Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
9 Ba ni da ꞌyanci ne? Ni ba manzo ba ne? Ba na ga Yesu Ubangijinmu ba? Ba ku ne aikina a cikin Ubangiji ba? 2 Ko da ni ba manzo ba ne ga wasu, hakika, ni manzo ne a gare ku! Domin ku ne hatimin da ke ba da tabbaci cewa ni manzo ne a cikin Ubangiji.
3 Ga yadda nake kāre kaina a gaban waɗanda suke yi mini bincike: 4 Muna da damar* ci da sha, ko ba haka ba? 5 Muna da ꞌyancin tafiya tare da matanmu masu bi, kamar yadda sauran manzanni da ꞌyanꞌuwan Ubangiji da Kefas* suka yi, ko ba haka ba? 6 Ko kuwa ni da Barnabas ne kawai ba mu da damar daina yin aiki don mu ciyar da kanmu? 7 Wane soja ne ke hidima da kuɗin kansa? Wane ne zai shuka inabi a gonarsa kuma ba zai ci daga ꞌyaꞌyan inabin ba? Ko wane makiyayi ne yake kiwon tumaki ba tare da ya sha madararsu ba?
8 Ina faɗin haka bisa ga raꞌayin mutum ne? Ko dai Doka* ma ba ta faɗi hakan ba? 9 Gama a rubuce yake a cikin Dokar Musa cewa: “Kada ka rufe bakin bijimi saꞌad da yake sussuka hatsi.” Bijimai ne Allah yake damuwa da su? 10 Ko dai domin mu ne ya faɗi hakan? Hakika, an rubuta wannan domin mu ne, don ya kamata mutumin da ke huɗa da kuma sussuka ya yi hakan da begen samun rabo.
11 Idan muka shuka abubuwa na ruhu a cikinku, shin wani babban abu ne idan muka girbi abubuwan da muke bukata daga wurinku? 12 Idan wasu suna da damar yin hakan, shin ba mu fi su damar yin hakan ba? Duk da haka, ba mu yi amfani da wannan damar* da muke da ita ba, amma muna jimre dukan abubuwa, don kada mu yi abin da zai hana yin shelar labari mai daɗi game da Kristi. 13 Ba ku sani ba cewa mutanen da suke ayyuka masu tsarki a haikali suna cin abinci daga haikalin, kuma waɗanda suke hidima a-kai-a-kai a bagade suna samun rabonsu daga bagaden ba? 14 Haka ma, Ubangiji ya ba da umurni cewa waɗanda suke shelar labari mai daɗi, su samu abubuwan biyan bukata ta wurin labari mai daɗi.
15 Amma ni ban yi amfani da ko ɗaya daga cikin waɗannan daman ba. Ba wai ina rubuta waɗannan abubuwan domin a yi mini hakan ba, ai gara in mutu, da a hana ni taƙama da wannan! 16 Ko da yake ina shelar labari mai daɗi, hakan ba dalilin yin taƙama ba ne a gare ni. Gama dole ne in yi wannan aikin. Kaito na, idan ban yi shelar labari mai daɗi ba! 17 Idan na yi hakan da son raina, ina da lada; ko da na yi ba da son raina ba, har ila, an ba ni riƙon amana. 18 To mene ne ladana? Ladana shi ne saꞌad da na yi shelar labari mai daɗi, in yi shi kyauta, don in guji yin amfani da ikona* na shelar labari mai daɗi a hanyar da ba ta dace ba.
19 Ko da yake na sami ꞌyanci daga dukan mutane, na mai da kaina bawa ga dukan mutane, domin in iya ceton mutane da yawa. 20 Ga Yahudawa na zama Bayahude, domin in iya jawo Yahudawa; ga waɗanda suke bin Dokar Musa, sai na zama kamar wanda yake bin dokar, ko da yake ni da kaina ba na bin dokar, na yi hakan ne don in iya jawo waɗanda suke bin dokar. 21 Ga waɗanda ba su da doka, na zama kamar ba ni da doka, ko da yake ina bin Dokar Allah kuma ina ƙarƙashin Dokar Kristi, domin in iya jawo waɗanda ba su da doka. 22 Ga marasa ƙarfi, na zama marar ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, don ko ta yaya in ceto wasu daga cikinsu. 23 Amma ina yin dukan abubuwa saboda labari mai daɗi, don in iya yin shelar sa ga wasu.
24 Ba ku san cewa dukan masu gudu a gasar tsere ne suke yin gudu, amma mutum ɗaya ne yake samun ladan ba? Saboda haka, ku yi gudu a hanyar da zai sa ku yi nasara. 25 Dukan waɗanda suke yin gasa, sukan kame kansu a cikin kowane abu. Hakika suna yin sa ne don su sami rawani da zai shuɗe, amma mu don rawanin da ba zai shuɗe ba ne. 26 Saboda haka, yadda nake gudu ba a banza ba ne; kuma yadda nake yin naushi, ina yi ne don kada in bugi iska; 27 amma ina horar da jikina kuma ina mai da shi kamar bawa, domin kada bayan na yi ma wasu waꞌazi, ni kaina a ƙi amincewa da ni.