Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
2 Gama na riga na yanke shawara cewa ba zan sake zuwa wurinku da baƙin ciki ba. 2 Domin idan na sa ku baƙin ciki, wane ne zai faranta mini rai in ba dai wanda na sa baƙin ciki ba? 3 Dalilin da ya sa na rubuto muku wancan wasiƙar kuwa shi ne, saꞌad da na zo, kada waɗanda ya kamata su sa ni farin ciki su sa ni baƙin ciki, domin ina da tabbaci cewa abin da yake sa ni farin ciki yana sa dukanku ma farin ciki. 4 Gama na rubuta muku wasiƙar ne cikin baƙin ciki mai yawa, da ɓacin zuciya, har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba, amma don ku san yawan ƙaunata* a gare ku.
5 In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni ba ne ya jawo ma baƙin ciki, amma a wani gefe sai in ce dukanku ne ya jawo wa baƙin ciki. Amma ba na so in yi magana da yawa game da batun. 6 Tsawatawa da irin wannan mutum ya sha daga yawancinku ta isa haka; 7 yanzu ya kamata ku gafarta masa kuma ku ƙarfafa* shi, domin kada yawan baƙin ciki ya sha ƙarfinsa.* 8 Don haka ina roƙon ku, ku tabbatar masa cewa kuna ƙaunar sa. 9 Shi ne kuma dalilin da ya sa na rubuta muku wasiƙar: don in ga ko za ku nuna cewa kuna yin biyayya a dukan abubuwa. 10 Duk wanda kuka gafarta masa kome, ni ma na gafarta masa. Gaskiyar kuwa ita ce, duk abin da na gafarta, (in har ma akwai abin da na gafarta) na yi hakan dominku ne a gaban Kristi, 11 domin kada Shaiɗan ya samu dama ya ruɗe mu, gama mun san dabarunsa sarai.
12 Saꞌad da na isa Toruwas don in yi shelar labari mai daɗi game da Kristi, kuma aka buɗe mini ƙofa in yi aikin Ubangiji, 13 hankalina bai kwanta ba, domin ban ga ɗanꞌuwana Titus ba. Sai na yi ban kwana da su kuma na kama hanya zuwa Makidoniya.
14 Amma godiya ga Allah, wanda a kullum yake yi mana ja-goranci a matsayinmu na mabiyan Kristi, kamar sojoji da suke dawowa daga yaƙi bayan sun yi nasara, kuma ta wurinmu yana yaɗa iliminsa kamar turare a koꞌina! 15 Gama a wurin Allah, mu turare mai ƙamshi ne na Kristi cikin waɗanda ake cetowa da kuma tsakanin waɗanda suke hallaka; 16 ga waɗanda suke hallaka, ƙamshin mutuwa ne da ke kai ga mutuwa, kuma ga waɗanda ake ceto, ƙamshin rai ne da ke kai ga rai. Wane ne ya cancanci ya yi ayyukan nan? 17 Mu ne, domin ba ma tallar* maganar Allah, yadda mutane da yawa suke yi, amma muna magana da dukan zuciyarmu cikin gaskiya, kamar waɗanda Allah ya aiko, hakika, muna yin hakan a gaban Allah tare da Kristi.