Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
13 Idan ina magana a harsunan mutane da kuma na malaꞌiku amma ba ni da ƙauna, na zama kamar ƙararrawa ko kuma ganga mai yawan ƙara. 2 Idan ina da baiwar yin annabci da fahimtar dukan asirai masu tsarki da kuma dukan ilimi, kuma ko da ina da dukan bangaskiya da zan iya kawar da tuddai, amma in ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne. 3 Kuma ko da na ba da dukan abubuwan da nake su don in ciyar da mutane, kuma ko da na ba da kaina don in iya yin taƙama, amma in ba ni da ƙauna, ban amfana ba ko kaɗan.
4 Ƙauna tana da haƙuri da kirki. Ƙauna ba ta kishi. Ba ta taƙama, ba ta girman kai, 5 ba ta rashin kunya, ba ta son kai, ba ta saurin fushi. Ba ta riƙe laifi a zuciya. 6 Ba ta murna a kan rashin adalci, amma tana murna don gaskiya. 7 Tana haƙuri da kome, tana yarda da kome, tana bege a kan kome, tana jimre kome.
8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma idan akwai baiwar yin annabci, za a kawar da ita; idan akwai baiwar yin magana a harsuna dabam-dabam, za ta shuɗe; idan akwai baiwar ilimi, za a kawar da ita. 9 Gama iliminmu ba cikakke ba ne, kuma annabcinmu ma ba cikakke ba ne, 10 amma saꞌad da abin da yake cikakke ya zo, za a kawar da abin da bai cika ba. 11 Saꞌad da nake yaro, nakan yi magana kamar yaro, nakan yi tunani kamar yaro, nakan yanke shawara kamar yaro; amma yanzu da na yi girma, na kawar da halayen yara. 12 Yanzu abin da muke gani a madubin ƙarfe, yana nan duhu-duhu, amma a nan gaba, za mu ga kome da kyau.* Abin da na sani a yanzu ba cikakke ba ne, amma a nan gaba, zan samu cikakken sani, kamar yadda Allah ya san ni sosai. 13 Abubuwa ukun nan za su ci-gaba da kasancewa: bangaskiya, da bege, da ƙauna; amma mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.