Darasi na 8
Rayuwar Iyali da ke Gamshe Allah
Minene matsayin miji cikin iyali? (1)
Ina yadda ya kamata miji ya bi da matarsa? (2)
Wane nawaya ne uba ke da shi? (3)
Minene aikin matar cikin iyali? (4)
Minene Allah ke bukata daga wurin iyaye da kuma yara? (5)
Minene ra’ayin Littafi Mai-Tsarki game da rabuwa da kisan aure? (6, 7)
1. Littafi Mai-Tsarki ya ce miji shi ne kan iyalinsa. (1 Korinthiyawa 11:3) Mace ɗaya kaɗai ne miji zai aura. Su yi aure daidai bisa doka.—1 Timothawus 3:2; Titus 3:1.
2. Ya kamata mai-gida shi ƙaunaci matarsa kamar yadda ya ke ƙaunar kansa. Sai ya bi da ita kamar yadda Yesu ya bi da mabiyansa. (Afisawa 5:25, 28, 29) Kada ya bugi matarsa ko kuwa wulakantar da ita a wata hanya sam. Maimako fa, sai dai ya girmama da kuma daraja ta.—Kolossiyawa 3:19; 1 Bitrus 3:7.
3. Ya kamata uba ya yi aiki sosai domin ya kula da iyalinsa. Tilas ya tanadar da abinci, sutura, da gida ma matarsa da yaransa. Tilas ne ma uba ya yi tanadin ruhaniyar iyalinsa. (1 Timothawus 5:8) Shi ya ke jagora wajen taimaka ma iyalinsa yin koyo game da Allah da nufe-nufensa.—Kubawar Shari’a 6:4-9; Afisawa 6:4.
4. Ya kamata mace ta zama mataimakiya na ƙwarai ga mijinta. (Farawa 2:18) Zata taimaki mijinta koyas da kuma fahintar da yaransu. (Misalai 1:8) Jehovah ya bukaci mace ta kula da iyalinta cikin ƙauna. (Misalai 31:10, 15, 26, 27; Titus 2:4, 5) Ta kasance da ladabi mai-zurfi ga mijinta.—Afisawa 5:22, 23, 33.
5. Allah ya bukaci yara su yi biyayya ga iyayensu. (Afisawa 6:1-3) Yana tammaha iyaye su galgaɗas da kuma gyara yaransu. Iyaye na bukatar ɓadda lokaci da yaransu su kuma yi nazarin Littafi Mai-Tsarki da su, suna biyan bukatunsu na ruhaniya da jiye-jiye. (Kubawar Shari’a 11:18, 19; Misalai 22:6, 15) Kada iyaye su hore yaransu cikin zalunci ko rashin tausayi.—Kolossiyawa 3:21.
6. Sa’anda abokan aure ke da matsaloli na zama tare, sai su aika galgaɗin Littafi Mai-Tsarki. Littafi Mai-Tsarki ya aririce mu mu nuna ƙauna da kuma gafartawa. (Kolossiyawa 3:12-14) Kalmar Allah bata goyi bayan rabuwa kamar hanyar warware ƙananan matsaloli ba. Amma mace zata iya barin mijinta idan (1) da taurin kai ya ƙi lura da iyalinsa, (2) idan yana nuna ƙarfi sosai da har lafiyar ta da ranta na cikin haɗari, ko kuwa (3) idan hamayyarsa ya kai ga hana ta yin sujada ga Jehovah.—1 Korinthiyawa 7:12, 13.
7. Tilas ne abokan aure su nuna aminci ga juna. Zina zunubi ne ga Allah da kuma abokin aure. (Ibraniyawa 13:4) Jima’i waje da aure ne kaɗai dalili na Nassi don ya kashe aure ga abokin aurensa kuma zama da izinin sake aure. (Matta 19:6-9; Romawa 7:2, 3) Jehovah baya son mutane su yi kisan aure ba tare da wani dalili na Nassi ba kuma su sake aure.—Malachi 2:14-16.
[Hotuna a shafi na 16 da 17]
Allah yana tammaha iyaye su galgaɗe yaransu da kuma gyara su
[Hoto a shafi na 17]
Uba mai-ƙauna yana tanadin bukatun abubuwan jiki da na ruhaniya ga iyalinsa