Ayyukan Manzanni
23 Yayin da Bulus ya zuba wa membobin Sanhedrin* ido, sai ya ce: “ꞌYanꞌuwana, har wa yau zuciyata ba ta damu na ko kaɗan domin irin rayuwar da na yi a gaban Allah.” 2 Da jin wannan, sai Hananiya shugaban firistoci ya umurci waɗanda suke tsaye kusa da shi su bugi bakinsa. 3 Sai Bulus ya ce masa: “Allah zai buge ka, kai bangon da aka shafa wa farin fenti. Shin ka zauna za ka yi mini shariꞌa bisa Doka* kuma kai da kanka kana taka Doka ta wajen ba da umurni cewa a buge ni?” 4 Sai waɗanda suke tsaye kusa da Bulus suka ce: “Kana zagin shugaban firistoci na Allah?” 5 Sai Bulus ya ce: “ꞌYanꞌuwa, ban san cewa shi shugaban firistoci ba ne. Domin a rubuce yake cewa, ‘Kada ka zagi mai mulkin jamaꞌarka.’”
6 Da Bulus ya gane cewa wasu daga cikin jamaꞌar Sadukiyawa ne, wasu kuma Farisiyawa, sai ya ta da murya a cikin Sanhedrin ya ce: “ꞌYanꞌuwa, ni Bafarisi ne, kakannina kuma Farisiyawa ne. Ana yi mini shariꞌa ne domin ina da begen tashin matattu.” 7 Da ya faɗi hakan, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, kuma jamaꞌar sun rabu kashi biyu. 8 Gama Sadukiyawa sun ce babu tashin matattu, babu malaꞌiku kuma babu ruhu, amma Farisiyawa sun amince da dukansu. 9 Sai suka soma hayaniya sosai, kuma wasu daga cikin marubutan Farisiyawa suka tashi suka soma gardama mai zafi suna cewa: “Ba mu sami wannan mutum da wani laifi ba, mai yiwuwa wani ruhu ko kuma malaꞌika ne ya yi masa magana—.” 10 Da gardamar ta yi zafi sosai, shugaban sojojin ya ji tsoro kada su yi kaca-kaca da Bulus. Sai ya umurci sojoji su sauka su ƙwato Bulus ƙarfi da yaji daga wurin mutanen kuma su kai shi barikin sojojin.
11 Amma washegari da dare, Ubangiji ya tsaya kusa da shi kuma ya ce masa: “Kada ka ji tsoro, kamar yadda ka yi ta ba da shaida game da ni a Urushalima, dole ne ka ba da shaida game da ni a Roma.”
12 Washegari, Yahudawa sun ƙulla makirci har da rantsuwa cewa ba za su ci ko su sha ba har sai sun kashe Bulus. 13 Mutane fiye da arbaꞌin ne suka ƙulla wannan makircin tare da rantsuwa. 14 Mutanen nan sun je wurin manyan firistoci da dattawa kuma suka ce: “Mun yi wata rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba har sai mun kashe Bulus. 15 Don haka, ku haɗa kai da membobin Sanhedrin,* ku gaya wa shugaban sojojin cewa ya kawo shi wurinku, kamar dai kuna so ku daɗa bincika ƙarar da aka kawo a kansa da kyau. Mu kuma za mu kasance a shirye don mu kashe shi kafin ya yi kusa.”
16 Amma ɗan ꞌyarꞌuwar Bulus ya ji abin da suke shirin yi, sai ya shiga barikin sojojin ya gaya wa Bulus. 17 Sai Bulus ya kira ɗaya daga cikin jamiʹan sojojin kuma ya ce masa: “Ka kai wannan saurayin wurin shugaban sojoji domin yana da wani abin da zai gaya masa.” 18 Sai ya kai saurayin wurin shugaban sojojin kuma ya ce: “Fursunan nan mai suna Bulus ya kira ni kuma ya ce mini in kawo maka saurayin nan domin yana da wani abin da zai gaya maka.” 19 Sai shugaban sojojin ya kama hannun saurayin kuma ya ja shi gefe, sai ya tambaye shi cewa: “Mene ne kake so ka gaya mini?” 20 Sai saurayin ya ce: “Yahudawa sun shirya su roƙe ka ka kawo Bulus gaban membobin Sanhedrin gobe, kamar dai suna so su daɗa jin bayani game da ƙarar da aka kawo a kansa. 21 Amma kada ka yarda su ruɗe ka, domin mutane fiye da arbaꞌin a cikinsu suna shirin su tare shi a hanya, kuma sun yi rantsuwa cewa ba za su ci ko su sha ba har sai sun kashe shi; kuma suna a shirye yanzu, suna jira ka amince da roƙonsu.” 22 Sai shugaban sojojin ya sallami saurayin bayan ya umurce shi cewa: “Kada ka gaya wa kowa cewa ka gaya mini wannan batun.”
23 Sai ya kira biyu daga cikin jamiꞌan sojojin kuma ya ce musu: “Ku shirya sojoji ɗari biyu, da sojoji sabaꞌin masu hawan dawakai, da sojoji ɗari biyu masu faɗa da māshi, su tafi Kaisariya wajen ƙarfe tara na dare.* 24 Ƙari ga haka, ku shirya wa Bulus dawakai da za su kai shi wurin Gwamna Felis lafiya.” 25 Kuma shugaban sojojin ya rubuta wasiƙa kamar haka:
26 “Daga Klaudiyus Lisiyas zuwa ga Mai Girma, Gwamna Felis: Ina gaisuwa! 27 Yahudawa sun kama mutumin nan kuma suna dab da kashe shi, sai na zo da sauri tare da sojojina na ƙwato shi daga hannayensu domin na ji cewa shi ɗan ƙasar Roma ne. 28 Da yake ina so in san laifin da ya yi da suke zargin sa, sai na kawo shi gaban Sanhedrin nasu. 29 Na gano cewa zargin da ake yi masa ya shafi abubuwa ne game da Dokarsu, amma babu zargi da ake masa da ya isa a kashe shi, ko kuma a ɗaure shi a kurkuku. 30 Amma da na sami labari cewa ana ƙulla masa mugunta, sai nan take na aika shi wurinka kuma na umurci waɗanda suke zargin sa su kawo ƙarar sa gabanka.”
31 Sai sojojin suka ɗauki Bulus bisa ga umurnin da aka ba su suka kai shi Antifatiris da dare. 32 Washegari, sai suka bar sojoji masu hawan dawakai su ci-gaba da tafiya da shi, su kuwa suka koma barikin. 33 Saꞌad da sojoji masu hawan dawakan suka isa Kaisariya, sai suka ba wa gwamnan wasiƙar, suka kuma miƙa masa Bulus. 34 Sai ya karanta wasiƙar, kuma ya yi tambaya ko daga wane yanki ne Bulus ya fito, sai ya gano cewa shi daga Kilikiya ne. 35 Sai gwamnan ya ce: “Zan saurari ƙararka da kyau idan masu zargin ka sun iso.” Sai ya ba da umurni cewa a yi gadin sa a fādar Hirudus.*