Ta Farko Zuwa ga Korintiyawa
10 ꞌYanꞌuwana, yanzu ina so ku sani cewa kakanninmu duka sun wuce ta ƙarƙashin gajimare kuma dukansu sun bi ta cikin teku, 2 an kuma yi musu baftisma a matsayin mabiyan Musa ta wurin gajimaren da kuma tekun, 3 dukansu kuwa sun ci abinci iri ɗaya wanda Allah ya ba su 4 kuma dukansu sun sha ruwa iri ɗaya wanda Allah ya ba su. Gama sukan sha daga dutse da ke bin su wanda Allah ya ba su, kuma dutsen nan shi ne Kristi. 5 Duk da haka, Allah bai yi farin ciki da yawancinsu ba, shi ya sa ya hallaka su a daji.
6 Yanzu abubuwan nan sun zama misalai a gare mu, domin kada mu yi shaꞌawar mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi shaꞌawar su. 7 Kada mu zama masu bautar gumaka, yadda wasu cikinsu suka yi; kamar yadda yake a rubuce cewa: “Mutanen suka zauna don su ci kuma su sha. Sai suka tashi don su shaƙata.” 8 Kada mu yi lalata,* kamar yadda wasu cikinsu suka yi lalata,* har mutane dubu ashirin da uku daga cikinsu suka mutu a rana ɗaya. 9 Kada mu gwada Jehobah* kamar yadda wasu cikinsu suka gwada shi, har macizai suka kashe su. 10 Kada mu zama masu gunaguni, kamar yadda wasu cikinsu suka yi gunaguni, har mai hallaka ya hallaka su. 11 Abubuwan nan da suka faru da su misalai ne, an kuma rubuta su ne don a yi mana gargaɗi, mu da ƙarshen zamanin nan ya same mu.
12 Saboda haka, bari wanda yake tsammanin yana tsaye, ya yi hankali don kada ya faɗi. 13 Babu jarrabar da ta taɓa samun ku wadda ba ta taɓa samun mutane ba. Allah mai aminci ne, kuma ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba, amma idan an jarrabce ku, zai buɗe muku hanya don ku iya jimrewa.
14 Don haka, ku da nake ƙauna, ku guje wa bautar gumaka. 15 Ina magana da ku a matsayin waɗanda suke da fahimta; ku duba da kanku ku ga ko abin da nake faɗa gaskiya ne ko ba gaskiya ba. 16 Kofin nan na godiya da muke yin godiya don shi,* ba shi ne yake sa mu sami amfani daga jinin Kristi ba? Kuma burodin da muke kakkaryawa, ba shi ne yake sa mu sami amfani daga jikin Kristi ba? 17 Domin burodin ɗaya ne, ko da yake muna da yawa, mu jiki ɗaya ne, domin dukanmu muna ci daga burodi ɗayan.
18 Ku duba mutanen Israꞌila: Shin ba waɗanda suke ci daga hadayu da aka yi a kan bagade suna zumunci tare da Allah ba? 19 Mene ne nake nufi a nan? Abin da aka miƙa wa gunki wani abu ne, ko gunkin da kansa wani abu ne? 20 Aꞌa; amma ina cewa hadayar da alꞌummai suke yi, suna yi ne ga aljanu ba ga Allah ba; kuma ba na so ku zama waɗanda suke zumunci da aljanu. 21 Ba zai yiwu ku riƙa sha daga kofin Jehobah* kuma ku sha daga kofin aljanu ba; ba zai yiwu ku riƙa ci daga “teburin Jehobah”* kuma ku ci daga teburin aljanu ba. 22 Ko dai ‘muna ƙoƙarin sa Jehobah* kishi ne’? Ba mu fi shi ƙarfi ba, ko mun fi shi ƙarfi ne?
23 Muna da damar yin dukan abubuwan da muke so, amma ba dukan abubuwa ba ne suke da amfani. Muna da damar yin dukan abubuwan da muke so, amma ba dukan abubuwa ba ne suke ƙarfafawa. 24 Bari kowa ya ci-gaba da neman abin da zai amfane wani, ba kawai abin da zai amfane kansa ba.
25 Ku ci duk abin da ake sayarwa a kasuwan nama, kuma kada ku yi tambaya saboda lamirinku, 26 gama “duniya da dukan abubuwa da ke cikinta na Jehobah* ne.” 27 Idan marar bi ya gayyace ku kuma kuna so ku je, ku ci duk wani abin da aka sa a gabanku, kada ku yi tambaya saboda lamirinku. 28 Amma idan wani ya gaya muku cewa, “Wannan abu ne da aka miƙa a matsayin hadaya,” kada ku ci saboda wanda ya gaya muku, kuma don kada lamirin wani ya dame shi. 29 Ba na nufin lamirinku, amma lamirin mutumin. Gama me ya sa za a shariꞌanta ꞌyancina saboda lamirin wani? 30 Idan ina cin abinci da godiya, zai dace ne in ci-gaba da yin hakan idan zai sa wasu su zarge ni?
31 Don haka, ko kuna ci, ko kuna sha, ko kuna yin wani abu dabam, ku yi kome don ɗaukakar Allah. 32 Ku guji zama dalilin tuntuɓe ga Yahudawa da mutanen Girka da ikilisiyar Allah ma, 33 kamar yadda nake ƙoƙarin faranta ran dukan mutane a dukan abubuwa, ba na neman abin da zai amfane ni, amma abin da zai amfane mutane da yawa, don su iya samun ceto.