Ayyukan Manzanni
7 Amma shugaban firistoci ya tambaye shi, ya ce: “Abubuwan nan da suka faɗa gaskiya ne?” 2 Sai Istifanus ya amsa ya ce: “ꞌYanꞌuwana da ubannina, ku saurara ku ji. Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim, saꞌad da yake Mesofotamiya, kafin ya koma zama a Haran, 3 kuma ya ce masa: ‘Ka bar ƙasarka da danginka kuma ka shiga ƙasar da zan nuna maka.’ 4 Sai ya fita daga ƙasar Kaldiyawa, ya soma zama a Haran. Kuma daga wurin, bayan da babansa ya rasu, Allah ya sa shi ya koma zama a wannan ƙasar da kuke a yanzu. 5 Duk da haka, Allah bai ba shi gādon a ƙasar ba, ko da ma ƙafa ɗaya ne; amma ya yi alkawarin ba shi ƙasar a matsayin gādo kuma bayan shi, ga zuriyarsa, ko da yake ba shi da yaro a lokacin. 6 Ƙari ga haka, Allah ya gaya masa cewa zuriyarsa za su zama baƙi a ƙasar da ba tasu ba, kuma mutanen ƙasar za su mai da su bayi, su kuma ba su wahala* na shekaru ɗari huɗu. 7 Allah ya ce: ‘Zan hukunta ƙasar da suka yi wa bauta, kuma bayan haka, za su fito daga ƙasar kuma su yi mini hidima mai tsarki a wannan wurin.’
8 “Ya kuma yi yarjejeniya da shi game da yin kaciya, sai Ibrahim ya zama baban Ishaku, kuma ya yi masa kaciya a rana ta takwas, Ishaku kuma ya zama baban* Yakubu, Yakubu kuma ya zama baban shugabannin iyalai goma sha biyu. 9 Sai shugabannin iyalan suka yi kishin Yusufu, kuma suka sayar da shi zuwa Masar. Amma Allah ya kasance tare da shi, 10 ya cece shi daga dukan wahalarsa, kuma ya ba shi farin jini da hikima a gaban Firꞌauna sarkin Masar. Firꞌauna ya naɗa shi ya yi mulkin Masar da kuma dukan gidansa. 11 Amma an soma yunwa a dukan ƙasar Masar da Kanꞌana, hakan ya sa mutane sun sha wahala sosai, kuma kakanninmu ba su iya sun sami abinci da za su ci ba. 12 Amma Yakubu ya ji cewa akwai abinci* a Masar, kuma ya aiki kakanninmu wurin a karo na farko. 13 A karo na biyu, Yusufu ya sanar da kansa ga ꞌyanꞌuwansa kuma Firꞌauna ya san iyalin Yusufu. 14 Sai Yusufu ya aika saƙo cewa babansa da dukan danginsa su bar wurin da suke su zo, dukansu mutane sabaꞌin da biyar ne. 15 Sai Yakubu ya tafi Masar kuma ya mutu a wurin. Haka ma kakanninmu. 16 An kai su Shekem, kuma an binne su a kabarin da Ibrahim ya saya da kuɗin azurfa daga hannun yaran Hamor a Shekem.
17 “Da lokaci ya yi kusa da Allah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim, mutanen suka ƙaru kuma suka yi yawa a Masar, 18 har zuwa lokacin da wani sarki ya soma sarauta a Masar, wanda bai san Yusufu ba. 19 Wannan sarkin ya yi wa kakanninmu wayo kuma ya tilasta musu su yashe yaransu, don su mutu. 20 A lokacin nan ne aka haifi Musa, kuma yana da kyau sosai a gaban Allah. An rene shi wata uku a gidan babansa. 21 Amma saꞌad da aka yashe shi, sai ꞌyar Firꞌauna ta ɗauke shi, kuma ta rene shi a matsayin ɗanta. 22 Sai aka koya wa Musa dukan hikimar mutanen Masar. Hakika, shi mai iko ne a furucinsa da kuma ayyukansa.
23 “Saꞌad da ya kai shekara arbaꞌin, sai ya tsai da shawarar kai wa ꞌyanꞌuwansa ziyara,* wato ꞌyaꞌyan Israꞌila. 24 Saꞌad da ya hango ana wulaƙanta ɗaya daga cikinsu, sai ya kāre shi kuma ya rama wa mutumin da ake wulaƙanta ta wajen buga mutumin Masar ɗin har ya mutu. 25 Ya ɗauka ꞌyanꞌuwansa za su gane cewa Allah yana ba su ceto ta wurinsa, amma ba su gane ba. 26 Washegari kuma, ya ga wasunsu guda biyu suna faɗa kuma ya yi ƙoƙarin sasanta su. Yana cewa: ‘Ku ꞌyanꞌuwa ne. Me ya sa kuke wulaƙanta juna?’ 27 Amma wanda yake wulaƙanta ɗanꞌuwansa ya ture shi, yana cewa: ‘Wane ne ya naɗa ka a matsayin shugaba da alƙali a kanmu? 28 Kana so ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar jiya ne?’ 29 Da jin haka, sai Musa ya gudu kuma ya zama baƙo a ƙasar Midiyan, wurin da ya haifi yara maza biyu.
30 “Bayan shekara arbaꞌin, sai malaꞌika ya bayyana a gare shi a cikin itacen ƙaya da ke cin wuta, a dajin Tudun Sinai. 31 Da Musa ya ga hakan, sai ya yi mamaki sosai. Amma da yake matsowa kusa don ya ga abin da yake faruwa, sai ya ji muryar Jehobah* tana cewa: 32 ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allahn Ibrahim, da na Ishaku, da na Yakubu.’ Sai Musa ya soma rawar jiki kuma bai ƙara yin ƙoƙarin sanin abin da yake faruwa ba. 33 Jehobah* ya ce masa: ‘Ka cire takalmanka domin wurin da kake tsaye wuri ne mai tsarki. 34 A gaskiya, na ga wahalar da mutanena suke sha a Masar, na ji kukansu, na kuma sauko don in cece su. Yanzu ka zo, zan aike ka zuwa Masar.’ 35 Wannan Musa da suka ƙi, suna cewa: ‘Wane ne ya naɗa ka a matsayin shugaba da alƙali?’ shi ne kuma Allah ya aika a matsayin shugaba da mai ceto ta wurin malaꞌika da ya bayyana a gare shi a itacen ƙaya da ke cin wuta. 36 Shi ne ya fitar da su, ya kuma yi abubuwan ban mamaki, da alamu a Masar, da Jar Teku, da kuma cikin daji na shekara arbaꞌin.
37 “Wannan ne Musan da ya gaya wa ꞌyaꞌyan Israꞌila cewa: ‘Allah zai ta da muku wani annabi kamar ni daga cikin ꞌyanꞌuwanku.’ 38 Shi ne mutumin da ya kasance a cikin jamaꞌar a daji tare da malaꞌikan da ya yi magana da shi a Tudun Sinai, tare kuma da kakanninmu. Kuma ya karɓo saƙo mai tsarki da ke ba da rai ya ba mu. 39 Kakanninmu sun ƙi su yi masa biyayya, kuma sun ƙi shi. Ƙari ga haka, sun koma Masar a zuciyarsu, 40 sun ce ma Haruna: ‘Ka yi mana alloli da za su ja-gorance mu. Domin ba mu san abin da ya faru da Musan nan ba, wanda ya fitar da mu daga ƙasar Masar.’ 41 A kwanakin, sai suka ƙera gunki mai kama da ɗan bijimi, kuma suka kawo masa hadaya, sai suka soma farin ciki domin aikin hannayensu. 42 Don haka, Allah ya juya musu baya, kuma ya miƙa su ga bautar* rana da wata, da taurari da ke sama, kamar yadda aka rubuta a littafin annabawa cewa: ‘Ya alꞌummar Israꞌila, ba ni ba ne kuka yanka wa dabbobi kuma kuka miƙa wa hadayu na shekaru arbaꞌin a cikin daji. 43 Amma tentin* Molok, da kuma tauraron allah mai suna Refan ne kuka yi ta yawo da su, wato siffofin da kuka ƙera don ku bauta musu. Don haka, zan cire ku daga ƙasar nan in kai ku gaba da Babila.’
44 “A dā kakanninmu suna da tenti da ke shaida musu cewa Allah yana tare da su a daji, kamar yadda ya ba da umurni saꞌad da yake magana da Musa cewa ya yi shi daidai yadda ya gani. 45 Kakanninmu sun karɓe shi, kuma tare da Joshuwa sun shigar da shi ƙasar alꞌummai, waɗanda Allah ya kore su daga ƙasar a gaban kakanninmu. Kuma tentin ya kasance a nan har kwanakin Dauda. 46 Dauda ya sami farin jini a gaban Allah, kuma ya roƙa a ba shi gatan gina wurin zama don Allah na Yakubu. 47 Amma Sulemanu ne ya gina masa gida. 48 Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da aka yi da hannaye, kamar yadda annabi ya faɗa cewa: 49 ‘Sama ne kujerar mulkina, duniya kuma ita ce matashin ƙafafuna. Wane irin gida ne za ku gina mini? Ko kuma ina ne wurin hutuna? In ji Jehobah.* 50 Ba hannuna ne ya yi dukan abubuwan nan ba?’
51 “Ku masu taurin kai da taurin zuciya, da kuma kunnen kashi, kuna ƙin yin biyayya ga ruhu mai tsarki a kullum; kamar yadda kakanninku suka yi, haka ku ma kuke yi. 52 A cikin annabawa, akwai wanda kakanninku ba su tsananta masa ba? Hakika, sun kashe waɗanda suka annabta zuwan mai adalcin nan, shi ne kuma kuka ci amanar sa kuma kuka kashe shi, 53 ku ne kuka karɓi Doka* da aka bayar ta hannun malaꞌiku amma ba ku bi ta ba.”
54 Da jin haka, sai suka ji zafi sosai a zuciyarsu, har suka soma cizon haƙora domin sa. 55 Amma an cika Istifanus da ruhu mai tsarki, sai ya dubi sama, ya ga ɗaukakar Allah, ya kuma ga Yesu yana tsaye a hannun daman Allah, 56 sai ya ce: “Na ga sama ta buɗu kuma na ga Ɗan mutum yana tsaye a hannun daman Allah.” 57 Da jin haka, sai suka yi ihu da dukan muryoyinsu, suka toshe kunnuwansu da hannayensu kuma dukansu suka gudu suka hau kansa. 58 Bayan da suka jefar da shi a bayan gari, sai suka soma jifan sa da duwatsu. Shaidun sun ajiye mayafansu kusa da wani saurayi mai suna Shawulu. 59 Yayin da suke jefan Istifanus da duwatsu, sai ya yi wannan roƙo ya ce: “Ya Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” 60 Sai ya sunkuya, kuma ya ɗaga murya ya ce: “Jehobah,* kada ka hukunta su don wannan zunubin.” Bayan da ya faɗi hakan, sai ya mutu.*