Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • cl babi na 6 pp. 57-66
  • Ikon Halaka—Jehobah, “Gwanin Yaki Ne”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ikon Halaka—Jehobah, “Gwanin Yaki Ne”
  • Ka Kusaci Jehobah
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yaƙe-Yaƙe na Allah da Kuma na Mutane
  • Abin da Yake Tilasta wa Allah na Salama Ya Yi Yaƙi
  • Allah Ya Aikata don Ya Kawar da Mugunta
  • Yaƙi Domin Sunansa
  • Yaƙi Domin Mutanensa
  • Ka Matso Kusa da “Gwanin Yaƙi”
  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Allah Yana da Suna
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Maganar Jehobah Tana Cika A Kullayaumi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Abin da Muka Koya Daga Ƙyale Mugunta da Allah Ya Yi
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Dubi Ƙari
Ka Kusaci Jehobah
cl babi na 6 pp. 57-66
Fir’auna da sojojin Masar sun mutu a Jar Teku.

BABI NA 6

Ikon Halaka—Jehobah, “Gwanin Yaƙi Ne”

1-3. (a) Wace barazana Isra’ilawa suka fuskanta a hannun Masarawa? (b) Ta yaya Jehobah ya yi yaƙi domin mutanensa?

ISRA’ILAWA sun kamu—tsakanin manyan duwatsu da kuma teku. Sojojin Masar marasa jinƙai suna binsu, sun ƙuduri aniyyar sai sun halaka su.a Duk da haka, Musa ya aririci mutanen Allah kada su fid da rai. Ya ba su tabbaci cewa “Yahweh da kansa zai yi yaƙi dominku.”—Fitowa 14:14.

2 Duk da wannan, Musa babu shakka ya yi wa Jehobah kuka, kuma Allah ya ce: “Don me kake yi mini kuka? . . . ka ɗaga sandanka na kiwo, ka miƙa hannunka a bisa ruwan. Ruwan kuwa zai rabu kashi biyu.” (Fitowa 14:15, 16) Ka yi tunanin abubuwan da suka fara aukuwa. Sai Jehobah ya umurci mala’ikansa, kuma umudi na gajimare ya koma bayan Isra’ilawan, wataƙila yana bazuwa kamar garu yana rufe inda Masarawan za su kai farmaki. (Fitowa 14:19, 20; Zabura 105:39) Musa ya miƙa hannunsa. Iska mai ƙarfi ta busa, tekun ta rabu biyu. Ruwan ya daskare ya tsaya kamar garu, ya buɗe hanya mai isashen faɗi da ya ɗauki dukan al’ummar!—Fitowa 14:21; 15:8.

3 Da ya fuskanci wannan nuna iko, da Fir’auna ya koma gida da rundunarsa. Maimakon haka, Fir’auna mai fahariya ya ba da umurnin a kai farmaki. (Fitowa 14:23) Masarawan suka yi sauri suka bi Isra’ilawan ba tare da wani tunani ba, amma farmakinsu ya koma ɗimaucewa sa’ad da ƙafafun karusansu suka soma ɓangalewa. Da isar Isra’ilawa ƙetaren tekun, Jehobah ya umurci Musa: “Ka miƙa hannunka a bisa tekun, domin ruwa ya koma bisa kan Masarawa, da kekunan-dokinsu, da masu hawan dawakinsu.” Garu na ruwan kuwa ya rushe, ya binne Fir’auna da rundunarsa!—Fitowa 14:24-28; Zabura 136:15.

4. (a) Mene ne Jehobah ya tabbatar a Jar Teku? (b) Yaya wasu za su ji game da wannan kwatanci na Jehobah?

4 Ceton al’ummar Isra’ila a Jar Teku abu ne na tunawa a tarihin sha’ani da Allah ya yi da ’yan Adam. A wannan wajen Jehobah ya tabbatar da kansa “gwanin yaƙi.” (Fitowa 15:3) Yaya ka ji game da wannan kwatanci na Jehobah? Hakika, yaƙi kan jawo azaba da bala’i ga ’yan Adam. Shin amfani da ikon halaka da Allah ya yi ya kasance ne kamar abin da zai hana ka kusantarsa maimakon ka matso kusa da shi?

A Jar Teku, Jehobah ya nuna cewa shi “gwanin yaƙi” ne

Yaƙe-Yaƙe na Allah da Kuma na Mutane

5, 6. (a) Me ya sa ya dace da aka kira Allah “Ubangiji mai-runduna”? (b) Ta yaya yaƙe-yaƙe na Allah ya bambanta da na mutane?

5 Kusan sau ɗari biyu da sistin a cikin Nassosin Ibrananci kuma sau biyu a Nassosin Helenanci na Kirista, aka bai wa Allah laƙabin nan “Ubangiji mai-runduna.” (1 Sama’ila 1:11, Littafi Mai Tsarki) Tun da Mamallaki ne, Jehobah yana ja-gorar runduna mai girma na mala’iku. (Yoshuwa 5:13-15; 1 Sarakuna 22:19) Halaka da wannan rundunar za ta iya yi abin ban tsoro ne. (Ishaya 37:36) Halaka mutane ba ta da daɗin a yi tunaninta. Amma, dole ne mu tuna cewa yaƙe-yaƙe na Allah ba kamar ɗan tashin hankali ba ne na mutane. Shugabanni na soja da na siyasa za su yi ƙoƙari su nuna suna da kyakkyawar niyya wajen nuna ƙarfinsu. Amma yaƙe-yaƙe na mutane babu shakka ya ƙunshi haɗama da son kai.

6 Akasin haka, motsin zuciya ba ya rufe wa Jehobah hankali. Maimaitawar Shari’a 32:4 ta ce: “Dutse ne shi, aikinsa cikakke ne, kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Allah mai aminci ne, ba ya ruɗu, mai adalci ne shi, mai gaskiya kuma.” Kalmar Allah ta haramta fushi da ba ta da makawa, mugunta, da kuma nuna ƙarfi. (Farawa 49:7; Zabura 11:5) Jehobah ba ya aikata abu babu dalili. Yana amfani kaɗan ne kawai da ikonsa na halakarwa, sai ya kasance babu wani abin yi kuma. Kamar yadda ya ce ne ta bakin annabi Ezekiyel: “Ni ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji ni Ubangiji Yahweh, ai, na gwammanci ya juya daga yin mugunta ya rayu!”—Ezekiyel 18:23.

7, 8. (a) Mene ne Ayuba ya kammala cikin kuskure game da wahalarsa? (b) Ta yaya Elihu ya gyara tunanin Ayuba game da wannan? (c) Mene ne za mu iya koya daga abin da Ayuba ya fuskanta?

7 To, me ya sa Jehobah yake amfani da ikonsa na halakarwa? Kafin mu amsa, za mu tuna da mutumin nan mai aminci Ayuba. Shaiɗan ya ƙalubalanci cewa ko Ayuba—hakika, kowanne taliki—zai riƙe amincinsa cikin gwaji. Jehobah ya amsa ta ƙyale Shaiɗan ya gwada amincin Ayuba. Domin wannan, Ayuba ya yi ciwo, ya yi hasarar arzikinsa, kuma ya yi rashin ’ya’yansa. (Ayuba 1:1–2:8) Cikin rashin sanin abin da ke tafiya, Ayuba ya kammala cikin kuskure cewa wahalarsa horo ne kawai na rashin adalci daga Allah. Ya tambayi Allah dalilin da ya sa Ya mai da shi ‘abin da yake so a harba,’ da kuma ‘abokin gabansa.’—Ayuba 7:20; 13:24.

8 Wani saurayi mai suna Elihu ya fallasa kuskure da ke cikin tunanin Ayuba, ya ce: “Daidai ne wannan a ganinka? Adalcina ya fi na Allah, in ji ka.” (Ayuba 35:2, LMT) Hakika, ba hikima ba ce mu yi tunanin cewa mun fi Allah sani ko kuma mu yi tsammanin cewa abin da ya yi bai dace ba. Elihu ya ce: “Allah ba zai taɓa aikata mugunta ba! A wurin Mai Iko Duka babu kuskure!” Daga baya ya ce: “Mai Iko Duka kuwa ikonsa ya yi yawa har ba mu iya zuwa kusa da shi ba. Shi mai gaskiya ne, mai adalci kuma a yalwace, ba ya cutar mutum.” (Ayuba 34:10; 36:22, 23; 37:23) Za mu tabbata cewa idan Allah ya yi faɗā, yana da kyakkyawan dalilin yin haka. Da wannan, bari mu bincika wasu dalilai da ya sa Allah na salama wasu lokatai yake ɗamarar yaƙi.—1 Korintiyawa 14:33.

Abin da Yake Tilasta wa Allah na Salama Ya Yi Yaƙi

9. Me ya sa Allah mai tsarki yake yaƙi?

9 Bayan Musa ya yabi Allah cewa shi “gwanin yaƙi ne,” ya ce: “Ya Yahweh, wane ne kamarka a cikin dukan alloli? Wane ne kamarka cikin darajar tsarkinka?” (Fitowa 15:11) Annabi Habakkuk ma ya ce: “Kai wanda idanunka masu tsarki ne, sun fi ƙarfin ganin mugunta, ba ka so ka kalli laifi.” (Habakkuk 1:13) Ko da yake Jehobah Allah ne na ƙauna, har ila shi Allah na tsarkaka, adalci, da kuma shari’a. Wasu lokatai, waɗannan halaye suke tilasta masa ya yi amfani da ikonsa na halakarwa. (Ishaya 59:15-19; Luka 18:7) Allah baya ƙazantar da tsarkakarsa sa’ad da ya yi yaƙi. Maimakon haka, yana yaƙi ne domin yana da tsarki.—Fitowa 39:30.

10. Yaya za a warware magabtaka da aka annabta a Farawa 3:15, kuma yaya mutane adalai za su amfana?

10 Ka yi la’akari da abin da ya faru bayan mata da miji na farko, Adamu da Hauwa’u, suka yi wa Allah tawaye. (Farawa 3:1-6) Da ya ƙyale rashin amincinsu, da Jehobah ya rage matsayinsa na Mamallakin Dukan Halitta. Tun da Allah mai adalci ne, ya zama dole ya yi musu hukuncin kisa. (Romawa 6:23) A cikin annabci na farko na Littafi Mai Tsarki, ya ce magabtaka za ta kasance tsakanin bayinsa da kuma mabiyan “macijin,” Shaiɗan. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9; Farawa 3:15) A ƙarshe, wannan magabtakar za ta ƙare ne kawai ta wajen ƙuje Shaiɗan. (Romawa 16:20) Amma wannan shari’ar za ta kawo albarka mai girma ga mutane adalai, ta kawar da rinjayar Shaiɗan a duniya kuma ta buɗe hanyar mai da duniya aljanna. (Matiyu 19:28) Har sai lokacin, waɗanda suke gefen Shaiɗan za su ci gaba da razana ga lafiyar jiki da ta ruhaniya ta mutanen Allah. A wasu lokatai, dole ne Jehobah ya saka hannu.

Allah Ya Aikata don Ya Kawar da Mugunta

11. Me ya sa Allah ya ga ya zama dole ya kawo rigyawa ta dukan duniya?

11 Rigyawa ta zamanin Nuhu aukuwa ce ta irin wannan saka hannu. Farawa 6:11, 12, ta ce: “Allah kuwa ya ga duniya duka ta ɓaci, ta kuma cika da tashin hankali. Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa dukan duniya ta ɓaci, gama dukan ’yan Adam sun ɓata rayuwarsu a duniya.” Allah zai ƙyale miyagu ne su kawar da ɗabi’a ’yar kaɗan da ta rage a duniya? A’a. Jehobah ya ga ya zama dole ya kawo rigyawa ta duniya ta halaka waɗanda suke da sha’awa na ƙwarai na nuna ƙarfi da kuma yin lalata.

12. (a) Mene ne Jehobah ya annabta game da “zuriyar” Ibrahim? (b) Me ya sa za a halaka Amoriyawa?

12 Hakanan ma hukuncin Allah bisa Kan’aniyawa. Jehobah ya bayyana cewa daga Ibrahim za a yi “ɗa” ta wurin wanda za a albarkaci dukan iyalai na duniya. Cikin jituwa da wannan nufin, Allah ya kafa doka cewa za a ba ɗan Ibrahim ƙasar Kan’ana, ƙasar da mutane da ake kira Amoriyawa suke zaune. Yaya za a ce Allah ya yi adalci idan ya fid da mutanen nan da ƙarfi daga ƙasarsu? Jehobah ya annabta cewa sai bayan shekaru 400 ne “mudun laifofin Amoriyawa” zai “cika.”b (Farawa 12:1-3; 13:14, 15; 15:13, 16; 22:18) Cikin wannan lokacin, Amoriyawan suka daɗa nitsewa cikin muguwar lalata. Kan’ana ta zama ƙasar bautar gumaka, kisa, da kuma ƙazamin jima’i. (Fitowa 23:24; 34:12, 13; Littafin Ƙidaya 33:52) Mazauna ƙasar suna kashe yara cikin wutar hadaya ma. Allah mai tsarki zai ƙyale mutanensa ga irin wannan muguntar? A’a! Ya ce: “Ƙasar ta ƙazantu, ina kuwa hukunta ta saboda laifofinta. Domin haka ne ƙasar ta amayar da mazaunanta.” (Littafin Firistoci 18:25) Jehobah bai halaka mutanen ba kawai, ba ji ba gani ba. Kan’anawa masu zukatan kirki, kamar su Rahab da kuma Gibiyonawa, an ƙyale su.—Yoshuwa 6:25; 9:3-27.

Yaƙi Domin Sunansa

13, 14. (a) Me ya sa ya zama dole Jehobah ya tsarkake sunansa? (b) Ta yaya Jehobah ya tsabtace sunansa daga zargi?

13 Domin Jehobah mai tsarki ne, sunansa yana da tsarki. (Littafin Firistoci 22:32) Yesu ya koya wa almajiransa su yi addu’a: “A kiyaye sunanka da tsarki.” (Matiyu 6:9) Tawaye a Adnin ya ƙazantar da sunan Allah, ya ta da shakka game da darajarsa da kuma yadda yake mulki. Jehobah ba zai taɓa ƙyale irin wannan zagi da kuma tawaye ba. Dole ne ya tsarkake sunansa daga zargi.—Ishaya 48:11.

14 Ka sake yin la’akari da Isra’ilawa. Idan suka ci gaba da kasancewa bayi a ƙasar Masar, alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim cewa ta wajen Zuriyarsa dukan iyalai na duniya za su albarkaci kansu ya kasance wofi. Amma ta wajen cetonsu da kuma shirya su su zama al’umma, Jehobah ya tsabtace sunansa daga zargi. Saboda haka, annabi Daniyel ya tuna cikin addu’a: “Yanzu ya Ubangiji Allahnmu, kai ne ka fito da jama’arka daga ƙasar Masar da hannu mai iko. Ta haka ka sami wa kanka suna.”—Daniyel 9:15.

15. Me ya sa Jehobah ya ceci Yahudawa daga bauta a Babila?

15 Abin farin ciki, Daniyel ya yi wannan addu’ar a lokacin da Yahudawa suke bukatar Jehobah ya sake ceto domin Sunansa. Yahudawa marar biyayya sun samu kansu cikin bauta, lokacin kuwa a Babila ne. Nasu babban birni, Urushalima, ya kasance kango. Daniyel ya san cewa mai da Yahudawan ƙasarsu zai ɗaukaka sunan Jehobah. Saboda haka Daniyel ya yi addu’a: “Ya Yahweh, ka gafarce mu. Ya Yahweh, ka saurare mu, bari ka yi wani abu domin a girmama Sunanka. Ya Allahna, kada ka ɓata lokaci, gama da Sunanka ne ana kiran birninka da jama’arka.”—Daniyel 9:18, 19.

Yaƙi Domin Mutanensa

16. Ka ba da bayanin dalilin da ya sa son ya kāre sunansa ba ya nufin cewa Jehobah ba shi da tausayi kuma yana da son kai.

16 Domin Jehobah yana son kāre sunansa yana nufin cewa marar tausayi ne shi kuma mai son kai? A’a, domin ta aikata cikin jituwa da tsarkakarsa da ƙaunar shari’a, yana kāre mutanensa. Ka yi la’akari da Farawa sura 14. A nan mun karanta game da sarakuna huɗu da suka kai hari kuma suka kama ɗan wan Ibrahim, Lot, tare da iyalinsa. Da taimakon Allah, Ibrahim ya yi kyakkyawar nasara bisa runduna mai yawa da ta ɗara tashi! Tarihin nasararsa wataƙila shi ne tarihi na farko a cikin “Littafin Labarin Yaƙe-yaƙen Yahweh,” wataƙila littafin da yake ɗauke da wasu arangama na sojoji da ba a rubuta cikin Littafi Mai Tsarki ba. (Littafin Ƙidaya 21:14) Nasarori da yawa za su biyo.

17. Mene ne ya nuna cewa Jehobah ya yi yaƙi domin Isra’ilawa bayan sun shiga ƙasar Kan’ana? Ka ba da misalai.

17 Ba da jimawa ba kafin Isra’ilawa su shiga ƙasar Kan’ana, Musa ya tabbatar musu cewa: “Yahweh Allahnku wanda yake tafiya a gabanku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a idanunku.” (Maimaitawar Shari’a 1:30; 20:1) Farawa da magajin Musa, Joshua, kuma ya ci gaba a lokacin Mahukunta da kuma lokacin sarautar sarakuna masu aminci na Yahuda, babu shakka Jehobah ya yi yaƙi domin mutanensa, ya ba su nasarori masu ban sha’awa da yawa bisa abokan gabansu.—Yoshuwa 10:1-14; Alƙalai 4:12-17; 2 Sama’ila 5:17-21.

18. (a) Me ya sa za mu yi godiya cewa Jehobah bai canja ba? (b) Me zai faru sa’ad da magabtaka da aka kwatanta a Farawa 3:15 ta zo ƙarshenta?

18 Jehobah bai canja ba; kuma nufinsa na mai da wannan duniya ta zama aljanna mai salama bai canja ba. (Farawa 1:27, 28) Har ila Allah yana ƙyamar mugunta. Hakanan kuma, yana ƙaunar mutanensa ƙwarai da gaske kuma ba da daɗewa ba zai yi yaƙi dominsu. (Zabura 11:7) Hakika, magabtaka da aka kwatanta a Farawa 3:15 ana tsammanin za ta kai lokaci na musamman na nuna ƙarfi ba da daɗewa ba. Domin ya tsarkake sunansa kuma ya kāre mutanensa, Jehobah zai sake zama “gwanin yaƙi”!—Zakariya 14:3; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 16:14, 16.

19. (a) Ka kwatanta abin da ya sa amfani da ikon halakarwa na Allah zai iya jawo mu kusa da shi. (b) Yaya ya kamata yadda Allah yake son ya yi yaƙi da son rai dominmu ya taɓa mu?

19 Ka yi la’akari da wannan kwatanci: A ce wata muguwar dabba ta faɗā wa iyalin wani mutum, sai mutumin ya shigo ya kashe dabbar. Za ka zaci matar da ’ya’yan su guje shi domin abin da ya yi? Akasin haka, za ka so ƙauna marar son kai ta motsa su. Hakazalika, bai kamata ba mu guji Allah domin ikonsa na halakarwa. Yaƙi da son ransa domin ya kāre mu ya kamata ya zurfafa ƙaunar da muke masa. Kuma daraja da muke ba shi domin ikonsa mara iyaka ya kamata ta ƙaru ita ma. Da haka, za mu “miƙa wa Allah sujada da ta dace a cikin tsoro da ban girma.”—Ibraniyawa 12:28.

Ka Matso Kusa da “Gwanin Yaƙi”

20. Idan muka karanta tarihin Littafi Mai Tsarki game da yaƙe-yaƙe na Allah da ba mu fahimta ba sosai, me ya kamata mu yi, kuma me ya sa?

20 Hakika, Littafi Mai Tsarki bai ba da cikakken bayani ba game da dukan yaƙe-yaƙe na Allah. Amma game da wannan za mu iya kasancewa kullum da tabbaci: Jehobah ba ya amfani da ikonsa na halakarwa cikin rashin adalci, mugunta, ko kuma ƙeta. Sau da yawa, bincika matanin tarihin Littafi Mai Tsarki ko kuma wasu ɓarin bayani zai iya taimakawa a fahimci batun. (Karin Magana 18:13) Ko sa’ad da ba mu samu cikakken bayani ba, koyo game da Jehobah da kuma bimbini a kan halayensa masu tamani za su taimake mu warware kowacce tantama da za ta taso. Idan muka yi wannan, za mu ga cewa muna da dalilai masu yawa na dogara ga Allahnmu, Jehobah.—Ayuba 34:12.

21. Ko da yake Jehobah “gwanin yaƙi” ne a wasu lokuta, mene ne hakan ba ya nufi?

21 Ko da yake Jehobah “gwanin yaƙi” ne, idan yanayi ya bukaci haka, wannan ba ya nufin cewa shi masoyin yaƙi ne ainihi. A wahayin karusa na sama na Ezekiyel, an kwatanta Jehobah da cewa yana shirye ya yi yaƙi da abokan gabansa. Duk da haka, Ezekiyel ya ga bakan gizo ya kewaye Allah—alamar salama. (Farawa 9:13; Ezekiyel 1:28; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:3) Babu shakka, Jehobah mai kamewa ne kuma mai salama. “Allah ƙauna ne,” in ji manzo Yohanna. (1 Yohanna 4:8) Dukan halayen Jehobah sun kasance daidai. Lallai muna da gata, mu kusaci irin wannan Allah mai iko har ila kuma mai ƙauna!

a In ji Bayahude ɗan tarihi Josephus, wajen “karusa 600 tare da mahayan dawakai 50,000 da dakaru wajen 200,000 suka bi Ibraniyawan.”—Jewish Antiquities, II, 324 [xv, 3].

b Hakika, kalmar nan “Amoriyawa” ya ƙunshi dukan mutanen Kan’ana.—Maimaitawar Shari’a 1:6-8, 19-21, 27; Yoshuwa 24:15, 18.

Tambayoyi don Bimbini

  • 2 Sarakuna 6:8-17 Ta yaya matsayin Allah na “Ubangiji mai-runduna” zai kasance da ƙarfafa gare mu a lokacin baƙin ciki?

  • Ezekiyel 33:10-20 Kafin Jehobah ya yi amfani da ikonsa na halakarwa, wane zarafi yake bayarwa cikin jinƙai ga waɗanda suke taka dokarsa?

  • 2 Tasalonikawa 1:6-10 Ta yaya halakar miyagu da take zuwa za ta kawo farin ciki ga bayin Allah masu aminci?

  • 2 Bitrus 2:4-13 Me yake motsa Jehobah ya yi amfani da ikonsa na halakarwa, waɗanne darussa yake koya wa dukan ’yan Adam?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba