Ta Hannun Matiyu
2 Bayan da aka haifi Yesu a Baitalami da ke Yahudiya, a lokacin da Hirudus* yake sarauta, sai wasu masanan taurari daga Gabas suka zo Urushalima, 2 suka ce: “Ina wanda aka haifa da zai zama sarkin Yahudawa? Domin mun ga wani tauraro da ke kai mu inda yake saꞌad da muke Gabas, kuma mun zo don mu rusuna* masa.” 3 Saꞌad da Sarki Hirudus da dukan mutanen Urushalima suka ji haka, sai hankalinsu ya tashi. 4 Sai ya tattara dukan manyan firistoci da marubuta, kuma ya tambaye su wurin da aka ce za a haifi Kristi.* 5 Sai suka ce masa: “A Baitalami da ke Yahudiya ne, domin abin da annabi ya rubuta ke nan cewa: 6 ‘Ya ke Baitalami da ke ƙasar Yahuda, ba za ki zama mafi ƙanƙanta a tsakanin gwamnonin Yahuda ba, domin a cikinki za a haifi sarki da zai zama makiyayin mutanena Israꞌila.’”
7 Sai Hirudus ya kira masanan taurarin a ɓoye, don ya san ainihin lokacin da suka ga tauraron. 8 Sai ya tura su Baitalami, kuma ya ce musu: “Ku je ku nemi yaron a koꞌina. Idan kun gan shi, ku dawo ku gaya mini domin ni ma in je in rusuna masa.” 9 Bayan sarkin ya gama magana, mutanen sun kama hanya. Sai tauraron da suka gani saꞌad da suke Gabas ya fito a gabansu kuma ya kai su inda yaron yake. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki sosai. 11 Da suka shiga gidan, sai suka ga yaron da mahaifiyarsa Maryamu, sai suka sunkuya, suka rusuna masa. Sai suka ciro kyautar zinariya, da turaren wuta, da mān mur suka ba shi. 12 Amma, da yake Allah ya yi musu gargaɗi a mafarki cewa kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.
13 Bayan da suka tafi, sai malaꞌikan Jehobah* ya gaya wa Yusufu a mafarki cewa: “Ka tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a wurin har sai na gaya muku ku dawo, domin Hirudus yana so ya nemi yaron don ya kashe shi.” 14 Da daren, Yusufu ya tashi ya ɗauki yaron, da mahaifiyar yaron suka gudu zuwa Masar. 15 Ya zauna a wurin har sai da Hirudus ya mutu. Hakan ya cika annabcin da Jehobah* ya yi ta wajen annabinsa cewa: “Na kirawo ɗana daga Masar.”
16 Da Hirudus ya ga cewa masanan taurarin sun yi masa wayo, sai ya yi fushi sosai. Ya aika a kashe dukan yara maza da ke Baitalami da dukan garuruwan da ke kusa da ita, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da masanan taurarin suka gaya masa cewa sun ga tauraron. 17 Hakan ya cika annabcin da annabi Irmiya ya yi cewa: 18 “An ji wata murya a Rama tana kuka sosai. Rahila ce take kuka don yaranta, kuma ta ƙi a taꞌazantar da ita domin yaranta ba sa nan.”
19 Saꞌad da Hirudus ya mutu, malaꞌikan Jehobah* ya yi magana da Yusufu a mafarki a ƙasar Masar, 20 kuma ya ce: “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku koma ƙasar Israꞌila, domin waɗanda suke so su kashe yaron sun mutu.” 21 Sai ya tashi ya ɗauki yaron da mahaifiyar yaron, suka koma ƙasar Israꞌila. 22 Amma da ya ji cewa ɗan Hirudus, wato Arkilayus ne ya gāji mulkin babansa a Yahudiya, ya ji tsoron komawa wurin. Kuma da yake Allah ya yi masa gargaɗi a mafarki, sai ya koma yankin Galili. 23 Sai ya zo ya zauna a garin da ake kira Nazaret, domin ya cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa: “Za a kira shi mutumin Nazaret.”*