Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
10 Yanzu, ni da kaina, Bulus, ina roƙon ku ta wurin sauƙin kai* da kuma alherin Kristi, ni da ake yi mini ganin marar ƙarfin hali saꞌad da ina tare da ku, amma mai ƙarfin hali saꞌad da ba na tare da ku. 2 Fatana shi ne kafin in zo, waɗanda suke ganin kamar muna yin rayuwa irin na mutanen duniya, sun riga sun canja domin kada in tsawata musu sosai. 3 Ko da yake muna zama a duniya,* ba ma yaƙi kamar mutanen duniya.* 4 Gama makaman da muke yaƙi da su ba na duniya ba ne, amma na ikon Allah ne, kuma da su muke rusa abubuwa da suka tsaya da ƙarfi kamar katanga. 5 Gama muna rushe raꞌayoyi, da kowane abu da aka ɗaga sama don a hana mutane sanin Allah, muna komar da kowane tunani cikin bauta kuma mu sa ya yi biyayya ga Kristi; 6 kuma a shirye muke mu hukunta duk wani mai rashin biyayya da zarar biyayyarku ta cika.
7 Kuna ganin abubuwa bisa yadda suke a zahiri. Idan wani yana da tabbaci cewa shi na Kristi ne, bari ya sake yin tunani a kan wannan batun, wato: Kamar yadda shi na Kristi ne, haka mu ma muke. 8 Ko da zan ɗan yi taƙama fiye da kima saboda ikon da Ubangiji ya ba mu don mu gina ku, ba don mu rushe ku ba, ba zan sha kunya ba. 9 Domin ba na so ya zama kamar ina ƙoƙarin tsorata ku da wasiƙuna. 10 Gama sun ce: “Wasiƙunsa na da muhimmanci* da kuma ƙarfi, amma in ka gan shi ido da ido ba shi da ƙarfin hali, kuma maganarsa ba ta da daɗin ji.” 11 Bari irin wannan mutum ya san cewa, abin da muka faɗa ta wurin wasiƙu saꞌad da ba ma nan, shi ne kuma za mu yi saꞌad da muke nan. 12 Gama ba za mu taɓa ce muna matsayi ɗaya ko mu gwada kanmu da wasu da suke yabon kansu ba. Amma saꞌad da suka auna kansu da kansu, kuma suka gwada kansu da kansu, sun nuna cewa ba su san kome ba.
13 Amma ba za mu yi taƙama har mu wuce iyakarmu ba, sai dai a cikin iyakar yankin da Allah ya auna mana, kuma wannan yankin ya kai har zuwa inda kuke. 14 A gaskiya, ba mu wuce iyakarmu ba saꞌad da muka isa wurinku, gama mu ne muka fara isa wurinku da labari mai daɗi game da Kristi. 15 Ba ma taƙama mu wuce iyakarmu game da aikin da wani ya yi ba, amma fatanmu shi ne yayin da bangaskiyarku take ci-gaba da ƙaruwa, abin da muka yi a cikin iyakarmu zai ci-gaba da ƙaruwa. Ta hakan za mu ci-gaba da yin ƙoƙari, 16 har ma mu iya yin shelar labari mai daɗi ga ƙasashe da ke gaba da ku, don kada mu yi taƙama a kan abin da an riga an yi a cikin iyakar yankin wani. 17 “Amma wanda yake taƙama, bari ya yi taƙama da Jehobah.”* 18 Gama, ba wanda ya yabi kansa ne ake amincewa da shi ba, amma wanda Jehobah* ya yaba masa ne.