Ta Hannun Luka
20 Wata rana, saꞌad da Yesu yake haikali, yana koyarwa da kuma yi wa mutane waꞌazin labari mai daɗi, sai manyan firistoci, da marubuta, da kuma dattawa suka zo 2 kuma suka ce masa: “Ka gaya mana, da wane iko kake yin abubuwan nan? Ko kuma wane ne ya ba ka wannan ikon?” 3 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Ni ma zan yi muku wata tambaya, sai ku ba ni amsa: 4 Daga sama ne Yohanna ya samu izinin yin baftisma, ko kuma daga wurin mutane ne?” 5 Sai suka yanke shawara a tsakaninsu suna cewa: “Idan muka ce masa, ‘Daga sama ne,’ zai ce mana, ‘To me ya sa ba ku yarda da shi ba?’ 6 Amma idan muka ce, ‘Daga wurin mutane ne,’ dukan mutanen za su jejjefe mu da duwatsu, domin sun gaskata cewa Yohanna annabi ne.” 7 Sai suka amsa suka ce ba su san daga ina ne ya samu ikon ba. 8 Shi kuma ya ce musu: “Ni ma ba zan gaya muku da wane iko nake yin abubuwan nan ba.”
9 Sai ya soma gaya wa mutanen wannan misalin: “Akwai wani mutum da ya shuka inabi a gonarsa, kuma ya sa wasu manoma su kula da shi, sai ya yi tafiya zuwa wata ƙasa na dogon lokaci. 10 Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawansa zuwa wurin manoman don ya karɓo masa wasu amfanin gonar. Amma manoman suka yi masa dūka, kuma suka sallame shi hannu wofi. 11 Sai ya sake aika wani bawa. Wannan ma, manoman suka yi masa dūka, suka wulaƙanta shi, kuma suka sallame shi hannu wofi. 12 Har ila, mutumin ya sake aika bawa na uku; wannan ma, manoman suka ji masa rauni kuma suka jefar da shi a waje. 13 Don haka, sai mai gonar inabin ya ce, ‘Mene ne zan yi? Zan aike ɗana wanda nake ƙauna sosai. Wataƙila za su daraja shi.’ 14 Saꞌad da manoman suka gan shi, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne zai gāji gonar. Mu kashe shi don gādonsa ya zama namu.’ 15 Sai suka jefa shi bayan gonar inabin, kuma suka kashe shi. To, mene ne mai gonar zai yi wa manoman? 16 Zai zo ya kakkashe waɗannan manoman kuma ya ba da gonar inabin ga wasu manoma dabam.”
Da mutanen suka ji hakan, sai suka ce: “Allah ya sawwaƙe hakan ya faru!” 17 Sai ya kalle su kuma ya ce: “To, mene ne nassin nan yake nufi da cewa: ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne ya zama dutse* mafi amfani a ginin’? 18 Duk wanda ya faɗi a kan dutsen, zai hallaka. Kuma duk wanda dutsen ya faɗi a kansa, dutsen zai murƙushe shi.”
19 A daidai lokacin, sai marubuta da manyan firistoci suka yi ƙoƙari su kama shi, domin sun san cewa ya ba da wannan misalin ne a kansu, amma sun ji tsoron mutanen. 20 Da yake suna neman hanyar kama Yesu, sai suka tura mutanen da suka yi hayar su a ɓoye, su yi kamar su masu adalci ne, don su sa Yesu ya faɗi abin da zai sa su kama shi, kuma su miƙa shi ga hukumomi da kuma gwamna. 21 Sai suka yi masa tambaya suna cewa: “Malam, mun san cewa abin da kake faɗa da abin da kake koyarwa daidai ne, kuma ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah a cikin gaskiya: 22 Ya dace ne mu biya haraji ga Kaisar ko bai dace ba?” 23 Amma da yake ya san wayonsu, sai ya ce musu: 24 “Ku nuna mini tsabar kuɗin dinari.* Hoton nan da sunan nan na waye ne?” Suka ce: “Na Kaisar ne.” 25 Sai ya ce musu: “Ko ta yaya dai, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, amma ku ba Allah abin da yake na Allah.” 26 Sun kasa sa shi ya faɗi abin da zai sa a kama shi a gaban mutanen, amma sun yi mamakin amsar da ya ba su, sai suka yi shuru.
27 Amma wasu Sadukiyawa waɗanda suka ce babu tashin matattu, suka zo suka tambaye shi cewa: 28 “Malam, Musa ya gaya mana cewa, ‘Idan ɗanꞌuwan mutum ya mutu ya bar matarsa kuma ba shi da ꞌyaꞌya, dole ɗanꞌuwansa ya auri matar domin ya haifa wa ɗanꞌuwansa ꞌyaꞌya.’ 29 Akwai ꞌyanꞌuwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure, kuma ya mutu ba tare da ya haifi ꞌyaꞌya ba. 30 Haka ma na biyun 31 da na ukun sun aure ta. Har dukansu bakwai sun aure ta, amma suka mutu ba tare da sun haifi ꞌyaꞌya ba. 32 A ƙarshe, sai matar ma ta mutu. 33 A tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Domin dukansu bakwai sun aure ta.”
34 Yesu ya ce musu: “Mutanen zamanin nan* suna aure da kuma aurarwa, 35 amma waɗanda za su cancanci tashi daga mutuwa, su kuma rayu a zamani mai zuwa, ba za su yi aure ba, ba za a kuma aurar da su ba. 36 Hakika, ba za su sake mutuwa ba, domin za su zama kamar malaꞌiku. Kuma tun da za a ta da su daga mutuwa, za su zama ꞌyaꞌyan Allah. 37 A labarin itacen ƙaya, Musa ya nuna cewa za a ta da matattu, don ya kira Jehobah,* ‘Allah na Ibrahim, da na Ishaku, da na Yakubu.’ 38 Shi ba Allah na matattu ba ne, amma Allah na masu rai ne, domin a wurinsa dukansu suna rayuwa.” 39 Sai wasu marubuta suka amsa suka ce: “Malam, ka faɗi daidai.” 40 Don ba su da ƙarfin zuciya su sake yi masa wata tambaya.
41 Sai shi ma ya tambaye su cewa: “Me ya sa ake ce Kristi ɗan Dauda ne? 42 Don Dauda da kansa ya faɗa a littafin Zabura cewa: ‘Jehobah* ya ce wa Ubangijina: “Ka zauna a hannun damana 43 har sai na sa abokan gābanka su zama matashin ƙafafunka.”’ 44 Don haka, Dauda ya kira shi Ubangiji. To yaya ya zama ɗan Dauda?”
45 Saꞌad da dukan mutanen suke sauraron sa, sai ya ce wa almajiransa: 46 “Ku yi hankali da marubuta, waɗanda suke son sa dogayen riguna suna yawo, kuma suna son mutane su riƙa gaishe su a kasuwanni, da kujerun gaba* a majamiꞌu, da wurin zaman manya a biki, 47 suna kwashe kaya na matan da mazajensu suka mutu, suna yin dogayen adduꞌoꞌi don a gan su. Hukuncin da za a yi musu, zai fi na sauran mutane tsanani.”