Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
1 Daga Bulus, wanda ya zama manzon Kristi Yesu bisa ga nufin Allah, tare da ɗanꞌuwanmu Timoti, zuwa ga ikilisiyar Allah da ke Korinti, har da dukan tsarkaka da ke duk faɗin Akaya:
2 Bari alheri da salama daga Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Kristi su kasance tare da ku.
3 Yabo ya tabbata ga Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, Uba mai yawan tausayi, da kuma Allah da ke ƙarfafa mu* a kowane irin yanayi, 4 wanda yake ƙarfafa mu a dukan wahalolinmu,* domin mu ma mu iya ƙarfafa wasu a kowanne irin wahala* da suke sha, da ƙarfafar da muka samu daga wurin Allah. 5 Gama, kamar yadda muke shan wahala sosai saboda Kristi, haka ma muke samun ƙarfafa sosai ta wurin Kristi. 6 Idan muna shan wahaloli,* muna shan su ne domin ku samu ƙarfafa da ceto; kuma idan ana ƙarfafa mu, domin a ƙarfafa ku ne, ƙarfafar ce take taimaka muku ku jimre irin wahalolin da mu ma muke sha. 7 Kuma begenmu a gare ku tabbatacce ne, domin mun san cewa, kamar yadda kuke shan irin wahalolin da muke sha, za ku samu irin ƙarfafar da ake mana.
8 ꞌYanꞌuwa, muna so ku san game da ƙuncin da muka sha a yankin Asiya. Mun sha wahala sosai fiye da ƙarfinmu, har ba mu san cewa za mu rayu ba. 9 A gaskiya, mun ma ɗauka cewa an yanke mana hukuncin kisa. Wannan ya faru ne don kada mu dogara ga kanmu, amma mu dogara ga Allah wanda yake ta da matattu. 10 Ya ceto mu daga yanayin da ya sa mun kusan rasa rayukanmu, kuma muna da bege cewa zai ci-gaba da yin hakan. 11 Ku ma za ku iya taimaka mana ta wurin yin adduꞌa dominmu, don mutane da yawa su yi godiya a madadinmu saboda alherin da aka yi mana ta wurin amsa adduꞌoꞌin mutane da yawa.
12 Abin da muke taƙama da shi shi ne, lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi shaꞌani a duniya, musamman ma da ku da zuciya ɗaya kuma tsakaninmu da Allah, ba da hikimar duniya ba, amma da alherin Allah. 13 Gama abin da muke rubuta muku, abu ne da za ku iya karanta da kuma fahimta,* kuma ina fatan cewa za ku ci-gaba da fahimtar abubuwan nan sosai,* 14 kamar yadda wasu a cikinku suka fahimci cewa mu ne dalilin da ya sa kuke taƙama, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama don ku, a ranar Ubangijinmu Yesu.
15 Da yake ina da wannan tabbacin, shi ya sa na so in zo wurinku da farko domin ku yi farin ciki a karo na biyu.* 16 Na shirya in ziyarce ku saꞌad da nake kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sake dawowa wurinku daga Makidoniya, saꞌan nan ku ɗan raka ni saꞌad da na kama hanya zuwa Yahudiya. 17 Saꞌad da na yi wannan shirin, ban ɗauki batun da wasa ba, kuna ganin na yi hakan ne? Ko dai na yi shirin nan da halin mutuntaka* ne, don in ce “E, e” daga baya kuma in ce “Aꞌa, aꞌa”? 18 Kamar yadda Allah mai aminci ne, haka ma za ku iya amincewa da maganarmu, ba za mu ce muku “e” kuma daga baya mu ce muku “aꞌa” ba. 19 Gama Ɗan Allah, Yesu Kristi, wanda ni da Silbanus,* da Timoti, muka yi muku waꞌazin sa, bai zama “e,” daga baya kuma ya zama “aꞌa” ba, amma “e” ya zama “e” game da shi. 20 Gama kome yawan alkawuran da Allah ya yi, sun zama “e” ta wurinsa. Saboda haka, ta wurinsa ne kuma muke ce wa Allah “Amin,” domin mu ɗaukaka Allah. 21 Amma Allah ne yake ba mu tabbaci cewa, mu da ku na Kristi ne, kuma shi ne ya shafe* mu. 22 Ya kuma sa hatiminsa a kanmu, ya saka ruhu a zukatanmu, kuma ruhun ya zama tabbaci na abin da ke zuwa a nan gaba.
23 Bari Allah ya hukunta ni, idan ƙarya nake yi cewa dalilin da ya sa ban zo Korinti ba shi ne don kada in ƙara muku baƙin ciki. 24 Ba wai mu ne muke da iko a kan bangaskiyarku ba, amma mu abokan aikinku ne don ku yi farin ciki, domin bangaskiyarku ce take sa ku tsaya daram.