Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
8 Yanzu game da abincin da aka yi hadaya da shi ga gumaka: Dukanmu mun san cewa muna da ilimi. Ilimi yana sa mutum fahariya, amma ƙauna tana ƙarfafawa. 2 Duk wanda yake ganin kamar ya san wani abu, to har yanzu bai san abin yadda ya kamata ya sani ba. 3 Amma idan mutum yana ƙaunar Allah, Allah ya san mutumin.
4 Game da cin abincin da aka yi hadaya da shi ga gumaka, mun san cewa gunki ba kome ba ne a duniya, mun kuma sani cewa Allah ɗaya ne babu wani. 5 Ko da yake mun sani cewa akwai abubuwa da yawa da ake kiran su alloli, ko a sama ne ko kuma a duniya, kamar yadda ake da “alloli” da yawa da “iyayengiji” da yawa, 6 a gare mu dai Allah ɗaya ne, Uba, wanda dukan abubuwa daga wurinsa ne, har da mu ma; kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kristi, wanda ta wurinsa ne dukan abubuwa suka fito, mu kuma ta wurinsa.
7 Amma ba kowa ba ne ya san wannan. Domin wasu da suka bauta wa gumaka a dā suna ganin kamar abincin da suke ci, abu ne da aka yi hadaya da shi ga gumaka, kuma da yake lamirinsu bai da ƙarfi, sai ya dame su. 8 Amma abinci ba zai sa mu yi kusa da Allah ba; rashin cin abinci ba zai sa yanayinmu ya fi muni ba, cin abinci kuma ba zai sa yanayinmu ya fi kyau ba. 9 Amma ku ci-gaba da lura domin kada ꞌyancinku na yin zaɓi ya zama abin tuntuɓe ga waɗanda ba su da ƙarfi. 10 Gama idan wani ya gan ka, kai da kake da ilimin nan kana cin abinci a haikalin gunki, shin lamirin wannan da ba shi da ƙarfi, ba zai sa shi ya soma cin abincin da aka yi hadaya da shi ga gumaka ba? 11 Saboda haka, ta wurin ilimin nan naka, ka sa ɗanꞌuwanka marar ƙarfi, wanda Kristi ya mutu domin shi ya hallaka. 12 Idan kun yi wa ꞌyanꞌuwanku laifi ta wannan hanyar kuma kun raunata lamirinsu da bai da ƙarfi, kuna yi wa Kristi laifi ne. 13 Shi ya sa idan abinci yana sa ɗanꞌuwana tuntuɓe, ba zan sake cin nama ba, domin kada in sa ɗanꞌuwana yin tuntuɓe.