Zuwa ga Romawa
9 Ina faɗin gaskiya a cikin Kristi; ba ƙarya nake yi ba, lamirina da ruhu mai tsarki ke yi masa ja-goranci na ba da shaida, 2 cewa ina baƙin ciki sosai da kuma damuwa a zuciyata kullum. 3 Da ma a ce ni kaina an raba ni da Kristi a matsayin wanda an laꞌanta, don amfanin ꞌyanꞌuwana da dangina, 4 waɗanda Israꞌilawa ne. Allah ya mai da su ꞌyaꞌyansa, ya nuna musu ɗaukakarsa, ya yi yarjejeniya da su, ya ba su Doka* da damar yi masa hidima mai tsarki, da kuma alkawura dabam-dabam da ya yi musu. 5 Asalinsu daga kakanninmu ne, kuma daga cikinsu ne Kristi ya fito. Bari a yabi Allah wanda yake mulki a kan kome har abada. Amin.
6 Amma, hakan ba ya nufin cewa kalmar Allah ba ta cika ba. Domin ba dukan waɗanda suka fito daga zuriyar Israꞌila ne “Israꞌilawa” na gaske ba. 7 Ko da yake su daga zuriyar Ibrahim ne, ba dukansu ne yaran Ibrahim da gaske ba. A maimakon haka, Allah ya ce, “Waɗanda za a kira zuriyarka za su fito ta wurin Ishaku ne.” 8 Hakan yana nufin cewa ba dukan yaran Ibrahim ne yaran Allah na gaske ba, amma waɗanda aka haifa saboda alkawarin, su ne ainihin yaran Ibrahim. 9 Gama Allah ya yi alkawari ya ce: “A wannan lokaci shekara mai zuwa, zan zo kuma Saratu za ta haifi ɗa.” 10 Ba a lokacin kaɗai ba, ya kuma faru saꞌad da Rifkatu ta ɗauki cikin ꞌyan biyu ta wurin kakan kakanninmu Ishaku. 11 Allah ya riga ya tsai da yadda zai zaɓi mutum, kuma ba bisa ga ayyukan mutumin ba, amma Allah da kansa zai zaɓi wanda yake so ya kira. Saboda haka, tun kafin a haifi su biyun, ko kafin su yi aikin nagarta ko mugunta, 12 an gaya mata cewa: “Babban ɗan zai zama bawan ƙaramin.” 13 Kamar yadda yake a rubuce cewa: “Na ƙaunaci Yakubu, amma na tsani Isuwa.”
14 To me za mu ce ke nan? Allah yana yin rashin adalci ne? Aꞌa, ko kaɗan! 15 Gama ya gaya wa Musa cewa: “Zan nuna jinƙai ga duk wanda zan nuna wa jinƙai, kuma zan nuna tausayi ga duk wanda zan nuna wa tausayi.” 16 Saboda haka, Allah ba ya zaɓan mutum, don abin da mutumin yake so, ko kuma don ƙoƙarin mutumin, amma ya dangana ne ga jinƙan Allah. 17 A rubuce yake cewa Allah ya gaya wa Firꞌauna:* “Ga dalilin da ya sa na bar ka da rai: don in nuna ikona ta wurinka kuma in sa mutane su san sunana a faɗin duniya.” 18 Saboda haka, yana nuna jinƙai ga duk wanda yake so ya nuna wa jinƙai, amma yana barin wasu su kasance da taurin kai.
19 Don haka, za ka tambaye ni cewa: “Me ya sa har ila Allah yana ganin mutane da laifi? Wane ne zai iya hana shi cika nufinsa?” 20 Amma wane ne kai, Ya mutum, da za ka riƙa mayar wa Allah magana? Abin da aka ƙera zai ce ma wanda ya ƙera shi: “Me ya sa ka yi ni haka?” 21 Shin maginin tukwane bai da iko ya yi amfani da laka yadda yake so ne? Zai iya yin amfani da dunƙulen laka guda ya yi waɗansu tukwane don a yi aiki mai daraja da su, waɗansu kuma don aiki marar daraja. 22 Haka yake da Allah, yana so ya nuna fushinsa a kan mugayen mutane kuma ya sa a san ikonsa, duk da haka, yana haƙuri da mutanen da yake fushi da su kuma suka cancanci ya hallaka su. 23 Domin ya bayyana yalwar ɗaukakarsa ga waɗanda ya nuna musu jinƙansa, waɗanda ya shirya su tun farko su samu ɗaukaka, 24 wato mu, waɗanda ya kira, ba kawai daga tsakanin Yahudawa ba, amma daga tsakanin alꞌummai ma. 25 Kamar yadda ya faɗa a littafin Hosiya cewa: “Waɗanda ba mutanena ba, zan kira su ‘mutanena,’ kuma matar da ba na ƙaunar ta a dā, zan kira ta ‘wadda nake ƙauna’; 26 a wurin da aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ a wurin za a kira su ‘ꞌyaꞌyan Allah mai rai.’”
27 Ƙari ga haka, Ishaya ya ɗaga murya game da Israꞌila ya ce: “Ko da yake ꞌyaꞌyan Israꞌila za su yi yawa kamar yashin teku, waɗanda suka rage ne kawai za a cece su. 28 Gama Jehobah* zai shariꞌanta duniya gaba ɗaya ba tare da ɓata lokaci ba.” 29 Ƙari ga haka, kamar yadda Ishaya ya faɗa cewa: “Da a ce Jehobah* mai runduna bai bar mana wasu ꞌyaꞌya ba, da za mu zama kamar Sodom, kuma a mai da mu kamar Gomorra.”
30 To me za mu ce ke nan? Duk da cewa mutanen alꞌummai ba sa ƙoƙarin yin adalci, Allah ya ɗauke su a matsayin masu adalci don bangaskiyarsu; 31 Israꞌilawa kuma, duk da cewa suna ƙoƙarin bin dokar adalci, ba su bi dokar sosai ba. 32 Me ya sa haka? Domin suna ƙoƙarin bin dokar adalci, ba ta wurin bangaskiya ba, amma ta wurin ayyukansu. Sai suka yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe”; 33 kamar yadda yake a rubuce cewa: “Ga shi, ina sa wani dutse a Sihiyona da ke sa mutane tuntuɓe, da kuma babban dutsen da ke ɓata wa mutane rai,* amma wanda ya ba da gaskiya gare shi ba zai sha kunya ba.”