Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
9 Yanzu, game da aikin da aka ba wa tsarkaka, ba lallai ne in rubuta muku game da shi ba, 2 gama na san niyyarku, har ma ina taƙama ga mutanen Makidoniya game da hakan, cewa ku ꞌyanꞌuwa da ke Akaya kun yi shiri tun shekarar da ta wuce, kuma ƙwazonku ya motsa yawancin ꞌyanꞌuwa da ke Makidoniya. 3 Amma ina aika ꞌyanꞌuwan domin kada taƙamar da muke yi game da ku ta zama banza a kan wannan batun, kuma ku kasance a shirye kamar yadda na ce za ku yi. 4 In ba haka ba, idan mutanen Makidoniya suka zo kuma suka ga ba a shirye kuke ba, za mu sha kunya domin yawan taƙamar da muka yi a kanku kuma ku ma za ku sha kunya. 5 Don haka, na ga ya dace in ƙarfafa ꞌyanꞌuwan su zo kafin in zo, domin su tattara kyaututtukan da kuka yi alkawarin bayarwa da dukan zuciyarku, don hakan zai nuna cewa ba tilasta muku aka yi ba amma daga zuciyarku ne.
6 Game da hakan, mutumin da ya shuka iri kaɗan, zai girbe amfanin gona kaɗan, amma mutumin da ya shuka iri da yawa, zai girbe amfanin gona da yawa. 7 Bari kowa ya bayar kamar yadda ya yi niyya a zuciyarsa, ba tare da gunaguni ko tilas ba, domin Allah yana ƙaunar mai bayarwa da farin ciki.
8 Ƙari ga haka, Allah yana iya sa dukan alherinsa su yi yawa a kanku, domin ku samu duk abin da kuke bukata a kowane lokaci, kuma ku samu abubuwa da yawa da kuke bukata don ku iya yin kowane irin aiki mai kyau. 9 (Kamar yadda yake a rubuce, cewa: “Ya bayar hannu sake; ya ba wa talakawa. Adalcinsa zai kasance har abada.” 10 Allah wanda yake ba da iri ga mai shuki da kuma abinci, zai ba ku iri kuma ya ninka shi don ku shuka, kuma ya sa abin da za ku girba daga adalcinku ya yi yawa sosai.) 11 A kowane abu, ana sa ku kasance da wadata don ku iya zama masu bayarwa a hanyoyi dabam-dabam, domin ta wurin abin da muke bayarwa, mutane su gode wa Allah; 12 domin hidimar nan da kuke yi ba kawai yana biyan bukatun tsarkaka ba, amma yana taimakawa a hanyoyi da yawa wajen sa mutane su gode wa Allah sosai. 13 Ta wurin shaidar da hidimar agajin nan take bayarwa game da ku, mutane suna ɗaukaka Allah domin kuna rayuwar da ta jitu da labari mai daɗi game da Kristi da kuke shelar sa, kuma kuna ba su da dukan mutane hannu sake. 14 Kuma ta wurin roƙon Allah da suke yi a madadinku, sun nuna cewa suna ƙaunar ku domin alherin Allah da ya wuce gaban misali yana kanku.
15 Mun gode wa Allah don wannan kyautarsa da ba za a iya bayyanawa ba.