Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
5 Na ji labari cewa akwai wani a cikinku da ke yin lalata,* kuma lalata* ce irin wadda ba a ma yi a tsakanin mutanen alꞌummai, wato wani mutum yana kwana da matar babansa.* 2 Har ma kuna taƙama da shi? Shin bai kamata ku yi baƙin ciki, domin a fitar da mutumin da ya yi wannan abu daga cikinku ba? 3 Ko da yake ba na tare da ku a zahiri, ina tare da ku a cikin ruhu, kuma na riga na yanke wa mutumin da ya yi wannan abin hukunci, kamar dai ina tare da ku a zahiri. 4 Saꞌad da kuka taru a cikin sunan Ubangijinmu Yesu, da sanin cewa ina tare da ku a cikin ruhu, da ikon Ubangijinmu Yesu, 5 dole ne ku miƙa mutumin nan ga Shaiɗan don a kawar da halin lalata da ya kawo cikin ikilisiya,* domin ruhun ya iya samun ceto a ranar Ubangiji.
6 Taƙamar da kuke yi ba ta da kyau. Ba ku san cewa ɗan ƙaramin yisti ne yake kumburar da ƙullun fulawa gabaki-ɗaya ba? 7 Ku kawar da tsohon yistin, don ku zama sabon ƙullun fulawa da ba shi da yisti. Hakika, haka ma kuke, domin an riga an yi hadaya da Kristi ɗan ragonmu na Bikin Ƙetarewa. 8 Don haka, sai mu ci-gaba da yin bikin ba da tsohon yisti, ko yistin mugunta da na zunubi ba, amma da burodi marar yisti na aminci da gaskiya.
9 A wasiƙata, na gaya muku cewa ku daina yin tarayya da mutane masu yin lalata,* 10 ba wai ina nufin dukan masu yin lalata* ko masu haɗama, ko masu damfara, ko masu bautar gumaka a wannan duniyar ba ne. In ba haka ba, za ku bukaci ku fita daga duniya gabaki-ɗaya. 11 Amma ina rubuta muku a yanzu cewa ku daina tarayya da duk wani da ya kira kansa ɗanꞌuwa amma shi mai yin lalata* ne, ko mai haɗama, ko mai bautar gumaka, ko mai zage-zage, ko mai buguwa, ko mai damfara, kada ma ku ci abinci da irin wannan mutumin. 12 Ina ruwana da shariꞌanta waɗanda ba sa cikin ikilisiya? Ku shariꞌanta waɗanda suke cikin ikilisiya, 13 saꞌan nan ku bar Allah ya shariꞌanta waɗanda ba sa cikin ikilisiya. “Ku cire mugun nan daga cikinku.”