Ayyukan Manzanni
21 Bayan da muka rabu da su da kyar, sai muka shiga jirgin ruwa muka miƙe zuwa Kos, washegari mun kama hanya zuwa Rodes, kuma daga wurin mun tafi Fatara. 2 Da muka samu jirgin ruwa da zai ƙetare zuwa Finikiya sai muka shiga kuma muka tafi. 3 Bayan da muka hangi tsibirin Saifrus ta hagunmu, sai muka wuce shi, muka ci-gaba da tafiya zuwa Siriya kuma muka sauka a Taya, wurin da jirgin ruwan zai sauke kayan da ke ciki. 4 Sai muka nemi almajiran da ke wurin kuma muka same su, mun kuma zauna a wurin na kwanaki bakwai. Amma ruhu mai tsarki ya sa su su yi ta gaya wa Bulus cewa kada ya shiga Urushalima. 5 Da lokacin tashiwarmu ya yi, sai muka tashi muka kama hanya, amma dukansu tare da mata da yara, sun raka mu har zuwa bayan garin. Sai muka durƙusa a bakin tekun muka yi adduꞌa, 6 kuma muka yi ban kwana da juna. Sai muka shiga jirgin ruwa, su kuma suka koma gidajensu.
7 Da muka ƙarasa tafiyarmu daga Taya zuwa Tolemayis, sai muka gai da ꞌyanꞌuwa da ke wurin, kuma muka zauna tare da su na kwana ɗaya. 8 Washegari, mun bar wurin kuma muka zo Kaisariya, sai muka shiga gidan Filibus mai waꞌazi, wanda yake cikin mazaje bakwai da aka zaɓa, kuma muka zauna tare da shi. 9 Wannan mutum yana da yara mata huɗu da ba su yi aure ba,* waɗanda suke yin annabci. 10 Amma bayan da muka yi ꞌyan kwanaki a wurin, sai wani annabi mai suna Agabus ya gangaro daga Yahudiya. 11 Sai ya zo wurinmu, kuma ya ɗauki ɗamarar Bulus, ya ɗaure hannayensa da ƙafafunsa kuma ya ce: “Ruhu mai tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawa a Urushalima za su ɗaure mutumin da yake da ɗamarar nan, kuma su ba da shi ga mutanen alꞌummai.’” 12 Saꞌad da mu da waɗanda suke wurin muka ji haka, sai muka soma roƙan Bulus kada ya je Urushalima. 13 Sai Bulus ya amsa ya ce: “Me ya sa kuke kuka, kuma kuke ƙoƙarin hana ni yin abin da na ƙudiri niyyar yi?* Ku san cewa, a shirye nake, ba don a ɗaure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.” 14 Da yake mun kasa sa shi ya canja raꞌayinsa, sai muka yi shuru kuma muka ce: “Bari nufin Jehobah* ya cika.”
15 Bayan kwanakin nan sai muka yi shiri, kuma muka kama hanya zuwa Urushalima. 16 Waɗansu almajirai daga Kaisariya sun raka mu, kuma suka kawo mu wurin da za mu sauka a gidan Manason mutumin Saifrus, yana cikin almajirai na farko. 17 Saꞌad da muka isa Urushalima, ꞌyanꞌuwan sun marabce mu hannu bibbiyu. 18 Amma washegari, Bulus ya tafi wurin Yaƙub tare da mu, kuma dukan dattawa suna wurin. 19 Sai ya gaishe su, kuma ya soma ba su labari dalla-dalla game da abubuwan da Allah ya yi wa mutanen alꞌummai ta wurin hidimarsa.
20 Bayan da suka ji hakan, sai suka soma yabon Allah, amma sun ce masa: “Duba ɗanꞌuwa, akwai dubban Yahudawa da masu bi ne, kuma dukansu suna bin Doka* da ƙwazo. 21 Amma sun ji jita-jita game da kai cewa, kana koya wa dukan Yahudawa da ke zama a ƙasashen alꞌummai cewa su daina bin Dokar Musa, kuma kana gaya musu cewa kada su yi wa yaransu kaciya ko kuma su bi alꞌadunmu. 22 To, mene ne za mu yi game da hakan? Babu shakka, za su ji cewa ka iso. 23 Don haka, ka yi abin da muka gaya maka: Akwai mazaje huɗu da suka yi wa Allah alkawari. 24 Ka ɗauki mutanen nan, kuma ka tsabtace kanka tare da su bisa doka, ka biya kuɗin abubuwan da suke bukata don a yi musu aski. Kuma kowa zai san cewa jita-jitar da suka ji game da kai ba gaskiya ba ne. Amma kana yin abin da ya dace kuma kana kiyaye Doka. 25 Game da masu bi da ꞌyan alꞌummai ne, mun rubuta musu wasiƙa game da shawarar da muka yanke cewa, su ci-gaba da guje wa abubuwan da aka miƙa wa gumaka, da jini, da naman dabbar da aka murɗe wuyarta,* da lalata.”*
26 Washegari, sai Bulus ya ɗauki mazajen kuma ya tsabtace kansa tare da su bisa Doka, sai ya shiga haikali don ya sanar da ranakun da tsabtacewar bisa doka za su ƙare, da lokacin da ya kamata a miƙa hadaya don kowannensu.
27 Da kwanaki bakwai na tsabtacewar sun kusan ƙarewa, sai Yahudawa da suka zo daga Asiya suka gan shi a haikali, sai suka zuga dukan jamaꞌar, suka kama shi, 28 kuma suka yi ihu suka ce: “Mutanen Israꞌila, ku taimake mu! Ga mutumin da yake koya wa dukan mutane a koꞌina cewa, su ƙi mutanenmu da Dokarmu da kuma wannan wuri. Ƙari ga haka ma, ya kawo mutanen Girka a cikin haikali kuma ya ƙazantar da wannan wuri mai tsarki.” 29 Dā ma sun ga Tarofimus mutumin Afisa a cikin birnin tare da Bulus kuma suka yi tsammanin cewa Bulus ya kawo shi cikin haikali. 30 Dukan birnin ya ruɗe, kuma mutane suka zo a guje, suka kama Bulus, suka fitar da shi daga haikalin, kuma nan da nan aka rufe ƙofofin. 31 Da suke ƙoƙarin su kashe shi, sai shugaban wani rukunin sojoji ya ji cewa dukan Urushalima ya ruɗe; 32 sai nan da nan ya ɗebi sojoji da manyan sojoji kuma suka tafi wurin a guje. Da jamaꞌar suka ga shugaban da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus.
33 Sai shugaban sojojin ya zo kusa, kuma ya kama Bulus, ya ba da umurni a ɗaure shi da sarƙoƙi biyu; sai ya tambaye shi ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi. 34 Amma wasu daga cikin jamaꞌar suka soma ihu, suna ce abu kaza, wasu kuma wani abu dabam. Da yake bai iya gane ainihin abin da ke faruwa ba saboda ihun da suke yi, sai ya ba da umurni a kai Bulus barikin sojoji. 35 Saꞌad da Bulus ya kai bakin matakala, sai da sojojin suka ɗaga shi sama domin jamaꞌar suna ƙoƙari su ƙwace shi, 36 gama jamaꞌar suna ta bin su a baya, suna ihu suna cewa: “A kashe shi!”
37 Da ake so a kai Bulus barikin sojojin, sai ya ce wa shugaban sojojin: “Don Allah, zan iya gaya maka wani abu?” Sai shugaban sojojin ya ce masa: “Ka iya yaren Girka ne? 38 Ba kai ne mutumin Masar nan da a kwanan baya ya ta da tawaye, kuma ya ja-goranci mutane dubu huɗu masu ɗauke da wuƙa zuwa cikin daji ba?” 39 Sai Bulus ya ce: “Ni Bayahude ne, mutumin Tarsus da ke Kilikiya. Ni ɗan wannan birni mai muhimmanci ne. Don Allah, ina roƙon ka ka ba ni dama in yi wa mutanen nan magana.” 40 Bayan da aka ba wa Bulus dama, sai ya tsaya a kan matakalan kuma ya yi wa mutanen alama da hannunsa. Saꞌad da dukan mutanen suka yi shuru, sai ya soma yi musu magana da Ibrananci, yana cewa: