wani daga gidan shugaban majamiꞌar ya zo yana cewa: “Yarka ta rasu; kada ka dami Malamin kuma.” 50 Da Yesu ya ji hakan, sai ya ce masa: “Kada ka ji tsoro, ka dai ba da gaskiya, kuma za ta rayu.” 51 Saꞌad da Yesu ya isa gidan, bai bar kowa ya shiga gidan da shi ba, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma baban yarinyar da mamarta. 52 Amma mutane suna kuka da makoki don yarinyar. Sai ya ce musu: “Ku daina kuka, domin yarinyar ba ta mutu ba, amma tana barci ne.” 53 Da suka ji hakan, sai suka soma yi masa dariyar reni, domin sun san cewa yarinyar ta mutu. 54 Amma Yesu ya riƙe hannunta, sai ya ce mata: “Yarinya, ki tashi!” 55 Nan da nan sai yarinyar ta tashi* kuma Yesu ya umurce su su ba ta abinci. 56 Iyayenta sun yi farin ciki sosai, amma Yesu ya ja musu kunne cewa kada su gaya ma kowa abin da ya faru.