Ayyukan Manzanni
18 Bayan haka, Bulus ya bar Atina kuma ya zo Korinti. 2 Sai ya samu wani Bayahude mai suna Akila ɗan garin Fontus, wanda bai daɗe ba da ya zo daga Italiya tare da matarsa Biriskila, domin Klaudiyus ya ba da doka cewa dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya je wajensu 3 domin yana sanaꞌa iri ɗaya da su. Ya zauna a gidansu kuma ya yi aiki tare da su, da yake su masu saƙa tenti ne. 4 Yakan ba da jawabi* a majamiꞌa a kowace Ranar Assabaci kuma yakan rinjayi Yahudawa da mutanen Girka.
5 Saꞌad da Sailas da Timoti suka zo daga Makidoniya, Bulus ya soma amfani da dukan lokacinsa yana waꞌazin kalmar Allah ga Yahudawa, yana tabbatar musu cewa Yesu ne Kristi. 6 Amma da suka ci-gaba da yin hamayya da shi da kuma zagin sa, sai ya kakkaɓe tufafinsa kuma ya ce musu: “Bari alhakin jininku ya zauna a kanku. Ni dai ba ni da laifi.* Daga yanzu, zan je wurin mutanen alꞌummai.” 7 Sai Bulus ya bar majamiꞌar, ya tafi gidan wani mutum mai suna Titiyus Justus, shi mai bauta wa Allah ne, kuma gidansa yana kusa da majamiꞌar. 8 Amma Kirisbus, shugaban majamiꞌar ya zama mai bin Ubangiji tare da dukan mutanen gidansa. Kuma Korintiyawa da yawa da suka saurara, sun soma ba da gaskiya kuma aka yi musu baftisma. 9 Ƙari ga haka, Ubangiji ya gaya wa Bulus a cikin wahayi da dare cewa: “Kada ka ji tsoro amma ka ci-gaba da yin magana kuma kada ka yi shuru, 10 gama ina tare da kai, kuma ba wanda zai kawo maka hari don ya ji maka rauni; domin ina da mutane da yawa a wannan birnin.” 11 Saboda haka, ya zauna a wurin har shekara ɗaya da rabi yana koyar da kalmar Allah a tsakaninsu.
12 A lokacin da Galiyo ne gwamnan yankin Akaya, Yahudawa sun haɗa kai suka kai wa Bulus hari, kuma suka kai shi wurin zaman shariꞌa, 13 suna cewa: “Mutumin nan yana rinjayar mutane su bauta wa Allah a hanyar da ta saɓa wa doka.” 14 Amma saꞌad da Bulus yake shirin yin magana, sai Galiyo ya ce wa Yahudawan: “Ya ku Yahudawa, da a ce mutumin nan ya yi wani babban laifi ne, da zai dace in yi haƙuri in saurare ku. 15 Amma da yake gardama ce da ta shafi furuci, da sunaye, da kuma dokarku, ai sai ku sasanta batun da kanku. Ba na so in zama mai shariꞌa a kan abubuwan nan.” 16 Sai ya kore su daga wurin zaman shariꞌar. 17 Sai dukansu suka kama Sostanus, shugaban majamiꞌar kuma suka soma dūkan sa a wurin zaman shariꞌar. Amma Galiyo ya ƙi ya sa baki a dukan abubuwan nan.
18 Bayan Bulus ya ƙara yin ꞌyan kwanaki a Korinti, sai ya yi ban kwana da ꞌyanꞌuwan kuma ya shiga jirgin ruwa zuwa Siriya, Biriskila da Akila suna tare da shi. Ya yi aski a Kankiriya domin wata rantsuwa da ya yi. 19 Sai suka iso Afisa, kuma ya bar su a wurin; sai ya shiga wata majamiꞌa kuma ya taimaka wa Yahudawa su fahimci nassosi. 20 Ko da yake sun yi ta roƙonsa ya ɗan ƙara kwanaki da su, bai yarda ba, 21 amma ya yi musu ban kwana, kuma ya ce musu: “Zan sake dawowa wurinku, idan Jehobah* ya yarda.” Sai ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa 22 kuma ya gangara zuwa Kaisariya. Sai ya haura* ya gai da ikilisiyar, daga wurin kuma ya gangara zuwa Antakiya.
23 Bayan ya zauna a Antakiya na ɗan lokaci, sai ya bar wurin, kuma ya tafi wurare dabam-dabam a dukan yankin Galatiya da Farijiya, yana ƙarfafa dukan almajirai.
24 Ana nan, sai wani Bayahude mai suna Afollos da ya fito daga Alekzandiriya ya zo Afisa; ya iya yin magana, kuma yana da ilimin Nassosi sosai. 25 An koyar da mutumin nan hanyar Jehobah,* ruhu mai tsarki ya sa shi ƙwazo sosai, yana kuma magana da koyarwa daidai game da Yesu, amma baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani. 26 Ya soma yin magana a majamiꞌa babu tsoro. Saꞌad da Biriskila da Akila suka ji shi, sai suka ɗauke shi, kuma suka ƙara bayyana masa hanyar Allah da kyau. 27 Ƙari ga haka, da yake yana so ya ƙetare zuwa Akaya, sai ꞌyanꞌuwan suka rubuta wasiƙa ga almajirai da ke wurin. Suna roƙon su su karɓe shi hannu bibbiyu. Da ya isa wurin, ya taimaka ma waɗanda suka zama masu bi ta wurin alherin Allah sosai. 28 Domin ya yi ƙwazo sosai a gaban jamaꞌa wajen ƙaryata Yahudawa, yana nuna musu tabbaci daga Nassosi cewa Yesu ne Kristi.