Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • dg kashi 3 pp. 4-9
  • Sashe na 3—Yadda Zamu Iya Sani Da Akwai Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sashe na 3—Yadda Zamu Iya Sani Da Akwai Allah
  • Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sararin Halitta Namu Mai-ban Tsoro
  • An Shirya Duniya Dabam
  • Ƙwayayen Naman Jiki Masu Mamaki
  • Ƙwalƙwalwanmu Mai-ban Mamaki
  • Tsarin Jini Mai-ban Girma
  • Wasu Al’ajibai
  • Maffificin Magini
  • ‘Ƙirarmu Abin Al’ajabi Ne’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
dg kashi 3 pp. 4-9

Sashe na 3—Yadda Zamu Iya Sani Da Akwai Allah

1, 2. Wane ka’ida ne ya taimake mu ga sani ko akwai Allah?

HANYA ɗaya na sani ko akwai Allah ita ce aika wannan sanannen ka’idar: Abinda aka yi duka na bukatar mai-yi. Iyakar kyaun abinda aka yi fa, haka ma ingancin wanda ya yi shi.

2 Alal misali, ka duba kewaye da gidanka. Teburai, kujaru, gadaje, tukwane, kayan tuya, farantai, da kwanukan cin abinci dukan suna bukatar mai-yi, kamar yadda yake azancen banguna, ɗabe, da silin. Duk da haka, waɗannan abubuwa suna da sauƙin yi. Da shike abubuwa masu sauƙi suna bukatar mai-yi fa, ashe ba daidai ba ne cewa abubuwa mafi-wuyan ganewa suna bukatar mai-yi mafi-fasaha?

Sararin Halitta Namu Mai-ban Tsoro

3, 4. Ina yadda sararin halitta ya taimake mu ga sanin cewa Allah ya wanzu?

3 Agogo yana bukatar mai-kera agogo. Me kuma za a ce game da tsarin su duniya namu da ke kewaye da rana mai-wuyan ganewa, da Rana da su duniya nata da ke kewaye rana waɗanda suke tafiya a kewaye da shi daidai yadda ake taƙaita su na ƙarnuka bisa ƙarnuka? Me fa za a ce game da taurari mai-ban tsoro da muke rayuwa a ciki, wanda ake ƙira shi Milky Way, wanda ke kunshe da taurarai sama da biliyan 100? Ashe ka taɓa tadda idanunka ka kalle Milky Way nan kuwa da dare? Ka burge kuwa? To sai ka yi tunanin sarari halitta mai-girma da ke ɗauke da taurarai biliyoyi barkatai kamar Milky Way namu! Hakannan ma, halittu na samaniya sun kasance daidai a tafiyarsu ƙarnuka bisa ƙarnuka da yasa an gwada su da abubuwan faɗi lokaci daidai.

4 Idan fa agogo, wanda da sauƙi yake, yana bukatar wanzuwar mai-yin agogo, lallai sarari mai-ban tsoro mai-wuyan ganewa fiye da haka yana bukatar wanzuwar mai-tsari da kuma mai-yi. Abinda yasa ke nan Littafi Mai-tsarki ya gayyace mu mu ‘tadda idanunmu sama mu kuma duba,’ sa’annan ya yi tambaya haka: “Wanene ya halicci waɗannan?” Ga amsarsa: “[Allah ne] Wanda yana kawo rundunansu bisa ga lissafinsu, yana kiransu duka da sunansu. Bisa ga girman ikonsa, domin shi mai-ƙarfi ne cikin iko, ba wanda ba shi ko ɗaya.” (Ishaya 40:26) Saboda haka, albarkacin wani iko mara-ganuwa, mai-sarrafawa, ikon azanci​—⁠Allah ne aka halicce sararin halitta.

An Shirya Duniya Dabam

5-7. Minene game da duniya sun nuna cewa tana da Mai-yinta?

5 Da ƙarin nazarin duniya da yan-kimiya suke yi, haka suke ƙara ganewa wai an shirya duniya dabam ƙwarai domin zaman yan-Adam ne. An ajiye ta da nisa yadda ya dace domin samun haske da zafi da ake bukata. Kowace shekara takan kewaye ranar sau ɗaya, da kusurwa mai-jirkitawa da ya dace kaɗai, wanda yake kawo canjin yanayi a yawancin kusurori na duniya. Duniya ma tana juyawa akan yininta kowace sa’o’i 24, wadda ke bada haske da dufu kullum. Tana da yanayi mai-haɗin iske da ta dace don mu sheƙa kuma ta tsare mu daga zafi mai-hallakaswa daga sararin sama. Tana da ruwa da ake bukata da kuma ƙasa domin noman abinci.

6 In ba tare da waɗannan abubuwa, da wasu na, yin aiki tare ba, rai ba zai yiwu ba. Ashe dukan wannan hatsari ne kawai? Science News ya ce: “Kamar dai irin yanayoyi na musamman da kuma taƙaitattun nan da ƙyar a ce sun auku babu shiri.” A’a, ba zasu iya zama haka ba. Suna kunshe da shiryawa mai-ma’ana ta wurin Mai-shiri mafi-girma.

7 Idan ka shigo cikin wani gida kuma ka iske cewa tana da abinci dayawa a shirye, kuma tana da na’uarar ɗumama yanayi da kuma na sanyayawa, tana kuma da famfo na bada isasshen ruwa, minene zaka faɗa? Wai cewa kome ya fito da kansa ne? A’a, lallai zaka tsai da cewa mutum mai-fasaha ne ya shirya kuma yi ta da kulawa sosai. An shirya duniya ma sosai da dukan abubuwa da mazaunanta suke bukata, kuma tana da wuyan ganewa fiye da wani gida da aka taɓa shiryawa sosai.

8. Minene akwai kuma cikin duniya da ya nuna kulawar Allah mai-ƙauna garemu?

8 Ka kuma yi la’akari da wasu abubuwa dayawa da suke ƙara daɗi ga rayuwa. Ka duba ire-iren furanni masu launi dabam dabam da ƙanshinsu masu daɗi da yan-Adam suke mora. Sai kuma ire-iren abinci dayawa masu daɗi domin ɗandanawarmu. Da akwai kurame, manyan duwatsu, taɓƙoƙi, da wasu halittu kuma masu kyaun kallo. Kuma, minene za a faɗa game da faɗiwar rana mai-kyaun gaske da ke ƙara ga moriyar rai? Kuma a cikin iyalan dabbobi, ashe bamu jin daɗin ganin wasan irin ƙananan karnuka, da ya’yan ƙyanwa, da kuma wasu ƙananan dabbobi? Saboda haka duniya tana kunshe da abubuwa masu marmari dayawa ba na tsare rai ne lallai ba. Wannan ya nuna cewa an shirya duniyar da kulawa mai-kyau, ana tuna da yan-Adam, ba don mu rayu kawai ba amma don mu iya moran rai.

9. Wanene ya yi duniyar, kuma don me ya yi ta?

9 Saboda haka, tsai da shawara da ya dace shine mu san da Mai-bayas da dukan waɗannan abubuwa, kamar yadda wani marubucin Littafi Mai-tsarki wanda ya gaya haka game da Jehovah Allah: “Kai ne ka yi sama da kasa.” Don minene fa? Ya bada amsar ta wurin kwatanta Allah kamar “Wanda ya halicci sammai; shi ne Allah; Mai-sifanta duniya Mai-yinta kuma; shi ya kafa ta, ya halicce ta ba wofi ba, ya kamanta ta domin wurin zama.”​—⁠Ishaya 37:16; 45:⁠18.

Ƙwayayen Naman Jiki Masu Mamaki

10, 11. Me yasa ƙwayar rai ke da ban mamaki haka?

10 Me fa za a ce game da abubuwa masu rai? Ashe basu bukatar mai-yi? Alal misali, ka yi la’akari da fasali mai-ban mamaki na ƙwayaye masu-rai. A cikin littafinsa Evolution: A Theory in Crisis, mai koya lafiyar jijiyoyin jiki Michael Denton ya furta haka: “Ko ƙananan abubuwa masu-rayuwa a duniya yau, kamar ƙwayayen bacteria, abubuwa masu-wuyan ganewa ne ƙwarai. Ko da shike ƙanƙanin ƙwayoyin bacteria ɗan tikil suke, . . . kowane ɗaya daga cikinsu ƙanƙanin ma’aikata ne da ke kunshe da dubban kashi-kashin inji na cikin jiki da aka ƙera . . . yana da wuyan ganewa fiye da wani inji da mutum ya taɓa ginawa kuma babu makamancinsa cikin tarin abubuwa marasa rai.”

11 Game da tsarin ƙwayaye cikin kowace ƙwayar rai kuwa, ya ce: “Iya riƙe saƙo na ƙwayar DNA yana da girma fiye da wani na’ura da aka taɓa sani; da gwani yake har da dukan saƙo da ake so don sanin rai kamar mutum mai-wuyan ganewa nauyinsa kamar yar ƙwaro ce kawai. . . . Azancen bayanawar abubuwa sarai da na wuyan ganewa da injin ƙwaron rai ke yi, [na’urarmu] mai-girma da muka yi ya zama banza. Muna kuwa jin kunya haka.”

12. Minene wani ɗan kimiya ya faɗa game da tushin ƙwayar rai?

12 Denton ya daɗa haka: “Wuyar ganewa na irin ƙanƙanin ƙwayar ran nan yana da girma ainun da yana da wuya a amince da shi cewa irin abin nan ya auku farat ɗaya ne, wanda ba a tsammance shi ba, ya fito hakanan kawai.” Lallai yana da mai-zanata da kuma mai-yinta.

Ƙwalƙwalwanmu Mai-ban Mamaki

13, 14. Me yasa ƙwalƙwalwa ya fi ƙwayar rai ban mamaki?

13 Wannan mai-ilimin kimiyar ya kuma ce: “Azancen abu mai-wuyan ganewa fa, ƙwayar rai guda ba wani abu ba ne yayinda aka gwada shi da ƙwalƙwalwan halitta mai-rai irin ta mutum. Ƙwalƙwalwan yan-Adam yana kunshe da ƙwayoyin ɗaukan saƙo miliyan dubu goma. Kowace ƙwayar ɗaukan saƙo tana zuba jijiyoyin kwashe saƙo tsakanin kusurori dubu goma da kuma dubu ɗari ɗaya na waɗanda ta ke sadarwa da wasu ƙwayoyin rai na ƙwalƙwalwan. Dukan mahadin sadarwa cikin ƙwalƙwalwan mutum yana kusan . . . miliyan miliyan dubu.”

14 Denton ya ci gaba da haka: “Ko da ɗaya ne daga cikin tsari dari na mahadin ƙwalƙwalwan aka shirya sosai fa, wannan har ila zai kasance kamar tsari da ke kunshe da mahadi na musamman ne fiye da dukan na’urar sadarwa a cikin dukan Duniya.” Sa’annan kuma ya tambaya: “Anya da wani irin shiri na barkatai ya iya shirya irin tsarin nan?” Hakika fa, amsar a’a ne. Lallai ƙwalƙwalwan yana da Mai-shiryawa da kuma Mai-yi mai kulawa.

15. Minene wasu suka faɗi game da ƙwalƙwalwa?

15 Ƙwalƙwalwan yan-Adam ma yana maida inji inji masu ƙwalƙwalwa masu-girma ƙwarai su kasance abinda ba inganta yinsa ba. Marubucin Kimiya Morton Hunt ya ce: “Azantanmu masu-aiki suna riƙe da saƙoni dayawa fiye da wata babbar inji mai ƙwalƙwalwa na zamani mai-bincike sau biliyan.” Saboda haka, likitan ƙwalƙwalwa Dr. Robert J. White ya kamala da cewa: “Ba ni da wani zaɓe sai dai in yarda da wanzuwan wani Mai-fasaha Mafi-girma duka, wanda shine ya shirya da kuma gina irin dangantaka da ke tsakanin azanci da ƙwalƙwalwa​—⁠abinda ya zarce ganewar mutum. . . . Dole in gaskata cewa dukan waɗannan suna da somawa mai-basira, cewa Wani ne ya yi su.” Lallai ne ya zama Wani mai-kulawa.

Tsarin Jini Mai-ban Girma

16-18. (a) A waɗanne hanyoyi ne tsarin jini da ban girma yake ƙwarai? (b) Ga wane tsai da shawara ne ya kamata mu kai?

16 Ka yi la’akari, kuma, da tsarin jini mai-ban girma wanda ke ɗaukan abubuwan gina jiki da iskar oxygen da kuma yin ƙariya daga kamuwa da cuta. Game da jan kwayoyin rai na jini, sashe na musamman na tsarin fa, littafin nan ABC’s of the Human Body ya ce: “Digon jini guda yana kunshe da ƙwayoyin rai dabam dabam miliyan 250 . . . Jiki yana kunshe da misalin biliyoyi 25 nasu, idan aka baza su kuwa zasu rufe, filin ƙwallon tanas hudu. . . . Da akwai sākewa da ke aukuwa, wajen miliyan 3 na kwayoyin jini a kowace daƙiƙa guda.”

17 Game da ƙwayoyin rai na farin jini, wata sashen tsarin jini mai-ban girma, tushen har ila ya gaya mana: “Yayinda irin ƙwayar rai na jan jini daya ne kaɗai, kwayoyin rai na farin jini suna da ire-irensu dayawa, kowane iri tana iya yin yaƙi da jikin ke yi a hanyoyi dabam dabam. Alal misali, wata iri, tana hallakas da ƙwayoyin rai da suka mutu. Wasu kuma suna haifad da rigakafi da ke yaƙe cututtuka, kawas da cutan wasu bakin abubuwa cikin jikin, ko kuwa a zahiri dai ci su bacteria ko kuwa nika su.”

18 Duba fa tsari mai-ban mamaki da shiryayye kuma! Lallai fa kowane abu da aka shirya shi sosai haka kuma yana ƙariya saboda haka tilas ya zama da mai-shiryawa mai-fasaha da kuma mai kulawa​—⁠Allah.

Wasu Al’ajibai

19. Ina yadda idanu yake yayinda aka gwada da na’urori yin mutum?

19 Da akwai wasu al’ajibai dayawa a cikin jikin yan-Adam. Daya daga cikinsu shine idanu, da aka shirya shi sosai har babu wata kamara da zata yi kusa da shi. Mai-ilimin taurari Robert Jastrow ya ce: “Kamar dai an shirya idanun ne; babu wani mai-ƙera dogon madubi mai kawo nesa kusa da ya iya yin wani abu mafi wannan.” Kuma littafin nan Popular Photography ya labarta: “Idanun yan-Adam suna ganin wuri mai-nesa sarai fiye da wanda fim ke yi. Suna gani cikin maunan wurare uku, a kusurwa mai-fadin gaske, ba tare da wani birkicewa ba, cikin tafiya babu fashi . . . Gwadawar idanun yan-Adam da kamara ba kwatanci da ya dace ba ne. Idanun yan-Adam kama yake da na’ura da ya zarce inji mai-ƙwalƙwalwa mai-azanci na ƙwarai mai-basira, mai-ingancin karɓan saƙoni, sauri, da shirin aiki da suke fiye da wani na’ura yin mutum, ko inji mai-ƙwalƙwalwa ko kuwa kamara.”

20. Minene wasu fasalolin jikin yan-Adam masu-ban al’ajibi?

20 Ka kuma, yi tunani, game da hanyar da dukan wasu ɓangarorin jiki suke aiki a haɗe ba tare da wani ƙoƙarin kanmu ba. Alal misali, muna ci ire-iren abinci da kuma abin sha cikin cikinmu, duk da haka jikin yakan niƙa su kuma haifad da karfi. Ka gwada hada irin abubuwa dabam dabam nan cikin tankin gas na mota kuma ka ga iyakar yadda zai zama! Akwai kuma mu’ujizan haifuwa, haifuwar jariri rayayye​—⁠makamanin iyayensa​—⁠a cikin watanni tara kawai. Me kuma zaka ce game da ingancin jaririn na koya yadda zaya yi magana a harshe mai-wuyan ganewa cikin yan shekaru kawai?

21. Bayan yin la’akari da al’ajibai na jiki, minene mutane masu azanci suka ce?

21 I fa, abubuwa masu ban-al’ajibi, halittu masu ban-mamaki cikin jikin yan-Adam yana cika mu da tsoro. Babu wani injiniya da zai iya yin kamanin waɗannan abubuwa. Anya su ayukan tsautsayi ne kawai? Lallai babu. Maimakon haka, yayinda suka yi la’akari da fasaloli masu ban-al’ajibi na jikin yan-Adam, mutane masu-azanci sukan faɗi, kamar mai-zabura da ya ce: “Zan yi godiya gareka [Allah]; gama ƙirata abin ban tsoro ce, abin al’ajibi ce kuwa. Ayukan ka suna da ban al’ajibi.”​—⁠Zabura 139:⁠14.

Maffificin Magini

22, 23. (a) Me yasa ya kamata mu yarda da wanzuwar Mahalicci? (b) Minene Littafi Mai-tsarki ya faɗi daidai game da Allah?

22 Littafi Mai-tsarki ya ce: “Gama kowane gida akwai mai-gininsa; amma Allah ne ya gina kome da ke wanzuwa.” (Ibraniyawa 3:⁠4, The Jerusalem Bible) Tun da shike kowane gida, ko ƙaƙa sauƙin gininsa, dole yana da magini, lallai fa sararin halitta mai-girma tare da ire-iren rayuka dayawa da suke bisa duniya, tilas suna da magininsu. Kuma da shike mun yarda da wanzuwar yan-Adam waɗanda suka ƙera na’urori kamar jiragen sama, su telebijin, da kuma injina masu ƙwalƙwalwa, ashe bai kamata mu yarda da wanzuwar Wani wanda ya ba yan-Adam ƙwalƙwalwa na yin irin abubuwan nan ba?

23 Littafi Mai-tsarki fa ya yi haka, yana kira shi “Allah na gaskiya, Jehovah, . . . Shi wanda ya halicci sammai, Ya miƙa su; shi Wanda ya shimfiɗa ƙasa, da abinda ke tsirowa a cikinta; Wanda ke bada lumfashi ga mutanen da ke kanta.” (Ishaya 42:⁠5) Daidai ne fa Littafi Mai-tsarki ya sanas: “Kai ne mai-isa, Jehovah, Allahnmu kuma, ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, saboda kai ka halicci dukan abu, domin nufinka kuma suka kasance kuma suka halittu.”​—⁠Ru’ya ta Yohanna 4:⁠11, NW.

24. Ina yadda zamu sani da akwai Allah?

24 I fa, zamu iya sani cewa da akwai Allah ta wurin abubuwa da ya yi. “Gama tun halittar duniya al’amuran [Allah] da basu ganuwa, watau ikonsa madawwami da Allahntakassa, a sarari ake ganinsu; ta wurin abubuwa da [Allah ya] halitta.”​—⁠Romawa 1:⁠20.

25, 26. Me yasa yin banza da wani abu bai yarda da cewa babu wanda ya yi shi ba?

25 Don wai an yi banza da wani abinda aka yi bai nufa cewa babu wani da ya yi abin. Za a iya amfani da jirgin sama domin dalili mai-kyau, kamar na’urar tafiya na sama. Amma za a iya amfani da shi don hallakaswa, kamar abin jefa bom. Yin amfani da shi don hallakaswa bai nufa cewa ba wani ne ya yi shi ba.

26 A makamancin hali fa, wai cewa yan-Adam sau dayawa sun juya ga yin mugunta bai nufa cewa basu da Wanda ya yi su ba, wai cewa babu Allah ba. Shi yasa, Littafi Mai-tsarki ya lura daidai haka: “Ga shiriritarku! Maginin tukwane za a gan shi daidai da ƙasa; har abinda aka yi zaya ce ma wanda ya yi shi, baya yi shi ba; ko kuwa abinda aka sifanta shi ce ma wanda ya sifanta shi, ba shi da fahimi?”​—⁠Ishaya 29:⁠16.

27. Me yasa zamu zace Allah ya amsa tambayoyinmu game da shan wahala?

27 Mahaliccin ya nuna hikimarsa ko ta wurin abubuwa da ya yi masu ban al’ajibi masu-wuyan ganewa. Ya nuna ko cewa yana kulawa da mu sarai ta wurin yin duniyar daidai wurin zama, da yin jikunanmu da azantanmu a hanya mai-ban al’ajibi, kuma ta wurin yin abubuwa masu kyau dayawa garemu don mu mora. Lallai zaya nuna makamancin hikima da kulawa ta wurin bada amsoshi ga tambayoyi kamar su: Me yasa Allah ya kyale shan wahala? Minene zaya yi game da shi?

[Hoto a shafi na na 5]

Duniya, da yanayin ƙāriya nata, gida ne na musamman da Allah mai kulawa ya shirya garemu

[Hoto a shafi na na 6]

An yi duniya da kulawa na musamman domin more rai sarai

[Hoto a shafi na 7]

‘Ƙwalƙwalwa ɗaya yana kunshe da haɗin dukan na’urorin sadarwa a bisa Duniya.’​—⁠Bisa ga Mai-ilimin abubuwa masu rai ƙanana

[Hoto a shafi na na 8]

“Kamar dai an shirya idanu ne lallai; babu wani mai-shirya madubi mai-kawo nesa kusa da zai shirya wani abu fiye da wannan.”​—⁠Bisa ga Mai-ilimin taurari

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba