Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
11 Ina fatan za ku yi haƙuri da ni ko da ina ɗan wawanci. Amma a gaskiya, kuna haƙuri da ni! 2 Gama na damu da ku sosai kamar yadda Allah ya damu da ku, domin ni da kaina ne na yi alkawarin aurar da ku ga miji ɗaya, don in iya miƙa ku ga Kristi a matsayin budurwa mai tsarki. 3 Amma ina tsoro cewa kamar yadda maciji ya ruɗi Hauwaꞌu da wayonsa, ku ma za a iya ɓata tunaninku don kada ku riƙa yin abubuwa da zuciya ɗaya da kuma tsabta, yadda ya dace da Kristi. 4 Gama, kuna saurin yarda idan wani ya zo yana yi muku waꞌazi game da wani Yesu ban da wanda muka yi muku waꞌazin sa, ko ya ba ku ruhu ban da wanda kuka karɓa, ko ya yi muku shelar labari mai daɗi ban da wanda kuka karɓa. 5 Domin a ganina, ban yi abu ko guda da ya nuna cewa waɗanda kuke kira manyan manzanni sun fi ni ba. 6 A gaskiya, ko da ban iya magana ba, ina da ilimi; hakika, mun bayyana muku hakan a kowace hanya kuma a kowane abu.
7 Na yi farin ciki saꞌad da nake muku waꞌazin labari mai daɗi na Allah kyauta, na ƙasƙantar da kaina don a iya ɗaukaka ku, shin hakan laifi ne? 8 Na karɓi taimako daga wasu ikilisiyoyi don in yi muku hidima. 9 Duk da haka, saꞌad da nake tare da ku, kuma na bukaci wani abu, ban takura wa kowa ba, domin ꞌyanꞌuwa da suka zo daga Makidoniya sun biya bukatuna sosai. A gaskiya, ta kowace hanya, na yi iya ƙoƙarina don kada in takura muku, kuma zan ci-gaba da yin hakan. 10 Muddin gaskiyar Kristi tana cikina, ba zan daina taƙamar da nake yi a yankunan Akaya ba. 11 Don wane dalili? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah ya san ina ƙaunar ku.
12 Akwai waɗanda suke taƙama cewa su manzanni ne kamar mu. Don haka, zan ci-gaba da yin abin da na saɓa yi domin in hana su samun hujjar yin taƙama. 13 Gama irin mutanen nan manzannin ƙarya ne, masu aikin yaudara, suna yin kamar su manzannin Kristi ne. 14 Kuma ba abin mamaki ba ne, domin Shaiɗan ma da kansa ya ci-gaba da yi kamar shi malaꞌikan haske ne. 15 Don haka, ba abin mamaki ba ne, idan masu yi masa hidima sun ci-gaba da yi kamar su masu hidimar adalci ne. Amma a ƙarshe, za su sami lada da ya yi daidai da ayyukansu.
16 Ina sake cewa: Kada wani ya yi tunani kamar ni wawa ne. Amma ko da kun yi, sai ku amince da ni a matsayin wawa, domin ni ma in ɗan yi taƙama. 17 Ba na bin misalin Ubangiji a yadda nake magana yanzu, amma ina taƙama kamar wawa ne. 18 Tun da mutane da yawa suna taƙama da abubuwan duniya,* ni ma zan yi taƙama. 19 Tun da yake kuna da “wayo” sosai, kuna farin cikin yarda da wawaye. 20 A gaskiya, kuna yarda da duk wanda yake sa ku bauta, da duk wanda yake ƙwace dukiyoyinku da abin da kuke da shi, da duk wanda yake ɗaukaka kansa fiye da ku, da kuma duk wanda ya mare ku.
21 Abin kunya ne mu faɗi wannan, da yake wasu cikinku za su iya ganin kamar mu marasa ƙarfi ne.
Amma idan wasu ba sa jin kunyar yin taƙama, ni ma ba zan ji kunya ba ko da wani zai ga kamar ni wawa ne. 22 Su Ibraniyawa ne? Ni ma haka. Su Israꞌilawa ne? Ni ma haka. Su ꞌyaꞌyan Ibrahim ne? Ni ma haka. 23 Su masu yi wa Kristi hidima ne? Na amsa kamar mahaukaci, ni na fi dukan su: Na yi aiki fiye da su, an saka ni a kurkuku sau da yawa fiye da su, an yi mini dūka sau da yawa, kuma na kusan mutuwa sau da yawa. 24 Sau biyar Yahudawa sun yi mini bulala talatin da tara,* 25 sau uku an yi mini dūka da sanduna, sau ɗaya an jejjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya fashe da ni a teku, na taɓa kwana har na yini a teku; 26 a kullum ina tafiye-tafiye, na shiga haɗari a cikin koguna, na shiga haɗari a hannun ꞌyan fashi, na shiga haɗari a hannun mutanena, na shiga haɗari a hannun mutanen alꞌummai, na shiga haɗari a birni, na shiga haɗari a daji, na shiga haɗari a teku, na shiga haɗari a tsakanin ꞌyanꞌuwa na ƙarya, 27 na yi fama kuma na sha wahala, na yi rashin barci sau da yawa, na yi fama da yunwa da ƙishin ruwa, sau da yawa ba ni da abinci, na sha sanyi, kuma na yi ƙarancin kayan sakawa.
28 Ban da waɗannan abubuwan, akwai wani abu kuma da nake fama da shi a kowace rana: wato yawan damuwa game da dukan ikilisiyoyi. 29 Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji kamar ni ne na rasa ƙarfi ba? Wane ne ya yi tuntuɓe, da ban ji zafi a zuciyata ba?
30 Idan zan yi taƙama, zan yi taƙama da abubuwan da suke nuna rashin ƙarfina. 31 Allah wanda shi ne Uban Ubangiji Yesu, Wanda za a yabe shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba. 32 A Damaskus, gwamna da ke ƙarƙashin Sarki Aretas ya yi ta gadin birnin mutanen Damaskus don ya kama ni, 33 amma an saka ni a cikin kwando kuma aka saukar da ni ta wundo* da ke katangar birnin, kuma na kuɓuce masa.