Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
11 Ku bi misalina kamar yadda nake bin misalin Kristi.
2 Ina yaba muku domin kuna tuna da ni a kome, kuna kuma riƙe da koyarwar nan sosai daidai yadda na koya muku. 3 Amma ina so ku san cewa, shugaban kowane namiji Kristi ne; shugaban mace namiji ne; shugaban Kristi kuma Allah ne. 4 Duk wani namiji da yake adduꞌa ko annabci da kansa a rufe ya kunyatar da kansa;* 5 kuma duk wata mace da take adduꞌa ko annabci ba tare da ta rufe kanta ba, ta kunyatar da kanta,* domin ɗaya take da macen da ta aske gashin kanta. 6 Gama idan mace ba ta rufe kanta ba, sai ta yanke gashin kanta; idan abin kunya ne ga mace ta yanke gashin kanta ko ta aske shi, sai ta rufe kanta.
7 Kada namiji ya rufe kansa, da yake shi kamannin Allah ne da kuma ɗaukakarsa, amma mace darajar namiji ne. 8 Gama Allah bai yi namiji daga jikin mace ba, amma ya yi mace daga jikin namiji. 9 Ƙari ga haka, ba a halicci namiji domin ta mace ba, amma an halicci ta mace domin namiji. 10 Saboda haka, ya kamata mace ta ɗaura wani abu a kanta don ta nuna cewa tana ƙarƙashin shugabancin wani, saboda malaꞌiku.
11 Ban da haka ma, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, kuma namiji ba a rabe yake da ta mace ba. 12 Gama kamar yadda aka yi mace daga jikin namiji, haka ma ake haifan namiji daga jikin mace; amma dukan abubuwa daga wurin Allah ne. 13 Ku duba da kanku ku gani: Ya dace ne mace ta yi adduꞌa ga Allah ba tare da ta rufe kanta ba? 14 Shin yadda Allah ya halicci mutane bai nuna muku cewa idan namiji ya bar dogon gashi hakan abin kunya ne a gare shi ba? 15 Amma idan mace ta bar dogon gashi, hakan ɗaukaka ce a gare ta. Gama Allah ya ba ta gashi don ta rufe kanta. 16 Idan wani yana so ya yi gardama don ya goyi bayan wata alꞌada dabam da wannan, ba mu da wata alꞌada, haka ma ikilisiyoyin Allah.
17 Amma yayin da nake ba ku waɗannan umurnan, ba na yaba muku, domin taronku ba ya jawo sakamako mai kyau, sai dai sakamako marar kyau. 18 Da farko na ji cewa, saꞌad da kuka taru a ikilisiya, ana samun rashin haɗin kai a tsakaninku; kuma na yarda cewa wasu abubuwa da na ji gaskiya ne. 19 Hakika, dole ne a samu ƙungiyoyi dabam-dabam a tsakaninku, don a iya gane waɗanda Allah ya amince da su.
20 Saꞌad da kuka taru a wuri ɗaya, ba don ku ci Abincin Yamma na Ubangiji ba ne. 21 Gama, idan lokacin cin abincin ya yi, kun riga kun ci abincinku na yamma, a sakamakon haka, wani yana jin yunwa, wani kuma ya bugu. 22 Ba ku da gidaje da za ku zauna ku ci kuma ku sha a ciki ne? Ko dai kun rena ikilisiyar Allah ne? Ko kuna ƙoƙarin kunyatar da waɗanda ba su da kome ne? Me zan gaya muku? In yaba muku ne? A wannan batun ban yaba muku ba.
23 Gama kamar yadda Ubangiji ya koyar da ni, haka na koyar da ku, wato a daren da za a ci amanar Ubangiji Yesu, ya ɗauki burodi, 24 kuma bayan da ya yi godiya, ya kakkarya kuma ya ce: “Wannan yana wakiltar jikina wanda zan bayar domin ku. Ku dinga yin haka don tunawa da ni.” 25 Ya yi hakan ma da kofin, bayan da suka gama cin abincin yamma, ya ce: “Wannan kofi yana wakiltar sabuwar yarjejeniya wadda aka tabbatar da ita da jinina. Ku dinga yin hakan a duk lokacin da kuka sha shi, don tunawa da ni.” 26 Gama a duk lokacin da kuka ci wannan burodin, kuma kuka sha daga kofin nan, kuna shelar mutuwar Ubangiji har sai ya dawo.
27 Saboda haka, duk wanda ya ci burodin, ko ya sha kofin Ubangiji ba tare da ya cancanta ba, ya yi wa jiki da jinin Ubangiji zunubi. 28 Da farko, bari kowane mutum ya amince da kansa bayan ya bincika kansa sosai, bayan haka ne kawai zai iya cin burodin kuma ya sha daga kofin. 29 Gama duk wanda ya ci kuma ya sha ba tare da ya fahimci abin da jikin Ubangiji yake nufi ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne. 30 Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma rashin lafiya. Kuma da yawa suna mutuwa. 31 Amma idan muka bincika kanmu da kyau, ba za a hukunta mu ba. 32 Amma idan aka hukunta mu, Jehobah* ne ya yi mana horo, domin kada a yanke mana hukunci tare da duniya. 33 Saboda haka ꞌyanꞌuwana, saꞌad da kuka taru don ku ci abincin, ku jira juna. 34 Idan wani yana jin yunwa, ya ci abinci a gidansa, domin kada taronku ya jawo muku hukunci. Amma game da sauran batutuwan, zan magance su idan na zo.