Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
2 Don haka, saꞌad da na zo wurinku ꞌyanꞌuwa, ban yi ƙoƙarin burge ku da maganata ko hikimata saꞌad da nake gaya muku asiri mai tsarki na Allah ba. 2 Gama na yanke shawara cewa ba zan yi muku magana a kan kome ba sai dai game da Yesu Kristi, da kuma yadda aka kashe shi a kan gungume. 3 Kuma na zo muku da rashin ƙarfi da tsoro da kuma rawar jiki sosai; 4 Ƙari ga haka, ban yi amfani da kalmomin rinjaya da masu hikima suke amfani da su saꞌad da nake jawabi da kuma waꞌazi ba, amma kalmomina sun nuna ruhu da kuma ikon Allah, 5 domin kada ku ba da gaskiya saboda hikimar mutane, amma saboda ikon Allah.
6 Muna yin maganar hikima a tsakanin waɗanda suka manyanta, amma ba hikimar wannan zamanin,* ko hikimar masu mulkin wannan zamanin waɗanda za su shuɗe ba. 7 Muna magana ne a kan hikimar Allah da ke cikin asiri mai tsarki, wato hikimar da take a ɓoye, wadda Allah ya tsara kafin zamanin nan don mu sami ɗaukaka. 8 Wannan hikima ce da babu wani daga cikin masu mulkin wannan zamanin* da ya sani. Don da a ce sun sani, da ba su kashe Ubangiji mai ɗaukaka ba.* 9 Amma kamar yadda aka rubuta cewa: “Ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, kuma babu mutumin da ya taɓa tunani a zuciyarsa abubuwan da Allah ya shirya domin masu ƙaunar sa.” 10 Amma mu ne Allah ya bayyana mana su ta wurin ruhunsa, gama ruhun yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah.
11 Wane ne a cikin mutane ya san abin da ke cikin zuciyar mutum in ba mutumin da kansa ba? Haka ma, ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai ruhun Allah. 12 Ruhun da muka karɓa ba na duniya ba ne, amma ruhu ne daga wurin Allah, don mu iya sanin abin da Allah ya ba mu da zuciya ɗaya. 13 Muna kuma gaya muku waɗannan abubuwa, ba da kalmomin da ake koyarwa ta hikimar mutum ba, sai dai ta ruhu, yayin da muke bayyana abubuwan ruhu da kalmomin ruhu.
14 Amma mutumin da ke rayuwa bisa shaꞌawoyin jiki, ba ya amincewa da abubuwan ruhun Allah, domin wawanci ne a wurinsa; kuma ba zai taɓa iya sanin su ba, domin ruhu ne yake taimaka wa mutum ya bincika su. 15 Amma mutumin da ke rayuwa bisa ruhu yana bincika kome, kuma babu mutumin da ke bincika shi. 16 Gama “wane ne ya san tunanin Jehobah,* don ya koyar da shi?” Amma mu dai muna tunani kamar Kristi.