Darasi na 3
Wanene Yesu Kristi?
Me yasa ake kiran Yesu Ɗan “fari” na Allah? (1)
Me yasa ake kiran sa “Kalman”? (1)
Me yasa Yesu ya zo duniya kamar mutum? (2-4)
Me yasa ya tafiyadda mu’ujizai? (5)
Minene Yesu zai yi nan gaba kurkusa? (6)
1. Yesu ya rayu a sama kamar ruhu kafin ya zo duniya. Shi ne halittar Allah na fari, kuma don haka ake kiransa Ɗan “fari” na Allah. (Kolossiyawa 1:15; Ru’ya ta Yohanna 3:14) Yesu kaɗai ne Ɗan da Allah ya halitta da kansa. Jehovah ya yi amfani da Yesu kafin ya zama mutum kamar “gwanin mai-aikinsa” don halittar dukan sauran abubuwa da ke sama da kuma duniya. (Misalai 8:22-31; Kolossiyawa 1:16, 17) Allah ya yi amfani da shi ma kamar wakilinsa mai-girma. Shi ya sa aka kira Yesu “Kalman.”—Yohanna 1:1-3; Ru’ya ta Yohanna 19:13.
2. Allah ya aiko da Ɗansa zuwa duniya ta wurin ƙaurad da ransa zuwa mahaifar Maryamu. Saboda haka Yesu ba shi da uba ɗan-Adam. Shi ya sa bai gāji zunubi ko rashin kamilci ba. Allah ya aiko Yesu zuwa duniya don dalilai uku: (1) Don ya koya mana gaskiya game da Allah (Yohanna 18:37), (2) don ya riƙe kamala na sarai, yana tanadar mana (1 Bitrus 2:21), da kuma (3) don ya saɗaukar da ransa don yantar da mu daga zunubi da mutuwa. Me yasa ake bukatar haka?—Matta 20:28.
3. Ta wurin rashin biyyaya ga dokar Allah, mutum na farko, Adamu, ya aika abinda Littafi Mai-Tsarki ya kira “zunubi.” Don haka Allah ya hukunta shi ga mutuwa. (Farawa 3:17-19) Bai dace da mizanan Allah kuma ba, saboda haka shi ba kamili ne kuma ba. Da sannu sannu ya tsufa kuma mutu. Adamu ya haye zunubi akan dukan yaransa. Shi yasa mukan tsufa, yi ciwo, kuma mutu. Ina yadda za a cetas da mutane?—Romawa 3:23; 5:12.
4. Yesu kamiltaccen mutum ne kamar Adamu. Amma dai, ba kamar Adamu ba fa, Yesu ya yi biyyaya ga Allah sarai har ma a ƙarƙashin gwadi mafi-girma. Wannan ya na nufin cewa zai iya saɗaukas da kamiltaccen ransa na mutum don biyan zunubin Adamu. Abinda Littafi Mai-Tsarki ya kira “fansa” kenan. Da haka za a iya kwance ’ya’yan Adamu daga hukuncin mutuwa. Dukan waɗanda suke bada gaskiya cikin Yesu za a gafarta masu zunubansu kuma su sami rai na har abada.—1 Timothawus 2:5, 6; Yohanna 3:16; Romawa 5:18, 19.
5. Yayinda Yesu ke duniya ya warkas da marasa-lafiya, ciyyad da masu-yunwa, da kuma tsayad da wani guguwa. Har ma ya tadda matattu. Me yasa ya tafiyadda mu’ujizai? (1) Ya ji tausayin mutane masu shan wahala, kuma ya so ya taimake su. (2) Mu’ujizansa sun tabbatas cewa shi Ɗan Allah ne. (3) Sun nuna abinda zai yi ma mutane masu biyyaya yayinda zai yi mulki kamar Sarki a duniya.—Matta 14:14; Markus 2:10-12; Yohanna 5:28, 29.
6. Yesu ya mutu kuma Allah ya tashe shi kamar halittar ruhu, kuma ya koma sama. (1 Bitrus 3:18) Tun lokacin, Allah ya maida shi Sarki. Bada daɗewa ba Yesu zai cire dukan mugunta da wahala daga duniyar nan.—Zabura 37:9-11; Misalai 2:21, 22.
[Hotuna a shafi na 7]
Hidimar Yesu yana kunshe da koyaswa, tafiyad da mu’ujizai, har ma da bada ransa domin mu