Ayyukan Manzanni
17 Sai Bulus da Sailas suka bi ta Amfibolis da Afoloniya suka kai Tasalonika, wurin da akwai majamiꞌar Yahudawa. 2 Sai Bulus ya shiga cikin majamiꞌar kamar yadda ya saba, kuma a Ranar Assabaci guda uku a jere, yana taimaka musu su fahimci Nassosi, 3 da yi musu bayani da kuma yin amfani da abubuwan da aka rubuta, don ya tabbatar musu cewa yana da muhimmanci Kristi ya sha wahala kuma ya tashi daga mutuwa, yana cewa: “Wannan ne Kristi, wato Yesu da nake yi muku shelar sa.” 4 Saboda haka, wasu daga cikinsu suka zama masu bi, kuma suka soma tarayya da Bulus da Sailas, haka ma mutanen Girka da yawa da suke bauta ma Allah, tare da manyan mata da yawa.
5 Amma Yahudawa suka soma kishin su kuma suka tattara mugayen mutane marasa aikin yi a kasuwa. Da dukansu suka taru, sai suka ta da hankalin mutanen garin. Sai suka kai wa gidan Jason hari, suna neman a fitar da Bulus da Sailas zuwa ga masu ta da hankalin. 6 Amma da ba su same su ba, sai suka kai Jason da waɗansu ꞌyanꞌuwa zuwa ga shugabannin garin, suna ihu suna cewa: “Waɗannan mutanen da suke ta da hankali a koꞌina a duniya, suna nan ma, 7 kuma Jason ya marabce su a gidansa. Dukan mutanen nan suna karya dokar Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wai sunansa Yesu.” 8 Da jamaꞌar da shugabannin garin suka ji abubuwan nan, sai hankalinsu ya tashi; 9 bayan da suka sa Jason da sauran ꞌyanꞌuwan su biya kuɗin beli, sai suka bar su su tafi.
10 Nan da nan da dare, sai ꞌyanꞌuwan suka aika Bulus da Sailas zuwa Biriya. Kuma da suka isa wurin, sai suka shiga majamiꞌar Yahudawa. 11 Mutanen Biriya kuwa masu son koyan abubuwa ne fiye da mutanen Tasalonika, domin sun karɓi saƙon da marmari sosai, suka kuma yi binciken Nassosi da kyau a kowace rana, su ga ko abubuwan da Bulus ya faɗa gaskiya ne. 12 Saboda haka, da yawa daga cikinsu suka zama masu bi, har da mata da mazajen Girka da yawa da ake daraja sun ba da gaskiya. 13 Da Yahudawa daga Tasalonika suka ji cewa Bulus yana waꞌazin kalmar Allah a Biriya, sai suka zuga jamaꞌa kuma suka ta da hankalinsu. 14 Nan da nan ꞌyanꞌuwan suka sa Bulus ya tafi bakin teku, amma Sailas da Timoti suka ci-gaba da zama a Biriya. 15 Waɗanda suka raka Bulus sun kawo shi har Atina, sai suka koma bayan da Bulus ya gaya musu cewa su gaya wa Sailas da Timoti su zo su same shi da wuri.
16 Saꞌad da Bulus yake jiran su a Atina, ya yi baƙin ciki sosai da ya ga cewa birnin cike yake da gumaka. 17 Saboda haka, a cikin majamiꞌa, ya soma tattaunawa da Yahudawa da wasu mutanen da suke bauta wa Allah, kuma a kowace rana a kasuwa yakan tattauna da waɗanda ya gani. 18 Amma mabiyan Abikuriya* da mabiyan Zeno* masu koyar da hikimar duniya suka soma gardama da shi, kuma wasunsu suna cewa: “Mene ne mai surutun nan yake so ya faɗa?” Wasu kuma suna cewa: “Kamar dai yana yin shelar alloli da ba na nan ba ne.” Hakan ya faru ne domin yana yin shelar labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu. 19 Sai suka kama shi suka kai shi gaban kotun da ake kira Ariyofagus, suna cewa: “Za mu iya sanin wannan sabuwar koyarwa da kake yin maganarta? 20 Domin kana faɗan abubuwan da ba mu taɓa ji da kunnuwanmu ba kuma muna so mu san abin da abubuwan nan suke nufi.” 21 Gaskiyar ita ce, a duk lokacin da dukan mutanen Atina da baƙin da ke zama a wurin ba sa yin kome, sun fi so su yi amfani da lokacin su koyi sabon abu ko su yi magana a kan sabon abu. 22 Sai Bulus ya tashi tsaye a tsakiyar kotun Ariyofagus kuma ya ce:
“Ya ku mutanen Atina, na dai lura cewa a kowane abu, kuna tsoron alloli* fiye da sauran mutane. 23 Alal misali, saꞌad da nake zagayawa, na lura da kyau abubuwan da kuke yi wa bauta, na ma ga wani bagade da aka yi rubutu a kai cewa, ‘Zuwa ga Allahn da ba mu sani ba.’ Don haka, abin nan da kuke bauta wa da ba ku sani ba, shi nake yi muku shelar sa. 24 Allahn da ya halicci duniya da kome da ke cikinta, shi ne Ubangijin sama da ƙasa, kuma ba ya zama a haikalin da aka gina da hannu; 25 ba ya sa rai cewa mutum zai yi masa hidima, sai ka ce yana bukatar wani abu, domin shi da kansa ne ya ba wa mutane rai da numfashi da kuma dukan abubuwa. 26 Daga mutum ɗaya ya halicci kowace alꞌumma don su zauna a duk duniya, ya zaɓi lokutan da wasu abubuwa za su faru, kuma ya ƙafa iyaka a wurin da ꞌyan Adam za su zauna, 27 domin su nemi Allah, ko wataƙila za su laluba su same shi, ko da yake bai da nesa da kowannenmu. 28 Domin ta wurinsa ne muke rayuwa, muke tafiya kuma muke wanzuwa kamar dai yadda wasu marubutanku suka rubuta cewa, ‘Domin mu yaransa ne.’
29 “Saboda haka, da yake mu ꞌyaꞌyan Allah ne, bai kamata mu yi tunanin cewa Allahn nan yana kamar zinariya ko azurfa ko dutse, kamar wani abu da ꞌyan Adam suka ƙera ba. 30 Gaskiya ne cewa Allah ya ƙyale mutane a dā don ba su san abin da suke yi ba; amma yanzu yana gaya wa dukan mutane a koꞌina cewa su tuba. 31 Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shariꞌa cikin adalci ta wurin mutumin da ya naɗa, ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin ta da mutumin daga mutuwa.”
32 Saꞌad da suka ji game da tashin matattu, sai wasunsu suka soma yin baꞌa, wasu kuma suna cewa: “Za mu sake jin batun nan daga wurinka.” 33 Sai Bulus ya tafi ya bar su, 34 amma wasu mutane sun bi Bulus kuma sun ba da gaskiya. A cikinsu akwai Diyonisiyus, wanda shi alƙali ne a kotun Ariyofagus, da wata mata mai suna Damaris, da wasu kuma.