Ta Biyu Zuwa ga Korintiyawa
4 Saboda haka, tun da yake muna da wannan hidima ta wurin jinƙan da aka nuna mana, ba za mu fid da rai ba. 2 Mun ƙi abubuwa da ke jawo kunya, abubuwan da mutane suke yi a ɓoye, ba ma yin abubuwa da wayo, ko kuma mu ɓata kalmar Allah; amma yayin da muke sa mutane su san gaskiya, muna nuna cewa muna yin abu mai kyau a gaban Allah domin lamirin kowa ya shaida hakan. 3 Idan da gaske labari mai daɗin da muke shelar sa an rufe shi da mayafi, an rufe shi ne a tsakanin waɗanda suke hallaka, 4 a tsakanin marasa bangaskiya waɗanda allah na wannan zamanin* ya makantar da zukatansu, don kada su iya ganin hasken labari mai daɗi mai ɗaukaka game da Kristi, wanda shi ne siffar Allah. 5 Gama, ba waꞌazi game da kanmu muke yi ba, amma game da Yesu Kristi a matsayin Ubangiji ne da kuma mu a matsayin bayi saboda Yesu. 6 Domin Allah ne wanda ya ce: “Bari haske ya haskaka daga cikin duhu,” kuma ya haskaka zukatanmu don ya ba su haske ta wurin ilimi mai ɗaukaka na Allah, kuma ya yi hakan ta wurin fuskar Kristi.
7 Muna da wannan dukiya a cikin tulunan ƙasa, don iko wanda ya fi na ꞌyanꞌadam ya zama na Allah, ba daga wurinmu ba. 8 Ana wahalar da mu a kowace hanya, amma hakan bai hana mu motsi ba; mun rikice, amma ba mu rasa mafita ba; 9 ana tsananta mana, amma ba a yashe mu ba; an buga mu a ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. 10 A kullum jikinmu na jimre irin wahalar da Yesu ya sha, wadda za ta iya kashe mutum, don irin rayuwar da Yesu ya yi ya nuna a jikinmu. 11 Don mu da muke rayuwa, a kullum ana sa mu fuskanci mutuwa saboda Yesu, don rayuwar Yesu ta nuna a cikin jikinmu mai mutuwa. 12 Shi ya sa muke fuskantar mutuwa, domin ku sami rai.*
13 Yanzu da yake muna da bangaskiya da ta yi daidai da wadda aka rubuta cewa: “Na ba da gaskiya, don haka na yi magana”; mu ma mun ba da gaskiya, don haka mun yi magana, 14 domin mun san cewa Wanda ya ta da Yesu zai ta da mu ma tare da Yesu, kuma zai miƙa mu tare da ku ga Yesu. 15 Gama, duk waɗannan abubuwa dominku ne, saboda alheri ya ci-gaba da ƙaruwa, don mutane da yawa suna gode wa Allah kuma ta hakan suna ɗaukaka shi.
16 Saboda haka, ba mu fid da rai ba, amma ko da jikinmu yana lalacewa, babu shakka ana sabunta zukatanmu da tunaninmu a kowace rana. 17 Ko da yake ƙuncin na ɗan lokaci ne kuma ba shi da girma, zai kawo mana ɗaukaka mai yawa da za ta wuce gaban misali kuma za ta dawwama; 18 shi ya sa ba ma zuba ido a kan abubuwan da ake gani, a maimakon haka, muna zuba ido a kan abubuwan da ba a iya gani. Gama abubuwan da ake gani na ɗan lokaci ne, amma abubuwan da ba a gani na har abada ne.