Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
13 Wannan ne karo na uku da zan zo wurinku. “Domin ta wurin shaidar* mutum biyu ko uku dole a tabbatar da kowace magana.” 2 Ko da yake ba na wurinku a yanzu, amma kamar dai ina tare da ku a karo na biyu, ina yi ma waɗanda suka yi zunubi a dā da kuma sauranku gargaɗi cewa idan na zo, ba zan fasa yi musu horo ba, 3 ta hakan zan nuna muku cewa Kristi yana magana ta wurina, kuma Kristi ba mai rashin ƙarfi ba ne* amma mai nuna iko ne. 4 Hakika, an kashe shi a kan gungume saꞌad da ba shi da ƙarfi, amma yana a raye domin ikon Allah. A gaskiya, mu marasa ƙarfi ne tare da shi, amma za mu yi rayuwa tare da shi domin ikon Allah a gare ku.
5 Ku ci-gaba da gwada kanku don ku san ko kuna cikin bangaskiya; ku ci-gaba da gwada kanku don ku san ko ku waɗanne irin mutane ne. Ko ba ku san cewa Yesu Kristi yana da haɗin kai da ku ba? Sai dai ko Allah ya ƙi ku. 6 Ina fatan za ku gane cewa Allah bai ƙi mu ba.
7 Yanzu muna adduꞌa ga Allah, don kada ku yi wani laifi, ba don mutane su ga cewa Allah ya amince da mu ba, amma don ku yi abin da ya dace, ko da yana kamar Allah ya ƙi mu. 8 Gama ba za mu iya yin wani abu da ya saɓa wa gaskiya ba, sai dai ya goyi bayan gaskiya. 9 Muna farin ciki sosai a duk lokacin da ba mu da ƙarfi amma kuna da ƙarfi. Adduꞌarmu ita ce ku riƙa yin canje-canjen da ake bukata. 10 Shi ya sa nake rubuta muku waɗannan abubuwa yanzu da ba na tare da ku, domin saꞌad da na zo wurinku, ba zan yi amfani da ikon da Ubangiji ya ba ni da zafi-zafi ba, ya ba ni ikon ne don in gina ku, ba don in rusa ku ba.
11 A ƙarshe, ꞌyanꞌuwana, ku ci-gaba da yin farin ciki, ku yi canje-canjen da ake bukata, ku sami ƙarfafa, bari tunaninku ya zama ɗaya, ku ci-gaba da zaman lafiya; kuma Allah na ƙauna da na salama zai kasance tare da ku. 12 Ku gaishe da juna da sumba mai tsarki. 13 Dukan tsarkaka sun aika muku gaisuwarsu.
14 Bari alherin Ubangiji Yesu Kristi, da ƙaunar Allah, da albarkun ruhu mai tsarki su kasance tare da dukanku.