Tambayoyi da Mutane da Suke da Marmari Suke Yi Sau da Yawa
Idan Allah ƙauna ne, me ya sa ya ƙyale mugunta?
ALLAH ya ƙyale mugunta, miliyoyin mutane kuma a duniya suna yinta. Alal misali, suna yaƙe-yaƙe, jefa wa yara bom, ɓata duniya, kuma suna haddasa yunwa. Miliyoyi suna shan taba su kamu da ciwon huhu, suna zina su ɗauki cututtuka da ake ɗauka ta jima’i, suna shan giya da yawa kuma su kamu da kumburin hanta, da sauransu. Irin waɗannan mutane ba sa son mugunta ta ƙare. Suna son a kawar da wahala da take kawowa ne kawai. Yayin da suka girbe abin da suka shuka, sai su yi kuka, “Me ya sa ya faɗo mini?” Sai su ɗaura wa Allah laifi, yadda Misalai 19:3 ta ce: “Wautar ɗan Adam ta kan ɓata rayuwarsa: Sai ya yi gunaguni wa UBANGIJI.” (The New English Bible) Idan Allah ya hana mugunta da suke yi, za su nuna rashin amincewarsu don ba su da damar yin ta!
Dalili na musamman da ya sa Jehovah ya ƙyale mugunta shi ne don ya amsa tuhumar Shaiɗan. Shaiɗan Iblis ya ce Allah ba zai samu mutane a duniya da ke bauta masa da gaskiya ba idan sun fuskanci gwaji. (Ayuba 1:6-12; 2:1-10) Jehovah ya ƙyale Shaiɗan ya zauna ya samu zarafi ya nuna zargi da ya yi. (Fitowa 9:16) Shaiɗan ya ci gaba da sa mutane wahala yanzu, don ya juya su daga Allah, yayin da yake ƙoƙari ya tabbatar da tuhumarsa. (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Amma dai, Ayuba ya tsaya da ƙarfi. Yesu ma ya yi haka. Kiristoci na gaskiya suna yin haka yanzu.—Ayuba 27:5; 31:6; Matta 4:1-11; 1 Bitrus 1:6, 7.
Zan so na gaskata da aljanna ta duniya inda mutane za su zauna har abada, amma wannan zai yiwu?
Ba bisa Littafi Mai Tsarki ba. Kamar abin da ba zai yiwu ba domin mutane suna yin mugunta ƙarnuka da yawa yanzu. Jehovah ya halicce duniya kuma ya gaya wa mutane su cika ta da maza da mata masu adalci da za su kula da tsiro da dabbobi kuma su adana kyanta maimakon halaka ta. (Duba shafi na 12 da na 17.) Maimakon a ce Aljanna da aka yi alkawarinta ba za ta yiwu ba, yanayin baƙin ciki na yanzu ne ba zai ci gaba ba. Aljanna za ta canje shi.
Ta yaya zan amsa wa mutane da suke ba’a da suke cewa Littafi Mai Tsarki ƙage ne kuma bai jitu da kimiyya ba?
Ba da gaskiya cikin waɗannan alkawura ba batun yarda ba ne kawai. “Bangaskiya fa daga wurin ji ne.” Ta wurin nazarin Kalmar Allah, hikima da ke ciki za ta bayyana kuma bangaskiya za ta ƙaru.—Romawa 10:17; Ibraniyawa 11:1.
Abin da aka tono daga ƙasa na Littafi Mai Tsarki ya tabbatar cewa tarihi na Littafi Mai Tsarki daidai ne. Kimiyya na gaskiya ta jitu da Littafi Mai Tsarki. Aukuwa na biye suna cikin Littafi Mai Tsarki tun dā kafin manazarta suka gano su: Yadda aka yi duniya har ta wanzu, cewa duniya tana kama da ƙwallo, ba a rataye take a kan kome ba, da kuma cewa tsuntsaye suna ƙaura.—Farawa sura ta 1; Ishaya 40:22; Ayuba 26:7; Irmiya 8:7.
Annabce-annabce da sun cika sun nuna cewa Littafi Mai Tsarki hurarre ne. Daniel ya annabta tun kafin lokaci cewa masu mulki za su tashi kuma su faɗi, da kuma lokacin da Almasihu zai zo a kuma kashe shi. (Daniel, surori 2, 8; 9:24-27) Har ila yau, wasu annabce-annabce suna cika, da ke nuna cewa waɗannan “kwanaki na ƙarshe” ne. (2 Timothawus 3:1-5; Matta, sura 24) Mutane ba su da ikon sanin abin da zai faru a gaba. (Ishaya 41:23) Don ƙarin bayani duba littattafan nan The Bible—God’s Word or Man’s? da kuma Is There a Creator Who Cares About You?, Watchtower Bible and Tract Society ne suka buga.
Ta yaya zan koyi yadda zan amsa tambayoyi na Littafi Mai Tsarki?
Dole ne ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ka yi bimbini a kai, kuma ka roƙi ruhun Allah ya ja-gorance ka. (Misalai 15:28; Luka 11:9-13) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Amma idan kowane a cikinku ya rasa hikima, bari shi yi roƙo ga Allah, wanda ya ke bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi.” (Yaƙub 1:5) Akwai littattafan nazarin Littafi Mai Tsarki da suke da amfani idan an bincika su. Yadda take, ana bukatar taimako daga wasu, kamar yadda Filibbus ya yi nazari da Bakushi. (Ayukan Manzanni 8:26-35) Shaidun Jehovah suna tafiyar da nazarorin Littafi Mai Tsarki kyauta da mutane da suka nuna suna so a gidajensu. Ka kasance a sake ka gaya musu su yi nazari da kai.
Me ya sa mutane da yawa suke hamayya da Shaidun Jehovah kuma suke gaya mini kada na yi nazari da su?
An yi hamayya da wa’azin Yesu, kuma ya ce za a yi hamayya da mabiyansa. Sa’anda wasu koyarwar Yesu ta burge su, ’yan hamayya na addini suka ce: “Har ku ma kun ɓata? A cikin hakimai, ko cikin Farisawa, akwai waɗanda sun bada gaskiya gareshi?” (Yohanna 7:46-48; 15:20) Mutane da za su shawarce ka kada ka yi nazari da Shaidu idan ba jahilai ba ne to maƙiya ne. Ka yi nazari da Shaidu ka gani da kanka ko iliminka na Littafi Mai Tsarki zai ƙaru ko babu.—Matta 7:17-20.
Me ya sa Shaidun suke ziyarar mutane da suke da nasu addini?
A yin haka suna bin misalin Yesu. Ya je wurin Yahudawa. Yahudawa suna da nasu addini, amma a hanyoyi da yawa sun kauce wa Kalmar Allah. (Matta 15:1-9) Dukan al’ummai suna da addinai, ko waɗanda suke da’awar su Kirista ne ko kuma waɗanda ba Kirista ba. Yana da muhimmanci mutane su riƙe imani da ya jitu da Kalmar Allah, ƙoƙarce-ƙoƙarcen Shaidun su taimaka musu su yi hakan ya nuna suna ƙaunar maƙwabcinsu.
Shaidun sun gaskata cewa addininsu ne kaɗai daidai?
Duk wanda ya ɗauka addininsa da muhimmanci zai yi tunanin cewa addininsa daidai ne. In ba haka ba, me ya sa shi ko ita za ta ko za ya duƙufa a yin sa? An gargaɗi Kiristoci: “Ku auna abu duka; ku riƙe mai-kyau.” (1 Tassalunikawa 5:21) Ya kamata mutum ya tabbata cewa imaninsa yana da asali daga Nassi, domin imani ɗaya ne, gaskiya kuma ɗaya ce. Afisawa 4:5 ta tabbatar da wannan, tana cewa “Ubangiji ɗaya, imani ɗaya, baftisma ɗaya.” Yesu bai yarda da ra’ayin zamani ba, cewa da akwai hanyoyi da yawa, addinai da yawa da duk suna kai wa ga ceto. Maimakon haka ya ce: “Ƙofa ƙunƙunta ce, hanya kuwa matsatsiya, wadda ta nufa wajen rai, masu samunta fa kaɗan ne.” Shaidun Jehovah sun gaskata cewa sun same ta. In ba haka ba, za su nemi wani addini.—Matta 7:14.
Sun gaskata cewa su kaɗai ne za su sami ceto?
A’a. Miliyoyin mutane da sun rayu ƙarnuka da suka shige da ba Shaidun Jehovah ba ne za su dawo a tashin matattu su sami zarafin rayuwa. Mutane da yawa da suke rayuwa yanzu za su iya karɓan gaskiya da kuma adalci kafin “ƙunci mai-girma,” kuma za su sami ceto. Ƙari ga haka, Yesu ya ce bai kamata muna shar’anta juna ba. Mu muna ganin waje ne; Allah yana ganin zuciya. Yana gani daidai kuma yana shar’anta da juyayi. Ya bayar da shari’a ga Yesu ne, ba mu ba.—Matta 7:1-5; 24:21; 25:31.
Wace irin kyauta ce ake bukata daga waɗanda suke halarar taron Shaidun Jehovah su bayar?
Game da ba da kyautar kuɗi, manzo Bulus ya ce: “Kowane mutum shi aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” (2 Korinthiyawa 9:7) A Majami’un Mulki da wuraren manyan taro na Shaidun Jehovah, ba a karɓan kuɗi. An ajiye asusu don wanda yake so ya saka abu, ya yi haka. Ba wanda yake sanin abin da ko idan wasu suka ba da. Wasu suna ba da abu fiye da wasu; wasu kuma ba sa iya ba da kome. Yesu ya nuna ra’ayin da ya kamata a kasance da shi lokacin da ya yi maganar asusu a haikali cikin Urushalima da waɗanda suke ba da kyauta: Abin da mutum zai iya ba da ne, ta halin bayarwa ke da muhimmanci, ba abin da aka bayar ba.—Luka 21:1-4.
Idan na zama ɗaya cikin Shaidun Jehovah, za a bukaci na yi wa’azi yadda suke yi?
Yayin da mutum ya sami cikakken sani na Aljanna ta duniya da aka yi alkawarinta a ƙarƙashin Mulkin Kristi, zai so ya gaya wa wasu. Kai ma za ka yi haka. Bishara ce!—Ayukan Manzanni 5:41, 42.
Yin haka hanya ce da ta fi muhimmanci a nuna cewa kai almajirin Yesu Kristi ne. A cikin Littafi Mai Tsarki, an kira Yesu “amintaccen mashaidi mai-gaskiya.” Lokacin da yake duniya ya yi wa’azi, yana cewa: “Mulkin sama ya kusa,” sai ya aika almajiransa su yi haka. (Ru’ya ta Yohanna 3:14; Matta 4:17; 10:7) Daga baya Yesu ya umurce mabiyansa: “Ku tafi fa, ku almajirantarda dukan al’ummai, . . . kuna koya masu.” Ya kuma annabta cewa kafin ƙarshe, “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai.”—Matta 24:14; 28:19, 20.
Akwai hanyoyi da yawa na yin wannan shelar bishara. Zance da abokane da idon sani sau da yawa yana buɗe hanyar yin haka. Wasu suna yin sa ta rubuta wasiƙu ko kuma yin amfani da tarho. Wasu suna aika wa wani idon sani littattafai da suke ɗauke da abubuwa da suke zaton zai so. Don kada su bar kowa a baya, Shaidu suna zuwa ƙofa zuwa ƙofa da saƙon.
Littafi Mai Tsarki na ɗauke da wannan gayyatar: “Ruhu da amarya suna cewa, Zo Mai-ji kuma, bari shi ce, Zo. Mai-jin ƙishi kuma, bari shi zo: wanda ya ke so, bari shi ɗiba ruwa na rai kyauta.” (Ru’ya ta Yohanna 22:17) Ya kamata a gaya wa wasu game da Aljanna ta duniya da albarkarta da yardan rai, daga zuciya da ke cike da sha’awa na gaya wa wasu bishara.
Mun tabbata kana da wasu tambayoyi game da Shaidun Jehovah da imaninsu. Wataƙila wasu al’amura suna da wuyan ganewa. Za mu so mu amsa tambayoyinka. Ba mu da waje a cikin wannan mujalla, saboda haka muna gayyatarka ka tambayi Shaidun. Za ka iya yin haka a taronsu a Majami’ar Mulki ko kuma lokacin da suka zo gidanka. Ko kuma ka aiko da tambayoyinka zuwa Watch Tower, ka yi amfani da adireshi da ya dace na ƙasa.