Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
12 Yanzu, game da baiwa da ruhu mai tsarki yake bayarwa, ꞌyanꞌuwana, ba na so ku zama da rashin sani. 2 Kun sani fa, saꞌad da ku mutanen alꞌummai* ne, an shawo kanku kuma an ruɗe ku ku soma bauta wa gumaka marasa magana, da kuma zuwa duk inda suka kai ku. 3 Yanzu zan so ku sani cewa, babu wanda yake magana ta ruhun Allah da zai ce: “Yesu laꞌananne ne!” kuma babu wanda zai iya cewa: “Yesu Ubangiji ne!” sai ta wurin ruhu mai tsarki.
4 Akwai baiwa dabam-dabam, amma ruhu ɗaya ne; 5 akwai hidimomi dabam-dabam, amma Ubangiji ɗaya ne; 6 kuma akwai ayyuka dabam-dabam, duk da haka, Allah ɗaya ne yake yin su a cikin kowa. 7 Amma taimakon da ruhun yake ba wa kowane mutum don amfanin kowa a bayyane yake. 8 Wani an ba shi baiwar yin magana da hikima ta wurin ruhu, wani kuma an ba shi baiwar yin magana da ilimi ta wurin wannan ruhun, 9 wani an ba shi baiwar bangaskiya ta wurin wannan ruhun, wani kuma an ba shi baiwar warkarwa ta wurin wannan ruhun, 10 wani an ba shi baiwar yin ayyukan ban mamaki, wani an ba shi baiwar yin annabci, wani kuma an ba shi baiwar gane saƙon da ya fito daga wurin Allah, wani an ba shi baiwar yin magana a harsuna* dabam-dabam, wani kuma an ba shi baiwar fassara harsuna. 11 Amma duk ayyukan nan ana yin su ne ta wurin ruhu ɗaya, kuma ruhun yana rarraba wa kowa daidai yadda ya so.
12 Kamar yadda jiki ɗaya yake da gaɓoɓi da yawa, kuma dukan gaɓoɓin jikin, duk da cewa suna da yawa, su jiki ɗaya ne, haka ma yake da Kristi. 13 Gama ta wurin ruhu ɗaya an yi wa dukanmu baftisma kuma muka zama jiki ɗaya, ko da mu Yahudawa ne ko mutanen Girka, ko da mu bayi ne ko ꞌyantattu, kuma an sa dukanmu mu sha ruhu ɗaya.
14 Gama ba a yi jiki da gaɓa ɗaya kawai ba, amma da gaɓoɓi da yawa ne. 15 Idan ƙafa ta ce, “Saboda ni ba hannu ba ne, ni ba gaɓar jiki ba ce,” wannan ba zai hana ta zama gaɓar jiki ba. 16 Kuma idan kunne ya ce, “Saboda ni ba ido ba ne, ni ba gaɓar jiki ba ne,” wannan ba zai hana shi zama gaɓar jiki ba. 17 Da a ce dukan jiki ido ne, to da me za a ji? Da a ce dukan jiki kunne ne, to da me za a sunsuna abu? 18 Amma yanzu Allah ya shirya kowace gaɓar jiki yadda yake so.
19 Da a ce dukan jikin gaɓa ɗaya ce, da ina sauran jikin zai kasance? 20 Yanzu su gaɓoɓi da yawa ne, amma jiki ɗaya. 21 Ido ba zai iya ce wa hannu, “Ba na bukatar ka” ba, kuma kai ba zai iya ce wa ƙafa, “Ba na bukatar ka” ba. 22 A maimakon haka, ana bukatar gaɓoɓin jiki da ake ganin kamar ba su da ƙarfi, 23 kuma gaɓoɓin jiki da muke gani kamar ba su da daraja sosai, su ne muka fi ba su girma, don haka, gaɓoɓin jiki marasa kyaun gani, mun fi mai da hankali a kansu, 24 amma gaɓoɓin jikinmu da suke da kyaun gani, ba sa bukatar wani abu. Duk da haka, Allah ya shirya jiki yadda gaɓar da ba ta da daraja za ta zama da muhimmanci sosai, 25 ya yi hakan ne domin kada a samu rashin haɗin kai a jiki, a maimakon haka, domin dukan gaɓoɓin su riƙa kula da juna. 26 Idan wata gaɓa tana shan wahala, sauran gaɓoɓin ma za su sha wahala tare da ita; idan kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sauran gaɓoɓin ma za su taya ta murna.
27 Yanzu, ku jikin Kristi ne, kuma kowannenku gaɓa ne. 28 Kuma Allah ya ba da aiki dabam-dabam ga kowa a ikilisiya: na farko, manzanni; na biyu, annabawa; na uku, malamai; sai masu ayyukan ban mamaki; da masu baiwar warkarwa; da masu ayyukan taimako; da masu iya ja-goranci; da masu iya magana a harsuna dabam-dabam. 29 Ba dukansu ba ne manzanni. Ba dukansu ba ne annabawa. Ba dukansu ba ne malamai. Ba dukansu ba ne suke yin ayyukan ban mamaki. 30 Ba dukansu ba ne suke da baiwar warkarwa. Ba dukansu ba ne suke iya yin magana a harsuna. Ba dukansu ba ne suke iya yin fassara. Ko ba haka ba? 31 Amma ku ci-gaba da yin ƙoƙarin samun baiwa da suka fi girma. Zan kuma nuna muku hanyar da ta fi duka kyau.