Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
5 Mun san cewa idan aka rusa gidanmu na wannan duniyar, wato wannan tentin, za mu samu gida daga wurin Allah, wato gidan da ba a gina da hannaye ba, kuma zai dawwama har abada a sama. 2 Gama a cikin gidan nan muna nishi sosai, kuma muna marmari sosai mu saka gidanmu da ke sama kamar riga, 3 domin saꞌad da muka saka shi, ba za a same mu tsirara ba. 4 Gaskiyar ita ce, mu da muke cikin wannan tentin, muna nishi, muna yawan damuwa domin ba ma so mu cire wannan, amma muna so mu saka wancan, ta hakan rai zai haɗiye jikin da ke mutuwa. 5 Yanzu wanda ya shirya mu domin wannan abin, Allah ne, shi ne kuma ya ba mu ruhu don ya zama tabbaci na abin da ke zuwa.
6 Don haka, a kullum muna da ƙarfin zuciya, domin mun san cewa yayin da muke da gidanmu a jiki, ba ma tare da Ubangiji, 7 gama muna tafiya* bisa bangaskiya ne ba bisa ga abin da muke gani ba. 8 Muna da ƙarfin zuciya kuma mun fi so mu rabu da jikin nan mu kuma kasance tare da Ubangiji. 9 Saboda haka, ko muna gida tare da shi, ko ba ma tare da shi, niyyarmu ita ce ya amince da mu. 10 Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shariꞌa na Kristi, domin kowannenmu ya karɓi ladan abubuwan da ya yi saꞌad da yake wannan jikin, ko abu mai kyau ne, ko marar kyau.
11 Saboda haka, tun da yake mun san abin da tsoron Ubangiji yake nufi, mun ci-gaba da rinjayar mutane, amma Allah ya san mu sosai. Ina fatan cewa ku ma kun san* mu sosai. 12 Ba wai muna so mu sake yabon kanmu a gabanku ba ne, amma muna ba ku dalili mai kyau ne na yin taƙama da mu, don ku iya ba da amsa ga waɗanda suke taƙama da siffarsu, ba da abin da ke cikin zuciyarsu ba. 13 Gama idan muka fita daga cikin hankalinmu, mun yi hakan don Allah ne; amma idan muna cikin hankalinmu, dominku ne. 14 Gama, ƙaunar Kristi a gare mu ce take tilasta mana, domin wannan shi ne abin da muka fahimta, cewa mutum ɗaya ya mutu don kowa; don haka kowa ya mutu. 15 Kuma ya mutu ne don kowa, don waɗanda suke raye su daina rayuwa don faranta ransu, amma don wanda ya mutu dominsu kuma aka ta da shi.
16 Daga yanzu, ba ma ganin mutum yadda ꞌyanꞌadam suke ganin sa. Ko da a dā muna ganin Kristi yadda ꞌyanꞌadam suke ganin sa, babu shakka a yanzu, ba haka muke ganin sa ba. 17 Saboda haka, idan wani yana da haɗin kai da Kristi, ya zama sabuwar halitta; abubuwa na dā sun shuɗe; ga shi! sababbin abubuwa muke da su a yanzu. 18 Amma dukan abubuwa daga wurin Allah ne, wanda ya yi sulhu tsakaninmu da shi ta wurin Kristi, kuma ya ba mu hidima ta sulhu, 19 wato, Allah yana amfani da Kristi don ya sulhunta kansa da duniya, ba ya kuma lissafta zunubansu a kansu, kuma mu ne ya ba wa saƙon sulhu tsakaninsa da mutane.
20 Don haka, mu wakilai ne a madadin Kristi, kamar dai Allah yana roƙo ne ta wurinmu. A matsayin wakilan Kristi, muna roƙo cewa: “Ku yi sulhu da Allah.” 21 Wanda bai san zunubi ba, ya mai da shi ya zama mai zunubi* dominmu, domin ta wurinsa mu zama masu yin adalci a gaban Allah.