Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
12 Ina bukatar in yi taƙama. Ko da yake ba shi da amfani, amma bari in gaya muku game da wahayi da kuma ruꞌuya da Ubangiji ya nuna mini. 2 Na san wani mutum da ke da haɗin kai da Kristi, wanda shekaru goma sha huɗu da suka shige an ɗauke shi zuwa sama na uku, ko a cikin jiki ne, ko ba a cikin jiki ba, ni ban sani ba; Allah ne ya sani. 3 Hakika, na san wannan mutumin, ko a jiki ne, ko ba a jiki ba, ban sani ba; Allah ne ya sani, 4 aka ɗauke shi zuwa cikin aljanna, ya ji maganganu da ba za a iya faɗa ba, kuma bai dace mutum ya faɗe su ba. 5 Zan yi taƙama da wannan mutumin, amma ba zan yi taƙama da kaina ba, sai dai a kan abubuwan da suke nuna kasawata. 6 Ko da ina so in yi taƙama, ba zan zama wawa ba, gama zan faɗi gaskiya. Amma ba na so in yi hakan, domin kada wani ya yabe ni fiye da abin da ya gani a kaina, ko abin da ya ji daga wurina, 7 don kawai na ga ruꞌuyoyi masu ban mamaki kamar haka.
Don kada in yi taƙama fiye da yadda ya kamata, sai aka saka mini wata ƙaya a jiki, wato malaꞌikan Shaiɗan, ya yi ta mari na don kada in yi taƙama fiye da yadda ya kamata. 8 Sau uku na roƙi Ubangiji ya cire mini wannan abu daga jikina. 9 Amma ya gaya mini cewa: “Alherina ya ishe ka, domin a lokacin da ba ka da ƙarfi ne ake ganin cikakken ikona.” Saboda haka, da farin ciki zan yi taƙama da rashin ƙarfina, domin ikon Kristi ya ci-gaba da kasancewa a kaina kamar tenti.* 10 Saboda haka, ina farin ciki da rashin ƙarfina, da zage-zage da ake yi mini, da rashin abin biyan bukata, da tsanantawa, da wahaloli saboda Kristi. Domin saꞌad da nake rashin ƙarfi, a lokacin ne nake da ƙarfi.
11 Na zama wawa. Kuma ku ne kuka tilasta mini in zama haka, domin ya kamata ku yaba mini. Gama ban yi wani abu da ya nuna cewa manyan manzanninku sun fi ni a wani abu ba, ko da ni ba kome ba ne. 12 Hakika, na nuna muku alamu da suka tabbatar da cewa ni manzo ne, ta wurin jimrewa, da alamu, da kuma ayyukan ban mamaki. 13 Ta yaya na ƙaunaci sauran ikilisiyoyin fiye da ku, in ba dai yadda na ƙi in takura muku ba? Ku gafarta mini don wannan laifin da na yi muku.
14 Ga shi, wannan shi ne karo na uku da na yi shirin zuwa wurinku, kuma ba zan takura muku ba. Gama ba dukiyarku nake so ba, amma ku ne; don ba a bukatar yara su tara wa iyayensu dukiya, amma iyaye ne za su tara wa yaransu. 15 A gare ni, zan yi farin cikin yin amfani da duk abin da nake da shi, har in ba da kaina domin ku. Tun da ina ƙaunar ku sosai, ya kamata ku rage ƙaunarku a gare ni ne? 16 Duk da haka, ban takura muku ba, amma kun ce na yi muku “wayo” kuma “na yaudare ku.” 17 Na cuce ku ne ta wurin waɗanda na aika muku? 18 Na ƙarfafa Titus, kuma na aika shi tare da wani ɗanꞌuwa. Titus ya cuce ku ne? Ba manufa ɗaya muke da ita ba? Ba mun yi abubuwa a hanya ɗaya ba?
19 Ashe tun dā kuna tunanin cewa muna ƙoƙarin kāre kanmu a gabanku ne? A gaban Allah ne muke magana cikin haɗin kai da Kristi. Amma ƙaunatattuna, duk abubuwan da muke yi don mu ƙarfafa ku ne. 20 Gama ina tsoro cewa saꞌad da na zo, wataƙila ba zan same ku yadda na yi tsammani ba, kuma ni ma ba zan kasance yadda kuke tsammani ba, a maimako, mai yiwuwa in tarar kuna faɗa, da kishi, da zafin rai, da rashin haɗin kai, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da kuma rashin tsari. 21 Mai yiwuwa saꞌad da na sake dawowa, Allahna zai sa in sha kunya a gabanku, kuma wataƙila zan yi makoki a kan mutane da yawa da a dā sun yi zunubi, amma ba su tuba daga ƙazanta, da lalata,* da kuma ayyukan rashin kunya* da suka yi a dā ba.