Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
8 To ꞌyanꞌuwa, yanzu muna so ku san game da alherin da Allah ya yi wa ikilisiyoyin da ke Makidoniya. 2 Saꞌad da suke shan wahala saboda gwaji mai tsanani da suka fuskanta, sun bayar hannu sake da farin ciki, duk da cewa suna cikin tsananin talauci. 3 Gama sun ba da kyautar daidai ƙarfinsu, a gaskiya, na shaida cewa sun bayar ma fiye da ƙarfinsu, 4 yayin da su da kansu sun ci-gaba da roƙon mu sosai mu ba su damar bayarwa don su ma su taimaka a hidimar agaji da ake yi wa tsarkaka. 5 Har ma suka bayar fiye da yadda muka yi tsammani, amma da farko sun ba da kansu ga Ubangiji da kuma mu ta wurin nufin Allah. 6 Don haka mun ƙarfafa Titus cewa, kamar yadda ya soma wannan aikin a tsakaninku, ya kamata ya ƙarasa tattara wannan bayarwa ta yardar rai, tun da yake shi ne ya fara. 7 Kamar yadda kuke kan gaba a cikin kome, a cikin bangaskiya, da magana, da ilimi, da niyyar taimakawa, da kuma yadda kuke ƙaunar mutane kamar yadda muke ƙaunar ku, bari ku zama a kan gaba a bayarwa da yardan rai.
8 Ba umurni nake ba ku ba, amma ina so ku san niyyar da wasu suke da shi kuma in gwada ko ƙaunarku ta ƙwarai ce. 9 Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kristi, cewa ko da yake shi mai arziki ne, ya zama talaka saboda ku, don ku iya zama masu arziki ta wurin talaucinsa.
10 Raꞌayina a wannan batun shi ne: Ai ya fi muku a yanzu ku ƙarasa abin da kuka fara shekarar da ta wuce domin ba wai kawai kun bayar ba ne, amma kuma kuna da niyyar yin hakan. 11 Don haka, yanzu sai ku ƙarasa aikin nan da irin niyyar da kuka fara da ita, kuna bayarwa daidai da abin da kuke da shi. 12 Gama idan akwai niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwar idan bayarwar bisa ga abin da mutum yake da shi ne, ba bisa ga abin da mutum ba shi da shi ba. 13 Domin ba na so ya yi ma wasu sauƙi, kuma ya yi muku wuya; 14 amma don a raba aikin nan daidai yadda ya kamata, sai ku taimake su a yanzu da kuke da hanyar taimako, kuma a lokacin da ba ku da wani abu kuma su suna da shi, sai su taimake ku, ta haka kome zai zama daidai. 15 Kamar yadda yake a rubuce cewa: “Wanda ya tara da yawa, bai yi masa yawa ba, wanda ya tara kaɗan kuwa, bai kasa masa ba.”
16 Mun gode wa Allah wanda ya sa Titus ya ɗauki niyyar taimaka muku kamar yadda muke yi, 17 ba kawai ya yarda ya je wurinku kamar yadda muka ƙarfafa shi ya yi ba, amma ya so ya zo kamar yadda ya riga ya yi niyya. 18 Amma muna aika wani ɗanꞌuwa tare da shi wanda dukan ikilisiyoyi suke yabon sa don shelar labari mai daɗi da yake yi. 19 Ba haka kaɗai ba, amma ikilisiyoyin sun zaɓe shi ya zama abokin tafiyarmu yayin da muke rarraba gudummawar da muka karɓa saboda ɗaukakar Ubangiji, kuma hakan zai nuna cewa muna da niyyar taimakawa. 20 Don haka, ba ma son wani ya zarge mu game da yadda muke rarraba wannan gudummawar da kuka bayar hannu sake. 21 Gama muna ‘iya ƙoƙarinmu mu yi abin da yake daidai ba kawai a gaban Jehobah* ba, amma har a gaban mutane ma.’
22 Ƙari ga haka, muna aika muku ɗanꞌuwanmu tare da su wanda sau da yawa muka gwada shi kuma muka tabbatar da niyyarsa a kan batutuwa da yawa, yanzu kuwa ya ƙara niyyar saboda ya amince da ku sosai. 23 Idan kuwa kuna da wata shakka game da Titus, shi abokin tafiyata ne kuma abokin aikina ne don amfaninku; ko idan kuna da shakka game da ꞌyanꞌuwanmu, su manzannin ikilisiyoyi ne, kuma masu sa a ɗaukaka Kristi ne. 24 Don haka, ku nuna cewa kuna ƙaunar su, kuma ku nuna wa ikilisiyoyin abin da ya sa muke taƙama da ku.